← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 48

Sashe 10

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinake Ga yara nan agabanki har mutum uku, nura, saifu dakuma Najma, aisu yakamata ace kinyi tunani sun tafi makaranta, to kinga ni bazan sai wata Mota inbar 'ya'yana cikin jahilci ba"
"to Alhaji nawane sukai karatun babu aikinyi?Ga Salisu nan shekararsa nawa dagama karatu babu aikinyi, ko 'yar adaidaitar nan baisamu tajaba
Shikuma Sultan gashinan kullum a qarqashin wasu yake, shima babu na kansa, haba ni wallahi nagaji da kashe kudin karatun nan babu aikinyi "
" kinsan da hakan kika daga hankali lokacin da Nawal zata tafi makaranta kikace saide Najma taje?"
" Alhaji Dan Allah kayi hakuri kabar wannan maganar, tare Muke da yarafa "cewar umma
Abba yace" Allah ya kyauta,to nide naje wajan Malam mungama magana dashi, kudin dana saida filina guda daya, yaqaramin dubu dari akai, Dan haka za'a budewa Salisu shago yaci gaba da juya kudin, koda ace ba'a samu albashi ba, akwai abin dogaro daki, kai kuma Sultan Ga kudin ka, kakama hanya kakoma bakin aikinka, daan Allah karnaji karnaga kayi fada da kowa musanman Anwar, domin kuwa nasan halin ka "
Sultan yace" to Abba, amma cikin ransa bai qyale ba, bayajin akwai Wanda zai taba Baby yaqyaleshi, babu shi
sannan yaci gaba da cewa amma Abba wannan kudin kabar shi wallahi, ahada da shima a kudin shagon, Allah yaqara hore mana gaba dayanmu"
Dukkaninsu suka aamsa da amin
Saif yace "Abba kuma yaya Baby tare dawa zasu tafi qasar wajan?"
"Dani da ita dakuma likitan dayake kula da ita, Dan kudin ma ta hannunsa zaizo, dole anjima Zan koma naji yaya zai tsaara mana tafiyar"
Cikin farin ciki ummah tace "to Allah yasaka masa da alkhaairi, shima Allah ya bashi Wanda zasu taimaka masa Kamar yanda ya temakemu"
Abba yace amin, tareda miqewa, ya kalli su Sultan dasu nura yace "anjima kuje gidan Malam akwai karatu, nima Zan biyoku idan nadawo daga asbitin"
Suka amsa masa da to, shikuma yayi cikin d'akinsa
*** ***** ***
Saida aka kawosu har kofar gidan su sannan ya kalli abokin nasa "MK mungode sosai, Allah yasaka da alkhaairi ubangiji Allah yayi ma...

Dakatar dashi yayi ta hanyar daga masa hannu," Yas babu godia tsakanina dakai "
" to shikkenan, nagode sosai, yanzu Abuja zaka wuce?"
" no , bazan shiga Abuja ba, saboda Ummi ma batasan nazo ba, ina ganin Zan wuce Dubai"
"toka shiga mana ku gaisa dasu mama"
Murmushi yayi kawai batare dayayi magana ba, Wanda hakan ya tabbatar wa da yasir cewa bazai shiga gidanba, Dan haka yace "toba damuwa Allah yakaika lafiya"
Ya yunqura zai fita daga motar yayi sauri yace "Yas"
Zuciyar yasir daya yajuyo yana kallansa yace "na'am?"
Cikin ransa yace To yanzu dana kirashin mezan cemasa?

Kasan Baby?

Kokuma ina zanga Baby?

Yarinyar da sunan ta kawai yaji baisan taba, baisan kamarta ba, saide Beautiful lips dinta daya gani sau daya
Dan haka yashare kawai
yace "shikkenan babu komai ma sai munyi waya kawai"
Yasir yace " Ok , tareda fita daga motar, sukuma sukaja suka tafi
*** ***** ***
Washe gari kuwa kudi suka shigo ciki account din Doc.yanemi Abba suka fara shirye shiryen tafiya Abania , kuma alhmdlh komai sunyi shi cikin kwanciyar hankali, cikin kwana hudu jirginsu yatashi daga MALLAM AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT zuwa
TIRANA INTERNATIONAL AIRPORT dake ALBANIA ( nene tereza )
Abangarensu Yasir suma sun tafi Germany shida qaninsa, already shi din Dan boko ne daya samu budewar ido awata qasa, shiyasa suma basu sha wahala ba wajan tafiyar tasu tareda Mu'azzam da taimakon likitan dake duba qafar yaron
*** ***** ***
Abu Dhabi
Babban birnin Dubai
Babban d'aki ne mai mutuqar girma daya amsa sunansa daki, babu wasu takarce masu yawa a dakin face gadonsa da wardrob, sai kujeru masu Ruwan zuma dasuka qara qawata dakin
Sai Dan qaramin kafet ashimfide agaaban gadon Mai launin baqi da Ruwan zuma
Da wata uwar plazma dake manne abangon dakin, tanada girma sosai kadan yarage tacika bangon dakin, girman ta yayi yawa, saikuma dressing mirrow dake cike da kayan qamshi, akan bedside drower computer sace qirar Apple Mai launin baqi
Kwance yake yana bacci hankalinsa kwance, bargon daya rufa dashi shima baqi ne da Ruwan zuma irin me laushin nan Kamar jikin mage
Gaba daya ya tattare bargon zuwa gabansa ya rungumeshi
Mafarki yake ga wannan de me mashin dinnan yataho da dugu zai sake kad'eta, cikin sauri kuma da karfi yace "BABY!!!

"
Adede lokacin yafarka daaga mafarkin da yakeyi, yatashi zaune tareda yaye bargon daya rufa dashi yayi wurgi dashi gefe guda yana maida numfashi Kamar Wanda yayi tseren gudu
Jikinsa na kalla babu vest ajikinsa bare riga, qirjinsa gashi dayawa baqi ya kwanta, sai gajeren wando ajikinsa Mai launin baqi
Kai Nawal yakamata kisayaya wa mk haka
koba hakaba fan's
Please sharhi sharhi sharhi Dan Allah
Share please
Amnah El Yaqoub
[1/27, 9:52 PM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE...
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
11&12
Baqin ciki ne da takaici suka kamashi, wai meyake damunsa ne?shikkenan daga ganin yarinya duk yabi yad'aga hankalin sa akanta?

Yarasa meyasa zuciyarsa take azalzalarsa akanta, qwaqwalwar sa takasa goge sunanta,meyasa yadamu da lamarin yarinyar haaka?

Yanaji aransa yanaso yasake ganinta koda sau daya ne, but meyasa hakan?

Ba kasafai fararen mata suke birgeshiba because of acikinsu yake, kullum suyake gani, kuma su din yatashi yaana gani, koda ace soyaiya zaiyi bashi da ra'ayi akan farar mace gara yayi mix shi fari ita baqa
That's why yakesan abu baqi, hatta kayansa kuwa da Komai na cikin d'akinsa da toilet dole sai kaga baqi
Amma kuma ya daga ganin yarinya zai mamuqata acikin ransa harda wani mafarki, kuma yarinyar ma qanwar qanwar bayansa, kawai hakurinta ne yabirge shi
Afili yafurta "Tausayi ne kawai, ba abinda nake tunani bane, Tausayi ne kawai" (
tofa)
Daga haka yatashi tsaye gajeran wandon nasa duk ya baiyanar da shacin komai
miqa yayi tareda kallan murdaddan hannunsa sannan yashige toilet
*** ***** ***
Kwanansu daya da zuwa qasar ta Albania aka gama duk wani shiri akan aikin idonta, sun riga sunbiya kudin komai washe gari za'a yi mata aiki
Washe gari kuwa tunda safe aka sauya mata kaya basufi minti ashirin ba aka shiga da ita d'akin da za'ayi mata aikin
Abba yayi shiru yana tunani, da yanzu fa a Nigeria za'ayi mata wannan aikin nanda wasu watannin, domin kuwa shide yasan kansa, yasan cewa bashi da hanyar dazai saimu wannan kudin saide Ahankali adinga ta rawa harya biya
Likitan daya rakosune ya bubbuga kafadar Abba "Alhaji kayi hakuri, ba wani aiki ne dazai dauki dogon lokaci ba, insha Allah lafiya zasu futo"
Abba "yace to likita Allah yasa, Allah yasa adace"
Yace "amin Alhaji"
Ko cikakkiyar awa biyu basuyiba suka futo,tana kwance akan gadon yayinda likitoci guda biyu suka turo gadon zuwa dakin da aka basu
Cikin sauri Abba yatashi yanufesu saide basu tsayaba saida suka danganata da d'akinsu
Daukarta sukai suka dorata akan gadon, suka gyara mata kwanciya, annad'e idonta da bandeji fari, kanta babu dankwali gashinta Mai tsantsi yazubo har bayanta
fita sukai daga dakin, likitan daya jagoranci aikin ne yashigo dakin fuskar sa daukeda Murmushi, ya d'aura mata ruwa sannan yadubi Abba da likitan "congratulation, aiki yayi kyau angama lafiya, yanzu anyi mata allurar bacci, zata dauki tsawon lokaci tana bacci kafin tafarka
Idan tatashi kada kubari ta dinga sunkuyar da kanta qasa, duk wani abu dazaisa ta sunkuya qasa ba'aso tayi, saboda yin hakan zai iya haifar da wata matsalar, insha Allah zuwa gobe za'a cire mata bandejin sai kuma mugani yaya ganin nata zai kasance, shin zata gani kokuma sabanin haka, amma mude anamu bangaren mungama aiki normal babu wani problem, saide muyi fatan rashin matsala bayan tafarka "
Murmushi ya wanzu afuskar Abba, har likitan yagama bayani kawai cewa yake insha Allah, insha Allah"
Likitan dasukazo dashi daga guda yabawa dayan likitan hannu suka sake gaisawa yayi masa godia da jinjina sannan shikuma yafice yabar su a dakin
Waje suka nema suka zauna bakin Abba yakasa rufuwa sai farin ciki yake
Yadauki wayarsa yakira Nigeria
Umma yakira a lokacin wayar tana hannunta, Dan tunda yace mata yau zasuyi mata aiki ta riqe wayar tana jiran kiransa yashigo, kiran nashigo wa kuwa tayi sauri tad'aga
Cikin farinciki Abba yace" Safiyya, kiyi farin ciki kiyiwa Allah godia, anyi aiki lafiya, gatanan a kwance tana bacci, likitan yace zuwa gobe zasu cire mata abin idonta, sai muyi addu'ah kuma Allah yasa anyi a sa'ah"
Tace "Alhamdulillah, Allah abin godia"
Salisu da Sultan dake gefenta sunajin furucinta suka fara Fara'ah
Sultan yace "wayyo umma Dan Allah sakata a handsfreee"
Shi kam Salisu qwace wayar yayi daga kunnanta yasaka musu ita a handsfree, nanfa sukaji komai, Kamar ba samari ba haka suka d'auki ihun murna, hakan ya janyo hankalin yan gidan duk sukayo falon ummah kowa yana tofa albarkacin bakinsa, yau kam mama mariya ma daka ganta zaka tabbatar tayi farin cikin jin wannan labarin
Anan fa Gida ya kaure da murna, kowa yana hamdala cikin ransa, Abangaren umma kuwa addu'ah take ta kwararowa wannan bawan Allah daya biyawa yarta mace qwaya daya kudin magani
*** ***** ***
Doc.

Yadubi Abba "Alhaji zandan fita nasiyo mana wasu abubuwan dazamu buqata kafin allurar tasake ta insha Allah Zan Zan dawo"
Abba yace "to likita adawo lafiya"
Likitan nafita Abba yakama hannun 'yarsa yariqe yana Kallanta, fatansa daya Allah yasa adace akan aikinda akayi
Yana zaune shiru har likitan yadawo da kaya ahannun sa, rigar sanyi ce yasiyowa kowa da kuma fruit da sauran abubuwan dazasu buqata
*** ***** ***
"usy yakake yagari"
"lafiya Sultan , ya kwana biyu"
"alhmdlh wallahi, ina kaga Anwar ne? , inata nemansa banganshi ba, Allah yasa yana gari
Usy yace"aikuwa Anwar baya nan, idan baiyi sati d'aya da barin gariba to yakusa sati gaskiya, me yafaru?

"
Sultan yace" wallahi nemansa nake ruwa ajallo usy
, akwai maganar da zamuyi Mai muhinmanci "
" kai Sultan ka fadamin gaskiya mana, meyake faruwa kake neman Anwar?
Chapter 10 · 0% Book details