← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 48

Sashe 25

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farhan ta so tai zamanta a gida ta dena zuwa tun da hutu za'ayi, amma idan ta zauna a gidan a takure take ga damuwa, dan haka take zuwa school ko ba komai tana ganin abun ƙaunarta tana jin daɗi.

************

"Meena, wai anya lafiyar ki ƙalau kuwa?"

"Mum why are you asking? Me kika gani?"

"Gaba É—aya kin É—ashe, se wata uwar rama da kike yi, ga wani uban bacci wanda na kasa gane miki gaba É—aya"

"Am ok fa, kawai weather nan ce is not compostable to me, yau zafi gobe sanyi, and I have no appetite bana iya cin Abinci, shiyasa nake rama But i will be ok insha Allah"

"To shikenan, idan kuma ba hali muje Asibiti a duba ki"

"No don't mind Mum, sena dawo"

"Ok safe journey"

Meena ta amsa da "Thank you" sannan tai waje.

An taru sosai a gurin hall É—in makarantar, dan kallon fafatwar da za'ai na Debate, É—alibai 'yan kallo suna cakuÉ—e maza da mata, ana kallon fafatawar.

Farhan na kusa da Prince, ya bata wayarsa tana kallon pictures ɗin 'yan gidansu, yanayin hotunan nasu ya tabbatar mata da Lallai Prince ɗinta ɗan hutu ne, sannan da alamun akwai kyakkyawar alaƙa da shaƙuwa a tsakanin su.

Farhan ta kalli hoton Mother tace "she's Your Mum ko?"

"Eh mana, in law É—inki ce, ai zaku haÉ—u agurin bikin Brother na, i will introduce you to my Family"

Zare ido tai tace "ni dai a'a gaskiya, se ace munyi rashin kunya ai"

"Meye wani rashin kunya, gara su sani tunda wuri ai, ko kin manta ina processing yadda zamuyi Aure ne? Gara su san da Maganar tunda wuri"

Shiru tai jikinta yai sanyi, duk da maganar Auren da yai yasa jikinta yai sanyi, amma a wani ɓangaren tana fatan Allah ya amince, yasa ta Auri Prince, First love ɗinta kenan, ba ta jin daga kansa zata kuma son wani namiji haka.

Ta cigaba da kallon hotunan ta, Sadik ya jiya yana magana da su Nas, yaji suna zancen wani Film.

"Nas, kune sarakan kallon series Films, dan Allah in mun bar nan System É—ina na mota, zaku turamin fina finai masu kyau sosai"

Amin yace "Allah mutumina, ka shigo layin kenan?"

Sadik yace "wani layin kenan?"

Nas yace "layin eh mana"

Sadik yai tsaki yace "Malam ba wannan haukan nace ba, just normal films nake so na Soyayya, za'ai hutu bayan bikin nan ina so zan kalla, ina son wanda ake soyaya sosai a ciki"

Amin yace "ji shi wai wani na Soyayya, se kace soyayyar suka iya, banda ƙauyanci da soyayyar yara ba abunda suke"

Farhan ta ɗago ta kalli su Amin, ta ja ƙaramin tsaki wanda Sadik ne kawai yaji, yai murmushi yace "don't mind them Baby, kar su mayar min da ke mafaɗaciya, i love Your silent character"

Farhan tace "ai ni ba faÉ—a zan ba"

"Ai tunda kika fara tsaki, nasan faÉ—an ma zakiyi ne"

Tai shiru ta cigaba da abunda take.

Sadik yace "Nasir zaku turamin ko kuwa?"

Nasir ya kashe ido É—aya yace "meze hana a turamaka ranka ya daÉ—e, akwai korean, indian, American Chinese and many hot Love series, depending on which you wish to watch"

Sadik yace "Kawai me kyau nake so"

"Shikenan, bari a tashi daga nan É—in, za'a tura maka Insha Allah"

Suna cikin maganar sega Babba ya nufo su, yana tunkaro gurin Farhan ta haÉ—e rai, jikinta ya hau tsuma, saboda yanzu a Duniya ta tsani ko ganin Mubarak.

Ya faki idon Sadik ya kashe mata ido, ta galla masa harara ta É—auke kanta.

Ya zauna kusa da su Sadik ya miƙa musu hannu, su kai musabiha, miƙewa Farhan tayi zata bar gurin, Sadik ya kalleta yace "ina zaki kuma?"

ÆŠan yatsuna fuska tayi tace "can zan koma"

Sadik yace "ok as you wish my love"

Tai masa guntun murmushi, ta koma cikin 'yan ajinsu mata, da suke ta zuba hira, gefen su kuma 'yan ajinsu Sadik ne, su Taslim da Meenal.

Can kuma ana can ana ta faman Debate, amma hankalin su ba'a akan abunda ake yake ba.

Su Lilly kam banda hirar litattafan da suke karantawa a Online ba abunda suke yi.

Taslim ta dubi su Lilly tace "Lilly, me kuke Magana a kai ne?"

Lilly tace "bakomai fa"

"A'a naji kamar kuna hirar romantic book ne na hausa"

A É—an tsiwace Lilly tace "eh"

"Dama akwai romantic books na Hausa?" Taslim ta tambaya

Lilly tace "eh, akwai masu zafi ma kuwa"

Nan Taslim ta dinga lallaɓa su Lilly, suna bata labarin litattafn da suke karantawa a Online.

Gaba É—aya hirar tasu ta gunduri Farhan, su gaba É—aya makarantar daga mazan har matan tunanin su iri É—aya ne, duk wata harka ta watsewa su ita suke so.

Haushi ne ya kuma kama Farhan, ta Tashi ta bar hall ɗin gaba ɗaya ta fito, zagayen ta ta shiga yi a makarantar, tana 'yan leƙe leƙen ta, makarantar shiru kamar ba kowa duk suna hall ɗin da ake gabatar da Debate ɗin.

Katsam idonta ya sauka akan corper George a cikin wani aji, abunda idanuwan ta su kai katarin gani ne ya kiÉ—imata, wanda har ya kusa awon gaba da nutsuwar ta na wani É—an lokaci, a very deep Romance with his ss3 student, she don't even know the name of the lady, ta san dai shine class mastern finalist student É—in.

Jikinta ne ya hau wata irin tsuma, kuma ta kasa motsi daga gurin, se idanunta da take ta faman jujjuyawa kamar taiwa Sarki ƙarya.

Ba tsammani George ya waigo ya ga Farhan tai musu ƙuri da ido, da sauri ya cika Nasreen, ɗalibar da suke watsewa taren, yana ƙoƙarin tattaro nutsuwarsa ya daidai ta.

Ganin da Farhan tayi sun ganta Ya bata ƙwarin gwiwar, fizgo kuzarin da ta rasa na wani ɗan lokaci, cikin sassarfa ta ja da baya cikin hanzari ta nufi hanyar da ta sauka daga kan benen.

Kana ganin ta kasan a firgice take, kamar wadda ke shirin zarewa, ba zato ba tsammani tai karo da Sir Nazir yana ƙoƙarin hawowa kan benan.

Cak ta tsaya tana cigaba da rarraba ido, kamar mara gaskiya.

Kallon tuhuma ya bi ta da shi, yana ƙare mata kallo yana son gano me ya razanata haka, fuskarta take bayyanar da alamun rashin gaskiya?

Hanya ta bashi, dan ya wuce sannan ita ma ta wuce, amma ya tsyaa kyam yana cigaba da kallon ta.

Ba tsammani taji muryarsa yace "me kike yi a nan?"

Girgiza masa kai tayi tare da faÉ—in "Nothing sir"

"Nothing as how? Ke da waye a saman gurin nan, bayan ba kowa duk ana hall É—in da ake Debate?"

Rasa amsar da zata ba shi tai, ta cigaba da tsatstasare shi da ido.

"Ke da wannan shashashan yaron ne a saman ko?"

A razane ta kalli Sir Nazir, tana son tabattar da abunda yake faÉ—a.

Ganin Farham taƙi magana ta cigaba da bin sa da idanu ya sa ya ji zargin sa na neman zama gaskiya.

"You Are Much more than stupid Farhan, ki cigaba da biyewa RUƊIN ƘURUCIYA, Kina rusa Rayuwar ki, nan gaba se kin yi kuka da idonki, a lokacin da kuskuren da ki kai ba ze gyaru ba, ki cigaba da ba shi damar keɓewa da ke, sheɗan na buga muku ganga, nan gaba zaki gane shayi ruwa ne stupid girl"

Maimakon ya hau saman benen, se ya fasa ya juya ya sauka, zuciyarsa na ƙuna, ganin yadda rayuwar yara mata masu ƙananun shekaru, ke lalacewa saboda RUƊIN ƘURUCIYA.

Farhan kuwa kasa matsawa ta yi daga in da take, maganganun sir Nazir suka cigaba da sukar zuciyarta, yana zarginta da wani abu, wanda ba shi da tabbas a kai, dan duk wannan masifar da yake a yanzu, bashi da wata hujja da ze kafa, akan ta, amma ya sa mata ido yana binta da miyagun maganganu, tabbas duk da ƙanƙantar shekarunta, tasan idan har aka zarge ka da keɓewa da wani namiji, to kuna aikata wani abune da be kamata ba, take ta tuno abunda ta gani yanzu a saman benen, kenan da irin abun Nazir yake zarginta kenan?.

Hawayena ya shiga bin fuskarta, fan take ta ji ranta yai ƙololuwar ɓaci, haka ta sakko jikinta a sanyaye ta tafi hanyar gate ɗin fita ta zauna, ana kaɗa jiniya, tai gaba ba tare da ta jira kowa ba.

Tun ranar da Nazir yai mata wannan zargin, gaba É—aya se ta tsargu take ganin kamar kowama haka yake kallonta, dan haka kasancewar da ma sun kammala jarrabawa, ba ta sake zuwa makarantar ba har aka yi hutu.

Hakan ya damu Sadik sosai, ganin ba ta zuwa har a kai hutu, ranar da za'ai hutu ya zo da system É—in sa, aka tura masa fina finai, wanda ze dinga kallo kan a koma school.

Satin da a kai hutu, a satin za'a fara bikin Ussy, ana ta shirye shirye, mussaman Sadik ya bugo nasa invitationsa É—in, da ze rabawa abokan sa.

Gefe ga son ganin Farhan da yake yi, gashi yasan gidan su Farhan Akwai tsaro sosai, dan mahaifinta malami ne, idan ya je gidan su Farham be san me zece ba.

Shiryawa yai, ya tafi gidan su Khairat, a falo ya tarar da ita tana cin Abinci.

Sadik yace "Ina Mama?"

"Ba ta nan, lafiya na ganka kamar an jefo ka? Ka wani sha Manyan kaya kamar wani ango, ni na taɓa ganin ka a manyan kaya kuwa?"

Sadik yace "Khairat gidan su Farhan na ke so ki rakani dan Allah"

Yamutsa fuska Khairat ta yi tace "wace hakan?"

"So nake na bata invitation, tace idan ban kai mata gida ba baza'a barta taje ba, ni kuma i dont know how to explain myself idan naje, shiyasa nace bari in zo muje tare"

Khairat tace "to ai ita Farhan É—in nake son jin wacece?"

" 'yar ajinmu ce" ya bata amsa.

"Gaskiya ban yadda ba, kana yawan kirana da Sunan ta, ko 'yar ajin ku ce akwai wani abu a tsakanin ku"

"Eh budurwa ta ce"

Yatsuna fuska Khairat tayi tace "kuma shine ni zan raka ka?"

"Kinga idan ba zaki ba ba se kin rainamin hankali ba" ya faÉ—a a kausashe.

"Naji zani" ta faɗa cike da ɓata rai.
Chapter 25 · 0% Book details