Sashe 39
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farhan abun duniya ya isheta, gashi haka nan tun da taga wannan jinin ta tsorata taji cikinta ya ƙara tsananta mata ciwo, tun tana basarwa harta kasa jurewa ta fara zubar da hawaye,ba tare da kowa ya gane halin da take ciki ba.
Ganin an tashi kowa na fita, amma ita tana zaune yasa Lilly ƙarasawa gurinta, ta taɓa ta tace "Farhan an tashi fa"
Shiru Farhan tayi ba ta É—ago ba, kuma ba tace komai ba.
Sadik yana fitowa daga ajinsu ya tafi gurin Farhan, sedai ya tarar da ita ta kifa kanta, ba ta da alamar tashi daga gurin zamanta, ga Lilly a tsaye a kanta.
Sadik ya ƙaraso da sauri yace "lafiya kuwa?"
Lilly tace "wallahi ban san meya sameta ba, na mata magana amma taƙi tashi"
"Princess menene? What's wrong with you?"
ÆŠago kai tayi a hankali, hawaye ya wanke mata fuska.
Yace "Ya Salam, menene?"
"cikina ne kemin ciwo".
A hankali ya durƙuso yace "Baki je Asibitin da nace ba ko? Tashi muje Clinic a duba ki"
"Um um ni bazanje ba, gida zan tafi" ta haÉ—a gumi sosai, ga hawaye na bin fuskarta. He just wish he can hug her and wipe her tears.
Yace "ba zaki A dubamin ke É—in ba kenan?"
"Ni gida kawai" tai maganar tana jujjuya kai saboda ciwo.
Yace "ok tashi muje mota" ita kam Lilly gaba É—aya burgeta sukayi, yadda yake nuna damuwarsa akan ta.
Sadik ya miƙa hannu ya riƙo hannunta, Lilly ta kama ɗaya hannun suna tafe tana durƙushewa, Sadik yace "Farhan, bari in ɗauke ki kawai in kaiki mota, tunda tafiyar ta gagara"
Da sauri ta sake fashewa da kuka tace ba ta yadda ba.
Da ƙyar suka ƙarasa mota, makaranta duk an watse.
Nazir yana bene na biyu, a Office yana ƙoƙarin tashi, ta window ya hango Lilly da Sadik sun riƙo Farhan, tana durƙushewa, ya girgiza kai ya nemi guri ya zauna, dan abunda tunanin sa ke kawo masa akan su daban ne"
Tare da Lilly Sadik suka tafi kai Farhan gida, Lilly na rungume da Farhan.
Da sukaje gidan ma, Sadik na mota Lilly ce ta kama Farhan Zuwa cikin layinsu.
Hakan yai daidai da fitowar Abban Farhan ze tafi masallaci, a kiɗime ya ƙarasa in da Su Lilly suke yace "lafiya kuwa? Meya sameta?"
Lilly tace "ba ta da lafiya ciwon ciki take"
Da Sauri Abba ya riƙota yana mata Sannu, Lilly ta juya zata tafi yace "Yarinya zo muje ko ruwa ki sha a gidan"
Lilly tace "A'a Nagode, zan tafi gida kar a ga na daÉ—e"
Abba yaita mata godiya yana sa mata albarka.
Sadik na bakin layin yana kallonsu, sedai be ƙarasa ba, da Lilly ta dawo seda suka kaita har gida sannan suka tafi.
Umma ma ta tsorata da ganin Farhan a haka, amma ta kasa nuna damuwarta sosai, Abba ya É—ebo ruwa yai tai mata tofi, ya bata ta sha.
Da ƙyar aka samu bacci ya ɗauke ta.
Sadik kam tunda ya koma gida kasa sukuni yai, yana ta tunanin halin da Farhan ke ciki, dan ya tsorata da halin da ya ganta a ciki.
Tunda Farhan ta fara bacci ba ta tashi ba, se la'asar kuma ta tashi da sauƙi da sosai, ƙannenta suka dinga jera mata Sannu.
Umma anyi abun kai ta kaiwa Farhan ruwa tace taje ta watsa, Farhan taji daÉ—in hakan sosai.
Sedai bayan tayi fitsari taga kamar jini a cikin fitsarin, basarwa tai dan bata kawo daga jikinta bane, dan haryanzu ta kasa manta abunda ta gani, lokaci lokaci ta kanji gabanta ya faÉ—i idan ta tuna.
Wankanta ta cigaba dayi, ta kammala tai Alwala ta miƙe kawai taga jini na bin ƙafarta.
Ihu ta buÉ—e baki zatai, tai saurin saka hannu ta tsohe bakinta, nan ta shiga zazzare idanu a banÉ—akin.
Kawai ta hasko abunda ya faru da Nasreen ta ss3 shine itama ya sameta, ta dinga rusa kuka a banÉ—aki.
Se da tai me isarta sannan ta sake wanke jikinta ta fito.
Ta dinga ƙoƙarin ɓoye hawayen da takeyi, ta shiga ɗakinta, ta tarar Umma ta ajiye mata shayi a ɗakin nata.
Kasa sha tai ta nemi Guri ta zauna ta cigaba da kukanta, can ta kalli ƙafarta ta ga yadda wani jinin ke cigaba da binta, nan ta sake rikicewa ta cigaba da kuka ta koma banɗaki da sauri ta sake wankewa.
Umma ta biyo ta É—aki da magani a hannunta tace "ga magani nan, Na aika gidan Nurse É—in nan, tace ki sha wannan"
 Sedai Umma taga kamar Farhan hankalinta baya kanta, nan ta lura da hawayen dake kwance a idonta.
"Ke lafiya kuwa?"
Cikin kuka Farhan tace "Umma mutuwa zanyi"
Cikin rashin fahimta Umma tace "ke bana son shirme, cikin ne yake miki ciwo haryanzu?"
"A'a fitsarin jini nake yi, kuma ko banje nayi fitsarin ba se inga ya zubo"
Gaban Umma me yai mummunar faɗuwa, ba ta taɓa kawowa Farhan yin Al'ada a Yanzu ba, saboda ƙananan shekarunta"
Jiki a sanyaye Umma ta bar ɗakin, ba ta daɗe ba ta dawo ta miƙawa Farhan pad tace "ki dena wannan kukan, jinin al'ada ne, ga wannan da shi ake amfani" Umma tai maganar ko haɗa ido ba ta san yi da Farhan, tana bata tai waje.
Mamaki ne ya kama Farhan, menstruation fa kenan, shikenan ta shiga uku itama za'a fara rubuta mata zunubi.
Jin tana ƙoƙarin sake ɓaci ne yasa, tabi direction ɗin yadda ake amfani da pad ɗin da ke rubuce a jiki ta saka, dan ba wani bayani da Umma tai mata, akan yadda zata dinga kula da kanta, da abunda ba'a so tayi.
Ita Umma hankalinta ne yai ƙololuwar tashi, duk wasu alamu na girma sun gama bayyana a jikin Farhan ɗin.
Duk da ƙanƙantar shekarunta, alamun girma kam yanzu babu wanda babu a tare da ita.
Farhan kuwa kukanta ta cigaba da rerawa, kamar wata ƙaramar yarinya, ko wadda wani bala'i ya faru da ita.
Bayan sallar magariba Abba ya dawo gida, ya siyowa Farhan kayan marmari, ko zata iya ci.
Yace Umma ta kira masa Farhan.
Ba jimawa sega Farhan ta zo, fuskarta duk ta kumbura saboda kuka, da ƙyar take tafiya, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta son tayi.
Abba ya kalli Farhan, Sannan ya kalli Umma yace "yarinyar nan ko dai mu tafi Asibiti ne?"
Umma tace "A'a base munje Asibiti ba"
"To ai naganta haryanzu wani iri ne"
Farhan tace "A'a Abba ai na samu sauƙi"
Abba yai ajiyar zuciya yace "shikenan, ga wannan ledar ki É—auka kije ki samu kici, Allah ya sawwake"
Tace "Ameen Abba Nagode sosai"
Ta tashi ta bar É—akin, Umma ta kalli Abba tace "Yarinyar nan fa, Al'ada ta fara"
Abba yace "to ciwon cikin kenan dama, lallai Farhan an girma, to Allah ya sawwake"
Cikin damuwa Umma tace "Nifa ina cikin damuwa, Farhan tayi ƙanƙanta, haryanzu fa ba shekarunta goma sha uku, tayi ƙanƙanta"
Abba yace "to banda abunki zamu hana Allah ikonsa ne akanta?"
"A'a, amma a tsorace nake, yarinya ce ƙarama amma kalli yanayin jikinta, anya ba za'a haƙura da bokon nan ba a Aurar da ita, ina jin tsoron wannan zamanin da muke ciki"
"A'a ki kwantar da hankalinki, ai Allah shi ke ds zamani, kuma kowacce yarinya da irin halittar da Allah yai mata, kiyi haƙuri ki yi mata Addu'a kawai"
Jiki a sanyaye Umma tace "to Allah ya tsare"
Har Dare yayi Sadik ya kasa bacci, yana son sanin halin da Farhan ke ciki amma ba damar sanin hakan.
Da safe da wuri Ya shirya ya tafi Makaranta, amma har aka tashi Farhan ba ta zo ba.
Abun ya sake É—aga masa hankali, da aka tashi ya koma gida da yamma, yaje ya É—akko Khairat yace mata zata rakashi gidan su Farhan ya duba ta.
Ba ta musa masa ba ta bishi, ya biya yai siyayya, suka tafi gidan su Farhan É—in. da sukaje layin ya bata kayan dubiyar yace in ta shiga ze kirata ta haÉ—a shi da Farhan.
Khairat har Mamaki take akan yadda Sadik rawar jiki akan wannan 'yar mistilar Yarinyar.
Yauma Umma ta karrama Khairat sosai, Farhan na ganin Khairat ta san tare suke da Sadik.
Suka shiga É—akin Farhan suka gaisa, Khairat ta kalleta tace "ya jiki?"
"Alhamdilillah na samu sauƙi"
"Bari in kira shi a waya, yace in haÉ—aku ku ze miki ya jiki"
Farhan ta jinjina kai, Khairat ta kira Sadik a waya ta bawa Farhan.
Sedai kowannen su ya kasa Magana, can Sadii ya katse shirun ta hanyar cewa "ya jikin naki?"
"Naji sauƙi Alhamdilillah"
"Kunje Asibitin ne?"
"Eh munje" ta bashi amsa.
"To shikenan, ki kula sosai dan Allah ki sha magungunan da aka baki kinji Babyna"
Murmushi tai tace "to insha Allah"
Su kai sallama ta katse wayar, Khairat ta miƙe tace "to shikenan Allah ya ƙara sauƙi, zan tafi"
Iya tsakar gida kawai Farhan ta iya raka Khairat, saboda gani take da tayi kyakyawan motsi, za'a gane halin da take ciki.
Wasa wasa seda Farhan ta shafe kwana biyar cif, sannan ta koma makaranta lokacin ta koma normal.
Lokacin da ta gama period É—in ma tayi amfani da karatun Islamiyyar ta ne gurin yin wanka, da gane É—aukewar jinin, dan in ta Umman ta ne sedai ta zauna a haka ba zata gaya mata ba, dan tunda Farhan ta fara period ma kamar sake janye mata tayi.
Ranar da ta koma makaranta Sadik ji yai kamar ya rungumeta saboda farinciki, tayi haske gau, amma fuskarta ta faÉ—a sosai.
"Princess, kin rame da yawa fa"
Murmushi kawai tai ta É—auke kai ba tace masa komai ba.
"Da kuka je Asibitin ba suce miki komai akan ciwon cikin naki ba?"
Gabanta ne ya faÉ—i, ta maze tace "kawai ciwon ciki ne kuma na warke ai"
Yace "to Alhamdilillah, Allah ya ƙara mana lafiya"
Ta Amsa da "Ameen"
Tun dawowarta makaranta, kullum idan aka fita break su Lilly ba su da aiki se karanta litattatafai masu ɗauke da zunzurutun batsa, wadda ta kasance barazana ga ƙwaƙwalwar ƙanan yaran.