Sashe 12
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mahaifinsa yai murmushi ya shafa sumar kan Sadik yace "maza kaje ka canza kaya ka huta, in zo muyi hira"
ÆŠaya daga abokan mahaifun nasa yace "Wai Sadik ne ya zama haka? Ya girma sosai, ko dan na daÉ—e ban ganshi ba?"
Daddy yace "Shine gashi ya zama big boy ba"
"Gaskiya girman É—an mutum ba wuya, kwata kwata yaushe muka je da kai a kai masa kaciya, ai nasan ba ze manta dani ko dan wannan ba"
Sadik a ransa yace "kutmar, ji ɗan rainin hankali wai suka kaini kaciya, abu ya wuce shekara goma sha, amma dan wulaƙanci wai an kaini kaciya dan cin zarafi, Allah yasa ma ba a gaban wanda zeji kunya ya faɗa ba, ya rasa dame ze tunani se sun kaini kaciya"
Saidk ji yai kamar ya yi tsaki, amma ya maze ya wuce, ba tare da ko sannun ku ya cewa abokan mahaifinsa ba.
Kuma hakan be damu mahaifinsa ba, dan yasan halin É—an nasa na rashin son mutane, da kula jama'a.
Da daddare bayan sallar isha'i, Sadik ya shiga cikin gida, dan gaba É—aya ya bar É—akinsa na cikin gida, saboda yawan mutane da suke zuwa gidan.
Ya tarar da Daddynsa da Mother, da su Usman a falonsa, suna tattauna maganar bikin Usman.
Prince yana zuwa ya haye kujerar da mahaifinsa yake zaun yace "bari in zauna ta nan inji É—uminka sosai"
Faruk yace "wai kaji É—uminsa, kamar wani wanda za'a shayar"
Daddy yai murmushi yace "kar ka damu ɗan auta mana, ƙyaleshi ya zauna kusa dani, nima ɗumin nasa zanji ai, nayi kewarsa sosai"
Ango Usman kuwa ɗan taɓe baki yai, saboda taɓarar da Sadik yake yi tana yin yawa, yaiwa Daddy yaiwa Mother, kuma lailaya shi suke kamar wani ɗanyen ƙwai.
"Auta na ga saƙonka kan in dawo, kuma shirye shirye sunyi nisa sosai, na tura kuɗin Neco da Waec ɗin ka, kamar yadda ka buƙata zaka kammala secondary this year ina sha Allah"
Cike da farinciki yace "Wow, thank you so much Daddy, Nagode sosai Allah ya ƙara Arziki me Amfani"
"Ameen My Son"
Mother tace "wai dagaske jumping za kai masa kenan? A ss2 yake fa"
"Ai ba laifi kin san yaron nawa ƙwaro ne, he can do it yace yana so, kinga ban san me yake hange da yace yana son ya kammala secondary School a wannan shekarar ba, may be he's planning something better for his future"
Mother tace "to ai shikenan, Allah ya bada sa'a, shine ni ko a gayamin"
Daddy yai murmushi yace "to ai gashi yanzu kin sani, kai kuma seka hanzarta gayamin jami'ar da kake so a waje, a fara processing tun da wuri"
Nan da nan jikin Sadik yai sanyi, dan yasan tabbas da zarar ya kammala makarantar nan, ƙasar waje za'a ce ya tafi karatu, Farhan ɗinsa fa zata iya jiran sa? Ƙaddara ma zata jira shi, shi baze iya jiran tsayin wannan lokaci, yana bautar biro da takadda ba, bayan shi abunda zuciyar sa take so daban ba, gaskiya Aure yake so, dan yafi damuwa da Yayi Aure akan wannan bokon.
"Ya naga kayi shiru? Ko baka son karatun ne?"
Ji yayi kamar yace baya so, Aure yake so ai masa Kafin karatu, amma yace "A'a ina so, ina nazarin wace jami'a zan tafi ne, don't mind me zanje inyi tunanin wace jami'a ta dace da ni"
Yai maganar yana miƙewa tsaye, Daddy yace "in wani abu ya shige maka duhu, ga yayyenka nan ko kazo ni ka sameni mu tattauna"
"To Daddy, Good night"
Yai maganar yana ficewa daga É—akin.
Da yaje nasa ɗakin ma kasa baccin yayi, ga ƙoshi ga kwanan yunwa.
Da ƙyar bacci ɓarawo ya sace Prince Sadik, saboda damuwar da yake ciki.
Washegari ya kama Asabar ranar da za'a kai kayan Auren Dr. Usman gidan Hakimi, wanda se an kai can sun kwana sannan za'a kai gidan su Yarinyar da ze Aura É—in.
Kaya sun kai kaya, akwatuna goma sha biyu ne na alfarma shaƙe da haɗaɗɗun kaya, masu tsadar gaske.
Lefen ya haɗu ƙarshen haɗuwa, haka aka zuba kayan a mota, za'a tafi.
Sadik yana saman bene, yana kallon yadda ake zuba kayan a Mota, ya É—anyi ajiyar zuciya yace "Allah ka nunamin lokacin da zan haÉ—a kaya fiye dana Dr. a kaiwa Farhan É—ina, a ce yau gani zan Aure nima.
Yana nan a tsaye aka ja motocin aka tafi dasu.
Shima komawa yai ɗakinsa, ya shirya cikin ƙananan kaya ya fice nasa guri, dan a 'yan kwananin nan zaman Gidan nasu sam baya masa daɗi.
Nana na tafe a hanya tana zura hannu a hijjabinta, tana rarraba ido kar taje wani ya kalleta a banza, Ta koma gida Inna ta gane, tana tafe tana ta sauri kamar wadda take da wani uzuri a gabanta.
Tana zuwa ƙofar gida ta tarar da cincirindon motoci a ƙofar gidan, dama tun safe ta ga ana dafe dafe a gidan, ta tambayi Inna me ake haka amma ta gaya mata baƙar magana, taƙi gayamata meke faruwa.
Fararan fararan ta shiga ratsa mutanen dake harabar gidan, ta shiga cikin gida.
Ta tarar da mata a zazzaune ana ta rangaÉ—a guÉ—a, banda masu bushe bushe da ta baro a waje.
Neman Inna ta shiga yi cikin lungu da saƙo na gidan, cikin sa'a ta hango Innan, ta sha Kwalliya.
"Innarmu wai me akeyi ne haka?"
"To tambaya, daga daowarki ko cire kayan makaranta baki ba, kin zo kin cikani da tambaya"
"To Inna ni duk an zo a cika gidan a ina zanje in canza kayan ko ina mutane"
"In kin gama fitsarar kya tafi kije ki canza kayan" Inna tai maganar tana cigaba da hada hadarta.
ÆŠakin Inna ta shiga ba kowa a ciki, ta cire kayan makarantar ta, ta zunduma uban hijjabi sannan ta shiga tai wanka, ta fito ta canza kaya.
Inna ta shigo É—akin zata É—au abu, ta ga Nana na binta da kallo, Inna tace "kayan lefen Usman aka kawo mu gani, sati me zuwa za'a kai shikenan?"
"Waye kuma Usman?"
Nana ta tambayi Inna, tana É—an tura baki.
"Au Usaman É—inma baki san shi ba? Iko se Allah to bari in miki yadda zaki gane, yaran nan masu tara gashi, na gidan Abdullahi"
Murmushi Nana tayi tace "Au se yanzu na gane, to ina kayan lefen suke?"
"Suna turakar Hakimi"
Nana ta zabura tace "bari inje ina gani"
"Ke bana son hauka, da baƙin a gurin zaki je? Kefa wani lokacin kwantacciya ce"
Nana ta É—an haÉ—e rai, dan taji haushin ce mata kwantacciya da Inna tayi.
Se la'sar sannan masu kawo kayan suka tafi, Hakimi yace a bar kayan a nan, Ranar da za'a kai lefen, za'a tafi dasu daga nan.
Haka kuwa akayi, aka tafi aka bar kayan a nan, akan se ranar da za'a kai sannan za'a tafi dasu.
Ko da labari ya ishi Mother an baro kayan lefen nan a ƙauye Gidan Hakimi, abun ya baƙanta mata rai, ta dimga sababi akan me za'a baro mata kaya a can, salon a sace musu wani abun, haka tai ta sababin ta ta haƙura.
Ranar Monday a school prince yai shirin ko ta kwana ko da Nazir ze gaya masa wata maganar banzan akan abunda ya faru Ranar Friday, amma yaga be kulashi ba.
Ita kuwa Farhan faragaba ta dinga yi, dan kar ya cimata mutunci, dan ta fuskanci ya tsane ta sosai, ba ita kaÉ—ai ke soyayya a makarantar nan ba amma yabi ya sa mata ido.
Cikin ikon Allah kuwa be tanka mata ba daga ita har Prince É—in.
Ana fita break kamar jira take, ta tafi ajinsu Prince, sun barbaje suna ta hira ana kwasar dariya, suna tsara irin yadda zasu raƙashe a bikin Yayan Prince da za'ai nan da wata ɗaya, wanda ze kama a cikin hutun kirsimeti da kuma sabuwar shekara.
Sallama tayi tana duba inda za ta ga Prince, yana kashingiÉ—e yana game a wayarsa, sedai in sunyi abun dariya shima yayi.
Duk d rashin son kallo da Farhan ba tayi, da kwarjini da 'yan ajin nasu Prince ke mata, hakan baya hanata shiga ajin in dai za ta ganshi, kamar yasan ta shigo ya É—ago aikuwa su kai ido huÉ—u da Farhan.
A tare sukayi murmushi yace "welcome my cwt"
A hankali ta tako cikin tafiyarta me É—aukar hankali.
Taslim ta kalleta ta É—an yatsuna fuska, dan yanzu haushi Farhan take bata tace "wai ke kam ba kya gajiya ne? Kullum cikin sintirin zuwa ajin nan ki ke?"
Take jikin Farhan yai sanyi, ta É—anyi sororo tana kallon Taslim, kuma Maganar Taslim tana kan gaskiya.
Prince yace "Taslim wallahi zan tatala miki rashin mutunci da baki taɓa tsammani ba, ina ruwan ki da ita? Me tai miki ko ajin daga gidanku ki ka zo da shi? Bana son haka ban sawa kowa ido ba, dan haka nima kar a samin"
Taslim tace "Allah ya baka haƙjri sarkin fushi, wasa nake mata"
"To ba'a san wasan" ya faɗa yana harar Taslim.
Ya kalli Farhan yace "ƙaraso mana"
A hankali ta ƙaraso tana ɗan wasa da yatsunta.
Kan ta zauna ya ɗan tsaya yana kuma ƙare mata kallo, girma Farhan take ƙara yi, ƙara buɗwa take ga wani kyau da take ƙarawa.
ÆŠan lumshe ido yai yana murmushi, ta zauna a É—an nesa da shi kaÉ—an.
"To ya, kina lafiya my love?"
Sunkuyar da kai tayi cike da jin kunya, tace "lafiya ƙalau"
"Ai tun É—azu naso in zo ajin ku, sedai nace bari in jira inga zaki zo?"
Murmushi kawai tayi ba tace komai ba.
"Nifa bana son wannan shirun, hira zaki min inji muryarki, kullum sedai ki zo ki kalleni kina murmushi, duk da murmushin naki burgeni yake, but say something"
"I have nothing to say" ta faɗa a ɗan shagwaɓe.
Dariya yai yace "muryarki da turancin kamar baturiyar England"
Seda ta É—an zare ido jin abunda Prince É—in nata yace.
"Farhan, an kusa bikin Yayana, zaki zo ko?"
"Yaushe ne?"
"Nan da 1month insha Allah, ai zaki zo ko?"
"Ina tunanin ko za'a barni inje a gida"
"Meyasa ba za'a barki ba?"
"Baban mu yana da tsaro sosai, ba'a barina fita sedai in a 'yan ajinmu wasu zasu je, su zo mu tafi tare, kuma ka bani kati in kai gida"