← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 48

Sashe 33

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu ta sume nan gaba kuma ai saide mutuwa
Ummi ce tafuto tazauna akusa da ita tace "Nawal,kiyi hakuri kinji, insha Allah Zanyi maganin Baffah, hakan bazata sake faruwa ba"
Murmushi tayi kawai ba tace komai ba, itakam batasan tada wannan magana
Sabirah ce ta kawo mata farfesun, ta zuba mata, tareda juyawa, ita kuma tadauka tafara ci
Saida tagama sannan Ummi takama hannunta takaita daki tace"ki kwanta kihuta, "
Ahankali tace" to Ummi ngd "
Kwanciya tayi agadon tana tunanin abinda yafaru akan gadon dazu, Baffah saikace wani kurma sai dukansa take amma ya qyaleta, shine ko kunyarta baijiba yacire kayansa, kuma agidan Ummi Dan rashin kunya, ai yasan zata sani
(nikwa nace harda text ma
Juyawa tayi ta kwanta ahannun ta na hagu, nan taci karo da wayarta awajan tareda takarda
Afili tace "meya kawo wayata nan kuma?

Tana dannawa taganta akunne, ga saqonni aciki, tasake cewa to waye ya kunna min waya?

Sunan Najma tagani dakuma na mtn, Dan haka kai tsaye tatafi ta bude na Najma
" _salamu alaikum, Baby dama kinsan mk kika aura shine ko ki kirani kin fesamin?"_
Cikin sauri tatashi zaune, gefen kanta yasara
Tasake bude na biyu tafara karantawa
" _Baby yaude naga mk dinki, yazo har gida munganshi, gaskiya Baby mk yayi "_
Ahankali tace" MK kuma?

Tayaya?

Tana nufin Baffah ne mk?

Kai bazai iyuba
Kiran Najma tayi, dama Najma jiran kiranta take dan haka cikin sauri ta daga tace"Baby ta mk, Wato kinsamu mk shine koki bamu labari 'yar renin hankali "
" Najma wai wacce irin magana kike?

Wanne mk kike nufi?

"
" MK de naki, Yazo gida, Abba yana ganinsa ya ganeshi, ingaya miki Malam ma yazo suka gaisa, nadinga kiranki wayarki akashe "
Idanunta ne suka kawo ruwa, nan take ta fashe da kuka, tace" Najma nashiga ukuna, Baffah ne mk?

Ya akai nakasa sani?

"
" to menene abin kuka kuma?

Keda zaki godewa Allah?

Kinga wannan shine amfanin yiwa iyaye biyaiya, lokacin dakika cewa bakya sansa da sun qyale ki shikkenan kin rasa shi "
Kasa bawa Najma amsa tayi, kawai kuka take rinzawa, irin wahalar dasuka sha itada Nas
Najma tace" toga ummah zakiyi magana da ita "
Tanaji ummah ta karbi wayar tace" ke komai abun kuka bayayi miki wahala?

Menene abin kuka anan?

Keda zakiyi murna?

Abinda kike so nefa, "
Cikin kuka tace" Ummah ya zanyi?

"
Ummah dabata fahimci Inda maganar tata tadosa ba tace" addu'ah zakiyi, ki kuma godewa Allah, wallahi yazo, mun dade dashi anan har abinci ma yaci, shi yama Manta da abban naku, saida yatuna masa, nadinga nemanki awaya amma wayarki akashe "
Ahankali tace" to ummah nagode "
Ummah ta qara yimata fada akan biyaiyar miji sannan takashe wayar
Kuka taci gaba dayi sosai, yanzu mk dinta ta qonawa kaya?

Shi take kira d'an cirani
, marar imani?

Hawaye kawai take zubarwa, Awannan halin ta kira Nas, cikin kuka tace"Nas naga ta kaina bansan ya zanyi ba "
Gaban Nasrin yafadi tace" subhanallah, beauty me yafaru?"
" Nas ashe Baffah shine mk?

Ina zaune da mk gida daya amma nakasa sani?

"
Nas tace" Innalillahi wai Dan Allah da gaske kike?

"
Cikin kuka tace" da gaske nake Nas, yanzu ummah take fadamin itada Najma "
" ikon Allah, wannan shi ake kira da ikon Allah, Inda munsan shi zaki aura Allah Bazamuje Abuja har ana zaromu daga adedeta ba
Amma kiyi hakuri, kidena kuka, Allah yakamata ki godewa "
Kawai kashe wayar tayi, ta dora kanta a cinyarta tana kuka
" _kince kina sona why zaki hanani haqqina?_ "
Maganarsa tadazu ta fado mata, kenan su ummah sun bashi labari, meyasa bazai cemata shine mk ba?

Meyasa?

Juyawa tayi tadauki takardar data gani tareda wayarta, Ahankali tafara budewa har tayi tozali da kyakykyawan rubutunsa
Tana gama karantawa ta cukwikwiye takardar ta rungumeta a qirjinta tana kuka, Ahankali take cewa "wallahi shine, wallahi shine"
Ummi ta turo kofar dakin tashigo taganta azaune ta rungume qirji tana cewa wallahi shine
, sai tayi tunanin abinda Baffan ya yi mata ne yasa take wannan kukan
Shiru tayi tana Kallanta, ita kanta abinda yayi baiyi mata dadi ba, rashin tausayin yayi yawa, sannan banda rashin kunya irinta Baffah shine acikin gidan ta zaiyi wannan abun
Ina laifin ma sukoma gidansu
Zama tayi agefen ta tace "Nawal kiyi hakuri, insha Allah Zan yi masa magana, bazai sakeba kinji"
Daga mata kai tayi kawai, tana share hawayen idonta
Ummi tace "na kirashi bai ban sameshi ba, ko zaa ki gwada kiransa muji?"
Tambayar ce tazo mata a bazata, itada batada number sa ta yaya zata kirashi?

Kame Kame tafara tace "ummi, k..

Kawai.

Kibarshi"
"Nawal kenan, naga alama bakida hankali"
daga haka tatashi tabar mata dakin
Tana ganin fitar Ummi ta koma gadon ta kwanta, idonta yana zubar da hawaye
Kawai tunanin abubuwan datayi masa marasa dadi take, Inda tasan shine mk yanda take nemansa ido rufe aida tuni ta dade dajawo hankalin abinta
But abinda ya daure mata kai shine yaya akai yasan sunan Baby?

Kodayaje gidane yaji suna fada?

Amma gashi acikin wannan latter da yabar mata Baby fal bakinsa
, Yaya akai yasani?

Wannan amsar tana wajan sa shi kadai
Haka tadinga tunani, still hannunta na dauke da takardar dayabar mata ta rungumeta sosai
Ahaka bacci ya dauketa
*** ***** ***
Tunda yatafi yakasa samun nutsuwa, tunanin halin da yabarta aciki kawai yake, ko Ummi taje?

Yanzu da wanne ido zai kalli Ummi bayan ya yi wannan abun agidan ta?

Abin akwai nauyi sosai
Juyi yasake yi agadon sa, ya kalli gefen sa yaga Babu kowa, daya sani ma Babynsa yadauko kawai suka taho nan
Yana son sakata a Kirjinsa ya lallasheta, yau rungumeta suyi bacci ahaka, yauga abinda yake mafarki a rungume tare dashi
Tsaki yasaki, yatashi zaune ya kalli agogo, bazai iyu yatafi yanzu ba, amma dole gobe zai tafi da sassafe, gara yaje ya fuskanci Ummi da hukuncin ta
Gara yaje yabawa Babynsa hakuri, yanason sake jin dumin matarsa, yasan cewa shime laifi ne a gareta, gara yatafi kawai
Yadade yana tunani kuma bacci Yaqi daukar sa, yasake kallan agogo yaga dare yayi a Nigeria, idan ya kunna waya yakirasu ma yasan cewa sunyi bacci, Dan haka shima saiya hakura ya kwanta
*** ***** ***
Washe gari dasafe Ummi ce dakanta tahada mata Ruwan dumi tace tashiga, daqyar da runtse ido tashiga, sannan Ummin tafuto daga ciki, tareda rufo mata
Haka tadinga sakata tanayi harta danji dadin jikinta, sannan ta shirya tafuto falo Inda Ummi take, ta zauna agefenta
Sabirah tazo tace "Anty Nawal me kike buqata akawo miki?"
Ahankali tace " Tea"
Sabirah tajuya tahado mata shayi Mai kauri, sannan ta koma kitchen
Ahankali take shan Tea din, tana kallo, amma zuciyarta gaba daya tatafi wajan mk
Tunanin sa kawai take, ko ina yatafi?

Ummi kuwa wayarta tana hannunta, ko yanzu ma ta gwada kiransa amma akashe, yatafi yabarta shida aiki itada jinya
in banda shirman Baffah duk kulawar da zata bata ai batakai tasaba, amma haka kawai yagudu yabar yarinya
Tana wannan tunanin taji yayi sallama yashigo cikin falon
Da Ummi yafara hada ido, cikin sauri Kamar munafuki yasunkuyar da kansa qasa sannan yafara sosa qeyarsa
Ummi ta zuba masa ido tana kallansa, takasa magana
Nawal dinma kallansa kawai take, Ahankali ta masa masa sallamar dayayi
Qasa qasa yake kallan Ummi yaga de har yanzu kallansa take
Ahankali yafara takowa zuwa cikin falon, har ya qarasa shigowa ciki, kai tsaye yaje gaban Nawal yazuba gwiwoyinsa aqasa,wato kneel down sannan yahade hannunsa guda biyu waje daya
yace " Baby, Baby nah please kiyi hakuri kiyafemin"
Ummi ta zuba musu ido tana kallan sabon salo awajan Baffah
wai harda cewa Babynsa, ko yaushe Baffah yafara wasan kwaikwayo bata saniba
Kawarda tunanin nata tayi, tana kallan su, tanaso taga wanne irin hukunci Nawal din zata masa?
(tuba nake fan's, nasan jiya anjirani anjirani ba adadi, kuyi hakuri, akwai aikinda nayi ne shiyasa bansamu damar typing da wuri ba, kawai saina barshi nace mahadu gobe
, dafatan wad'anda sukayi ta zuba idon ganina sukaji shiru zasumin uzuri
Sharhi Dan Allah
Amnah El Yaqoub
[2/9, 10:59 PM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
37&38
Ahankali ta ajiye cup din hannun ta, akaro na farko data fara kama hannunsa da kanta, hannayensa ta kama tasaukar dasu qasa tace"baka buqatar neman yafiyata, nadade dayafema duk abinda kamin,"
Idanunta ne suka ciko da qwallah still hannunsu yana had'e dana juna taci gaba da cewa" meyasa Dan Allah?

Meyasa baka fadamin kaine mk ba?

"
Tana kaiwa nan hawaye suka qarasa sakko mata
Ganin tana kuka yasa shima idonsa yafara cikowa da ruwa
Yayi qasa da muryar sa Kamar Wanda yake mata rad'a, daga ita saishi ne kadai zasu iya ji yace" kin hakura?

"
Murmushi tasaki, ga hawaye yana zuba ta daga masa kai alamun eh ta hakura
Yasake yin qasa da murya yace"Nagode Baby nah, kibari latter zamuyi magana kinji?

"ya qarasa maganar cikin sigar lallashi
Still ba tayi magana ba tasake d'aga masa kai
Ummi na gefe tana ganin ikon Allah, saita zuba musu tana kallan su Kamar a film, da alama sun Manta da ita awajan
cikin zuciyarta tace Tijara
Anya kuwa Baffah ba kwalli yasaka a idonsa ba yarinyar nan tana ganinsa taji tahuce?

Nida nake jira naga ta wanka masa mari
shine ta zauna tanayi masa kuka?

Shikuwa Baffah me yataka?
Chapter 33 · 0% Book details