← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 48

Sashe 34

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali tayi gyaran murya, cikin sauri suka kalleta gaba d'ayansu, atare suka saki hannun juna, shikuma yatashi daga Gabanta ya qaraso kusa da Ummi ya zauna aqasa tareda sunkuyarda kansa
Kallan Nawal din tayi tace"tashi ki wuce daki kije ki kwanta kihuta, mutumin da ya kusan kaiki lahira kika zauna kinawa kuka
Ahankali tatashi tana tafiya da dingishi
Dago kansa yayi yaga yanda take tafiya, tausayinta ya kamashi, satar kallan Ummi yayi yaga itama Nawal din take kallo
Babu bata lokaci yatashi yabi bayanta, yana zuwa yasa hannu yadauketa cak, sai cikin dakin datake
Ummi tabi bayan su da kallo tana magana cikin ranta, ba kalau Baffah yabar Nawal ba
Suna shiga dakin ya kwantar da ita akan gadon, yadora mata kanta akan fillo, sannan ya zauna agefenta, ya zubawa fuskarta ido, itama shi take kallo Kamar sunga sababbin halitta
Babu Wanda yaceda dan'uwansa komai, Ahankali yadora hannunsa saman lips dinta ya shafa na qasan, cikin muryar rad'a yace"meyasame su suka qarayin ja?

"
Shiru tayi takasa bashi amsa, shima kuma bai daina shafa lips dinba
Yasake Kallanta yace" uhm?meyasa me su?

"
Towai itakam meyake so tace masa?

Kaine kasha kokuma Babu komai?

Hawaye taji ya gangaro mata Wanda itama batasan dalilin zuwansu ba
Dena shafa mata lips din yayi, Ahankali yakawo Fuskarsa dab da tata, tana ganin haka ta lumshe idonta, saukar harshansa taji afuskar ta, hawayen daya zubo mata yasa harshe ya lashe su tas
Sannan yace "ina zuwa, zanje wajan Ummi"
Bai jira amsarta ba yaqara jamata bargo yafita daga dakin
Ummi taji Baffah da Nawal shiru
tasaki ajiyar zuciya tace "kome yake qara kitsa mata?"
, nide Babu Inda zan bisu
, tunda yazo har gida yayi wannan abun idan nabi bayansu kuma ai Zan iya ganin abinda yafi karfina
Dan haka saita zubawa tv ido tana kallo
Shima yana futowa daga dakin
Yazauna agaban Ummi tareda sunkuyarda kansa qasa yana jiran sakamako
Wayar hannunta ta ajiye takama kunnansa guda daya ta murde
Cikin sauri yariqe kunnnen yace"Aucch!

Ummi Dan Allah kiyi hakuri "
Kunnan tasaki sannan ta kalleshi dakyau tace" Wato Baffah saboda nace kasaki Nawal shine ka aikata mata haka danta samu ciki nace najanye zancen sakin ko?

"
Kansa ya shafa, cikin sanyin jiki yace," Ummi kiyi hakuri, nayi kuskure"
Ta kalleshi taga sosai maganar daga
Zuciyarsa take, ba qarya yakeba, tace"to saki yana nan Baffah, ban fasaba "
Cikin sauri ya kalleta yace" Ummi Dan Allah kiyi hakuri, wallahi nasan nayi muku laifi, umm insha Allahu bazan sakeba "
Tausayi yabata, amma danta sake gwadashi tace" toni narasa gane kan wannan aure naku Baffah, bakasan yarinya, sannan ka lallaba kayi abinda kayi
sannan kuma kaqi sakinta "
Cikin sauri yace" Ummi wallahi ina sonta
, Dan Allah Karki rabamu Ummi, wallahi idan nasake ta akwai matsala Ummi "
Murmushi Ummi tayi, ko banza yau de yabude baki da kansa yace yana sonta, godia tayiwa Allah cikin ranta, sannan tace" to shknn Baffah, komai yawuce, amma karna qarajin kayiwa yarinyar nan abu irin haka
, Baffah ina tausayin ka yatafi?

"
Jikinsa ne yayi sanyi, yace" Ummi insha Allahu nadena, Dan Allah kiyi hakuri, ummi itama na bata hakuri, kuma tace tayafemin "
" A a ni Al'amarin Nawal ai nasan ba kalau kabarta ba
Murmushi yayi, baice mata komai ba
Takalleshi taga har yanzu Yaqi hada ido da ita, ciki ranta tace "um su Baffah yau yaushe
, waishi ma nan ya girma
Dagowa yayi ya kalleta suka hada ido, yayi saurin sunkuyarda kansa
Murmushi tayi tatashi tsaye tace" to inka gama jin kunyar Umminka sai anjima nina tafi nahuta "
Saida yayi Murmushi sannan yace" Ummi idan kin futo Zan baki wani labari "
"labari kuma?"
Miqewa yayi tsaye shima yace "yes, dangane da Baby"
Murmushi tayi tace "to masu Baby, harka saka mata suna kenan"
"Ummi ai shiyasa nace Zan baki labarin, kede saikina futo" yana fadar haka ya yi dakin da Nawal take ciki
Ummi tayi sauri tace "Baffah dawo, babu Inda zakaje
kai likita ma yace abarta tahuta, inso samu nema surutu ma kar amata
Murmushi yayi ganin yanda Ummi take kaffa kaffa da Nawal yace" Ummi sallama zanyi mata kawai zanfita unguwa ne "
Tace" to yanzu naji zance, yi sauri kafuto minti biyar "
Yace" to Ummi sannan ya shige dakin"yana shiga yahaye gadon shima ya kwanta, ya janye Bargon daya rufa mata, Ahankali ya janyo ta jikinsa tareda dora kansa agefen wuyanta
Bude idonta tayi ta kalleshi, cikin sauri ta sunkuyarda kanta qasa, gaba daya yasaka ta a Kirjinsa yahanata motsi
Cikin rada yace"natasheki ko?

"
Shiru tayi masa, gaba daya ya yi mata kwarjini, gashi ya qaqumeta yahanata katabus
Ahankali yadora bakinsa akan kunnenta yafara lasa
Wani iri yarrr taji a jikinta, cikin kunnanta yace" please fadamin yaushe kika fara son mk?, ya maida idonsa kan kirjinta yazuba musu ido yace "bani nasha"
Kallansa tayi yace abashi labari yasha amma kuma idonsa yanakan nono
Ahankali tadanyi baya kadan, yasake janyo ta jikinsa yace "inajin ki"
Ahankali tace masa "saika fadamin yaushe kasan sunan Baby"
Murmushi yayi, yadora hannunsa akan gashin idonta yafara shafawa, Ahankali ta lumshe idon, yaci gaba da shafa mata idonta, sannan cikin rad'a yace "inbaki labarin kinason ji?"
Ahankali ta d'aga masa kanta
(mk kode ya Manta Ummi tana jiransa ne
Duk yanda kukaga nayi posting Dan Allah kuyi hakuri kuce sannu
, ni kaina banso na tsaya anan ba wallahi, amma kuyi hakuri da ace banyi posting ba gara ku samu ko yaya ne, inajin dadin yanda mutane sukemin sharhi wallahi, babu abinda zance da masoyan ni dake sai godia, nagode mgode naagode sosai
Mrs Usman ce
[2/11, 6:27 PM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
39&40
Cikin nutsuwa yafara cewa "Tun lokacin dana ganki mai machine ya kad'eki
Sainaji Kamar ni aka kad'e, abinda yafi bani mamaki yakuma yad'auki hankali na shine yanda aka kad'ekin amma kuma kika tashi kika tafi batare dakin yi masa fad'aba kamar sauran mata, wannan ne yaja hankali na gareki naji kinbani tausayi, nafara tunanin dududu ma nawa kike dazaki d'orawa kanki wannan abubuwan, nafara tunanin anya za'a samu Mai hakuri Kamar ki kuwa a yanzu?

Naga Wanda ya bigekin yana kokarin tafiya batare daya kaiki asbiti andubaki ba, nafara yimasa magana amma inaa har yaja yatafi, nawaiga kozan ganki kema naga Babu ke kwata kwata, banji dadi ba a lokacin, mukaje wajan gaisuwa, har muka dawo ina waigen hanyar dana ganki
Yakalleta cikin ido yace"tundaga lokacin nafara tunanin ki, gashi ban ganki ba, saide lokacin da aka kad'eki kince wayyo kuma abinda kikasa a fuskarki yad'an yaye anan naga lips dinki, dakuma sunanki danaji wasu yara sun ambata, nafara qarya ta kaina cewa ina sonki, kawai tausayinki yasa nake tunanin ki, daga baya de abu yaci gaba harna fara mafarkin ki, still ban yarda ba nabarshi a tausayi, saida Ummi ta auramin Nawal,
anan nashiga tashin hankali, kuma nasan cewa lalle inason Baby
Kullum saina tunaki, zuciyata bata samun nutsuwa idan banyi tunanin kiba, tunanin kine yasa nakasa kwantar da hankalina inkula dake, naje wajan limamin unguwar nan shima yabani shawara akan nayi hakuri naso mata ta kuma nabada bincike akan Baby
Tundaga lokacin nasa yasir Abokina yafara yimin bincike akan Baby, nikuma na shirya natafi saudia nayi addu'ah akaan Allah yabaiyana min ke, ashe bansaniba kece kike tare Dani, ashe dake nake tare harna bata lokacina wajan kiran Mai zane yazanamin ke, nasan cewa nashiga haqqinki amma pls kiyafemin, yayi qasa da muryar sa yace "kinji?"
Kai tsaye ta jefo masa tambaya a maimakon amsa "dama kana surutu haka?"
Murmushi yayi yace"ina yiwa Ummi, sannan Inayiwa Nawal lokacin da kishinta yakama ni nakira Mai sunan saurayinta nadinga zuba masa surutu akan ya wanke min motocina duk Dan taji haushi
, saikuma Baby nah dazan zauna inyi ta miki zance idan kinaso"
Itama Murmushi tayi, tace "Sai yanzu nagane ma'anar zoben nan guda biyu Wanda aka sakawa kowanne harafin B ajikinsa"
Yace "yes Baffah & Baby, means BB, wato har bincike kikai adakina bayan qone kayan?"
Rufe idonta tayi, da hannunta
tace"kayi hakuri, shawarar qawata nabi "
Yace" nadade dayafe miki Baby nah, yanzu bani labarin mk "
Kafin tafara bashi labarin suka jiyo alamun tafiya a kofar dakin, anqi ashigo amma kuma sai taku ake agaban dakin
Zaro ido yayi
yace" Ummi ce wallahi namanta, "yayi sauri yaduro daga gadon
Yanda yasakko din har daria yabata
Futowa yayi daga dakin aikuwa saiga Ummi a kofar daki tana safa da marwa ta kuma kasa shiga
Ta kalleshi tace" Baffah yadaga baka minti biyar ka shanyani awaje sama da Rabin awa
Kansa ya sunkuyar yace" Ummi kiyi hakuri wallahi namanta
Tace" Baffah, Baffah, Baffah nakiraka sau uku kabar yarinyar nan tahuta, likita yamin kashedi cewa abarta tahuta Baffah, karnaji karna gani Baffah
Daria ta bashi, wai shine yazama haka awajan Ummi
, kansa aqasa yace" Ummi insha Allah bazakiji komai ba "
Tace" to shikkenan, nina tafi da kina, "
Dadi yaji har ransa, yace" to Ummi afuto lafiya"
Saida yaga tafiyar ta sannan ya koma cikin dakin, a lokacin har bacci yafara fizgarta, Ahankali ya janyo ta jikinsa yace"tashi yarinya ai baki isaba saikin bani labarin mk tukunna "
Ahankali ta bude idonta tace" mk, nikuwa nice Zan baka labarin mk
, in fadama a Sanadin neman mk Babu irin azabar daban shaba
Nide Tun a asbiti danaji kana magana da Abba nah lokacin daka biya mana kudin aikin idona, tundaga lokacin narasa gane kaina, nide fatana kawai naganka koda saudaya ne arayuwata, gashi baabu idon ganin ka, nasa Najma ta ganomin kai tacemin ai itama bayanku tagani, baabu yanda na iya haka na hakura, damuka dawo daga qasar waje nasamu number ka awajan Doc.

Nakiraka a lokacin da aka sakoni agaba agida akan na auri Nuhu, narasa ya zanyi, dole tasa ta nemeka, da nufin in fadama cewa agida za'a bani wani amma inaso kazo kayi magana da Abba nah, akan yabar maganar Nuhu, tunda shi idan yaganka zai ganeka, kuma zaiji nauyin yimaka musu, amma ina kiranka kahauni da fada kace na yiwa iyayena biyaiya, daga qarshe ma kakashemin waya "
Dasauri ya kalleta yace" wai kece?
Chapter 34 · 0% Book details