← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 48

Sashe 48

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Tace "wallahi kai, Dan nide bana cin abinci kasani"
Yace "nima kinsan banaci"
"to naji dauke hannunka daga kai kar Ummi tazo"
Yace "nadauke hannu na ki qwace ki hana yarinya shan nono, narasa me zakiyi dashi, abin nan dai nawa ne, daga ni sai Ummi nah,"
Yaqarasa maganar yana kama hannun yarinyar yana mata wasa
Rayuwar gidan mk da Babynsa kenan, suna zaune lafiya saide abinda baza'a rasa ba, wannan kuma dama ansan Zomu zauna Zomu saba ne, harshe da hakori ma wataran ana sabawa
Yarinyar su d'aya Mai kama da mk, babu Inda tabar ubanta, suka sanya mata sunan Ummi Wato Halima, suna kiranta da Ummi itama
Nawal nayin karatun ta a Dubai lokaci zuwa lokaci suna zuwa gida idan sun samu hutu a makaranta
Wani lokacin shida kansa yake sakata ta shirya suje gidan marayu da asbiti domin kai musu ziyara, hakan da yakeyi ba qaramin dadi yakewa Ummi ba, saboda tana ganin Kamar bai Manta da halaiyar mahaifinsa ba
Sultan da Sahla suna zaune agidan su lafiya, Inda take dauke da ciki na wata uku, suna zaune a Abuja, dasafe su shirya su tafi wajan aikinsu, idan sun dawo gida
Suyi aikin komai tare, hakuri da daukar qaddara irin nata shine yaja hankalin Sultan yafada cikin sonta batare daya saniba
Yayinda Najma suke shan amarcinsu akano cikin gidan ta Mai shegen kyau, watan su biyu da aure "
Shima Salisu yana zaune da matarsa lafiya
Mutanan iko kuwa,
an saduda, anbada kai,Nasrin tanata yin shagwaba son ranta, suna zaune a Abuja, da Dan qaramin cikin ta na wata biyu
Lokaci zuwa lokaci suna ziyartar juna itada Nawal, rayuwa Mai juyawa kenan, wataran qunci wataran farin ciki
Abaya sunsha wahala da gwagwar mayar rayuwa,musanman Nawal amma Haquri yabata komai
*** ***** ***
Kallanta yayi "Baby nah yakamata afara kokarin nemawa Ummi qani fa"
"qani kuma?

Yarinyar da ko yayeta ba'aiba"
Yace "nikam gaskiya nagaji kawai sonake kiyita haihuwa"
Tace "saikace wata inji?

Wato na tsufa da wuri kaje ka Auro wata irin fatar dakake so
Murmushi yayi yajata jikinsa ya rungumeta yace
"Baby nah kenan,Allah yabarmin ke,
NI DAKE
mu kasance tare har Abadah"
Itama ta rungumeshi tace "Amin mijina"
TAMMAT BI HAMDULLAH
Anan nakawo qarshan wannan labarin nawa Mai taken NI DAKE,Allah yabamu ikon yin amfani da abubuwan dasuke ciki masu kyau, yabamu damar watsi da marar kyau
ABIN LURA:
Hakuri, shine idan kayishi Awannan lokacin zaka samu riba, mutum yamaka laifi tattarashi ka watsar karka sawa kanka hawan ruwa, inde wannan Rayuwar ce kana zaune agiidanka zakaga abinda zai biyo baya
Tausayi da taimakon mutanan da baka sansu bama, Awannan lokacin abinda yafi mana qaranci kenan, Inda ace mutane zasuyi koyi da abinda mk yakeyi na taimakon mutane, da anji dadi, bai santaba Babu dangin iya Babu na baba, amma yatai maka mata daga ita har dangin ta, gashi sunyi aurensu suna zaune lafiya.

GODIA :
Hafsat Hausa novel (H2)
Khaleesat Haiydar Hausa novel
Nidake fan's
Best Hausa novels
Prince and princess hausa novel
Wanda yace... novel fan's
Meenat novel
Alkawari
hausa novel
Novels and kitchen
Ina godia sosai yanda kuke bibiyata Tun daga farko har qarshe, dama sauran Wanda ban fadaba
JINJINA GA:
Hajiyar...

Maman Ahmad
Mom haneef
Samirah yahya niger
Fatimaxahara
Maman dr.insha Allah
Fatima me voice
Hajiya qarama
Khadijat Aminu
Ummu farouq
Maman khalifa
Saudat
Mom asas
Futuha luv
Shamsiyya dahiru
Ruqaiyasalisu
Anty ~zubaidah
fateema shu'aibu abdulla
Mrs isma'eeil ce
Mom hydar
Nana
Khadeejat
Salma hamman sa'eed
Baby
Ummu haneef
Maman basma
Saudat
Maman sadiq
Sumyb
Mrym
Mmn khalil and rukky
Ummu affan
Hashmart
Rabiat Mafida Suleiman
Bashirm Halima
Khadija bashir
Fatima abdulqadir tatu
Deefat
Fati sd
Bazaqu qirgu ba
Group dina na whtspp Zan rufeshi zuwa jibi insha Allah, saikuma nafara wani novel din Zan bude wani
Daga qarshe duk Wanda na yiwa laifi a Sanadin wannan littafin yayafemin
Mutara asabon novel dina Mai taken DANGI DAYA, kai dagajin sunan kasan kwamacala ce ta family, Wanda zaizo muku bayan Sallah insha Allah
Karku Manta da sunan...

DANGI DAYA
miss you All
Amina Muhammad El Yaqoub jigawa state
H J L
J L
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
aff495c097d74780bc5735f707732581
Chapter 48 · 0% Book details