Sashe 9
Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga kansa yayi alamar eh, sannan yace"shine Najma, gasucan sun tafi shida shugaban asbitin"
Wajan da Abba ya nuna mata ta kallah, ta hangosu suna tafiya saide bayansu tagani, bataga fuskar kowa ba kasancewar Sunbasu baya, saide jama'ar datagani sunada yawa sun kai kusan mutum ashirin like wani gwamna,
hakan ya tabbatar mata dacewa lalle ko waye wannan ba qaramin mutum bane
Juyowa sukai cikin dakin itada Abba
Tana zuwa ta fada jikin Nawal ta rungumeta cikin murna tace "Babyyyyyy"
Tace "Najma zaki karyani,"
Daria tayi tace "Baby anbiyamiki kudin aikin ki, yarinya kiyi murna kin kusa hawa jirgi"
"me kike nufi Najma?"
Najma tace "eh da gaskiya nake, mutumin dakikaji muryarsa yana magana da Abba, shine yabiya kudin aikin ki gaba daya" ta kalli Abbansu daya zuba musu ido yana kallansu cikeda qauna tace "hakane ko Abba?"
Yace "hakane, yakarbi account number likitan dayake dubaki, zai turo masa kudin ta account dinsa, tare zamuje da shima ma, Ga wani kati dayabani ma yace ba sai mun sai ticket ba kawai idan munje airport din mubasu muce inji MK"
Yamiqawa Najma katin
Takarba tagani tace "Abba katinma kansa wallahi yayi kyau Dan qarami dashi"
Murmushi Abban nasu yayi baice komai ba, dadi yakeji aransa jiyake Kamar ansashi a aljanna ya maqale yaqi futowa
Ta kama hannun Baby tasaka mata katin cikin tafin hannun ta tace"To Baby kema riqe katin da hannunki kiji, Ga kati nan daga MK"
" MK "
ta maimaita sunan cikin ranta yayinda take shafa katin da hannun ta babu damar gani
Me hakan yake nufi kenan?
Mukhtar, muddassir, musa, mus'ab, muhsin, muhmood, muzaffar, mustapha, ko mubarak?
(niko nace duk ba daya
kin Manta da sunan babanki Baby )
Najma ce takatse mata tunanin ta hanyar qwace katin tabawa Abbansu "Abba Ga katinku wannan ba magana zatayi ba"
Abba yakarba yayi Murmushi, yana sake jin dadi cikin ransa, saide wani abu dayake masa yawo a qwaqwalwarsa shine yaro Kamar wannan meyasa iyayen sa zasu zuba masa ido su Barshi yana irin wannan shigar?
Kobashida da iyaye ne maraya ne?
To inba iyaye ma ai kana da makusanta wadanda zasu iya fadama gaskiya
Kawarda tunanin yayi aransa yadauki waya yakira Malam, yana dagawa yace "muhammadu yaya kukai da likitan?"
Abba yace "Malam ai zance yawuce"
"Kamar ya kenan?"
"yanzu de kana Gida ne??
Malam yace" eh ina Gida "
" to ganinan zuwa "cewar Abba tareda kashe wayar
Yakalli Najma" bari naje naga Malam, anjima Zan dawo mu qarasa tattaunawa da likitan naku"
Tace "to Abba agaida su mama, kace musu kuma abincinmu"
Yace "to babu damuwa Najma" tareda ficewa daga dakin
Yana fita tace "Najma shine nace kidubo minshi kikaqi ko"
Kallanta tayi cikeda mamaki tace "Baby anya kuwa wannan rashin lafiyar bayan idanunki Data taba banda tunaninki?
Nafita nagansu har sunyi nisa, tukunna ma kinsan da mutanan dayake tare?
Sunfi su goma sha, haka zanje na ratsasu ingano miki shi?
Kidauka ma naganshi, tayaya kike tunanin zance yazo nan d'akin ta yanda zaki sake jin muryar tasa?
Baby adauka ma yazo dakin, tayaya zaki ganshi?
Wani irin qullutun baqin cikine yatokare mata wuya, sai yau tayi baqin ciki da rashin idonta, cikin ranta tace "Allah ya'isa tsakanina da kai Anwar"
Ganin idonta nason kawo ruwa yasa Najma takama hannunta tace "kiyi hakuri Baby, insha Allah zakiji sauqi, murna yakamata kiyi kinji?
Ta shi Muje kiyi wanka"
Ahankali tasauko daga kan gadon, Najma tasaka mata takalmi aqafarta, ita kuma ta qarasa saka kafar tata ciki, sannan tajata zuwa toilet din
*** ***** ***
Abba yana zuwa wajan Malam yanemi tabarma ya zauna yabude ledar kudin hannunsa yadauki dubu dari biyu yace "Baba Ga kudin ka"
"mekake nufi muhammadu?
Kosunqi karba ne?"
"ai Malam yau Allah ne ya aiko mana da wani bawan Allah, ashe a'irin wannan zamanin akwai mutane masu qarancin shekaru da halin qwarai irin nasa?
Wallahi Malam wani baqo asbitin sukayi, nikuma naje Zan bawa likitan namu kudin shine wannan yaro yace yadauki nauyin komai nata, intaqaice maka bayani de Malam wallahi yaron nan yace afitar da Baby qasar waje ayi mata magani "
Malam yace" Allahu akhbar, Allahu akhbar, Allah Mai iko, Allah Mai yadda yaso, muhammadu kaga ikon Allah ko?
Kaga amfanin hakuri da yafiya ko?
"
Abba yace" nagani Malam, wallahi najima ina mamaki "
" ba abin mamaki bane muhammadu, ikon Allah yawuce nan, yakamata yau na zauna tareda almajirai ayiwa yaron nan saukar alqur'ani akan Allah yadafa masa, Allah kuma yaqara yimasa budi ta hanyar halak "
Abba yace "amin Malam, yanzu de Ga kudin naan, Allah yahutar dakai
Malam yace "A a muhammadu ai wannan kudin ba duka Zan karba ba, ka dauki dubu dari aciki kahada dana wajan ka a budewa Salisu shago babba yadinga juya kudin, idan Allah yayiwa abin albarka sai kaga Gida anhuta watarana"
"toshknn Malam, bari nawuce can Gida suma nayi musu bayani, zuwa anjima Zan dawo dasu Sultan suma muhadu ayi sauqar tare damu"
"bazaka tsaya talatu ta kawoma abin kari ba?"
Murmushi yayi yace "a a Malam zanci agida, agaida mutanan gidan"
"to muhammadu zasuji"
*** ***** ***
Suna zaune a dakin kowa yayi shiru, sai Najma datake waya da antynsu maryam dake zamfara
Amma gaba daya hankalin ta bayakan wayar da Najma takeyi, tunanin ta yatafi wajan tunawa da daddadar muryar datayi magana da Abbanta, tarasa meyasa muryar takasa barin cikin ranta, to wai ita menene natama na dagewa akan saita ganshi?
Muryar Najma ce ta katse ta, ta hanyar kama hannunta tasaka mata wayar tace "Ga anty maryam tana magana"
Ajiyar zuciya tasauke tace " Hello anty"
Itama anata bangaren tace "Baby nah ya jikin naki?
Dafatan de bakya tunani ko?"
"bana tunani anty, jiki da sauqi, yaushe zaki zo?"
"zanzo Abba ya hanani zuwa, amma insha Allah zanzo, yanzu naji Najma tacemin anbiya kudin aikin ko?
" eh wallahi anty wani yabiya "
" to Allah yasaka masa da alkhaairi, bari nakira gidan, sai anjimanku "
Tace" to anty "
Sunayin sallama da anty maryam nura yayi sallama suka shigo tareda Nuhu
Najma ce ta amsa musu, ita kuwa tanajin harda muryar Nuhu acikin masu sallamar tayi shiru
Sannunku da zuwa nuhu, Ga waje ku zauna mana, inji Najma
Yayi Murmushi yace" to Najma yaya Mai jiki?
"jiki da sauqi Nuhu, gatanan"
"to Allah yasawaqe, Allah yarufa Asiri"
Tace "amin," sannan tamiqe suka fice daga dakin itada nura
Yana ganin fitarsu yace "ya sayyida, yamukaji da hakuri kuma?"
Tace "Alhamdulillah," ataqaice
Yace "wallahi banida labari saboda inata kiran wayar taki akashe, sai da nazo Gida shine nakejin wannan mummunan labari"
Tace "wallahi kuwa"
"to Allah yabaki lafiya, ya ajiye leda me yallow da baqa cikeda fruit yace toga wannan kyasha"
Haushine yakamata wai ga wannan kyasha, saikace wadda take gani
Saita daure tace "to"
Daga nan sukai shiru gaba dayansu, sai shine yace "to ya labari"
"babu"
Yace "to shknn my heart Rabin raina, naga Kamar kin gaji, bari natafi"
"to sai anjima"
Kallanta yayi yasaki Murmushi, ganin fuskarta tayi futu-futu alamun batai murna da zuwansa ba
Yanada fita Nasrin tashi go dakin ita dasu Najma, itama suka gaisa dashi sannan yatafi tareda nura
Tana qaraso wa dakin tace "Beauty"
Lalume tafara itama tana nemanta
Tace "Nas ina kike?"
Kama hannayenta tayi tariqe "Beauty na, ya jikin naki?"
"jiki da sauqi Nas, kinga Anwar yahadani da masifa ko"
"gaskiya bai kyautaba wallahi, amma ai akwai Allah, waima menene yahadaki dashi ne?
Dama kinsan shine?
Nan take taabata labarin komai, Nasrin tayi ajiyar zuciya tace" Gaskiya akwai marasa imani agarin nan, amma kiyi hakuri Allah zai saka miki "
Najma tace" A a mukam ai munga sakayya Nasrin,
dan dazu wani bawan Allah ma yazo yabiya mata kudin aikin daza'a yi mata duka wallahi"
Nasrin tace "Dan Allah"
Kafin Najma tayi magana Baby tace "wallahi Nas ba kiji muryar sa ba me dadi, inajin maganarsa bansan lokacin dana saurara ba danna cigaba da saurarensa"
Gaba dayansu suka juya suna Kallanta cikeda mamaki
Najma tace "ni Baby ba Nuhu ne yazo yanzu bane?"
"shine mana, to Dan Nuhu yazo sainaqi fadar abinda ya birgeni?"
"gaskiya ne, amma kinsan hakan bai kamataba, tunda mutumin nan yana sanki, kuma kowa agida yasan dashi, sannan kema yan'uwan sa duk sunsanki, bai kamata kidinga yimasa wulakanci ba"
Nasrin tace "wannan gaskiya ne, wulakanci bashi da da dadi, especial ma akaan mutumin daya nuna yana sanka, idan bakya sansa kai tsaye ki fada masa mana"
Cikin haushi tace "bazan fada masaba Nas, shi mahaukacin inane da bazai gane cewa ba'a sansa ba?
Na nuna masa nanuna masa to menene kuma na dagewa bazai rabu daniba"
Nas tace "kai wasu mazanma de sai abarsu"
Najma tace "wallahi kuwa, mukam ina ruwanmu, tafadi haka tana janyo ledar fruit din gabanta
Dauko ayaba tayi tameqawa Baby tace " Baby Ga ayaba daga masoyi
" banaso Najma bazan ciba "
Tasake dauko apple tace" toga Tuffah"
Cikin bacin rai tace "nace miki bazanciba bazan ciba dole nene?
Kaje ma andanna ma wani asirin aciki"
Gaba dayansu suka sa daria, ganin yanda tayi kicin-kicin da fuskarta, lalle Nawal batasan Nuhu
*** ***** ***
Abba yana zuwa Gida yatarasu su Salisu da sauran yan Gida yafada musu abinda yafaru kowa sai murna yake yana hamdala, mama mariya tace "gaskiya Alhaji naji dadi, yanzu kaga sai kasai mana Mota maikyau wadda za'a dinga nunamu ana cewa oh su mariya ana can ana hawa motar wane da wane"
"mariya anya zakiyi hankali kuwa?kudin da ko zuwa hannu na basuyi ba?
Yanzu mariya koda kudin nan sunzo wajena wacce irin Mota Zan siya?
Me Mota zata tsinana min?