← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 48

Sashe 6

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nura yace "fad'a mata de, idan ke kin hakura, mu amatsayin mu na makusantanki bamu hakura ba yaya Baby"
Yakalli Abba yace "Abba kawai asiyar da gidan,bazamu juri ganinta ita bata ganinmu ba"
Najma ma tace "gaskiya kam Abba, kawai asiyar din, mutum dubu nawane suke zaune agidan haya"
Malam ya girgiza kansa, yana mamakin yaran, yanda suke qaunar junansu haka, yace "dare yayi, yakamata mu tafi gida, sai musan wacce shawara zamu yanke"
Ke Najma ki zauna tare da ita, su nura saisu dawo sukawo muku abinci, mu zamu tafi,zamu bincika muji gidansu yaron, kafin gobe kuma mud'auki mataki
Tace "to Malam, Allah yakiyaye hanya, Umma ki gaida mama
Umma tace" to Najma, ta kalli 'yar tata dukda ita bata ganin ta tayi musu saida safe suka tafi gida
Suna hanya Sultan yakira Salisu, "yaya Salisu yaya kukayi da likitan?"
"wallahi yace idanun nata suna riga da sun sami matsala, za'a basu million daya da dubu dari da sittin, suyi mata aiki"
"tabd'i jam, akwai damuwa kenan, wannan ko waye yatada mana qafar baya, inama zanga yaron nan"
"to wallahi de itama kanta tace kawai ganinsa take a hanyar ta tazuwa school batasan gidansu ba, yasan de sunansa Anwar"
"Anwar?"
"eh haka tace"
"Anya kuwa ba Anwar din dana sani bane?"
"eto may be kasan shi d'in tunda duk mutanan ku ne
Murmushi sultan yayi "kabari kawai yaya Salisu, sainazo goben insha Allah, ka gaidamin umma tah, ka kwantar mata da hankalinta kafin nima nazo nad'ora
Dan nasan dole ta damu antaba mata autarta
Salisu yace" to qanina Allah yakawo ka lafiya "
Awannan dare Malam bai runtsa ba, yana zaune akan sallaya yana addu'ah akan Allah yakawo musu Mafita, Allah yadubesu ya kawo musu dauki, Umma kuwa tana nan zaune itama da carbi a hannunta, tanaja tana kuma tunanin Rayuwar 'yarta qwalli daya aduniya,wadda zata kasance makauniya, domin kuwa idan tace zasu sami wannan kudin haqiqa ta yaudari kanta, ayayinda Abba yakasa zaune yakasa tsaye yanata zagaya d'akinsa yana tunanin Inda zai sami wannan kudin ya tallafi Rayuwar 'yarsa mafi soyuwa agareshi
Haka yayi tunanin yagama baisamu mafitaba, daga qarshe shima alwala yad'auro yazo yafara sallah
Wacece Nawal?

Itace 'ya guda d'aya tilo awajan ummanta maisuna safiyya,Abbanta Alhaji Muhammad lawan yanada mata biyu, safiyya ce babba,'ya'yanta uku, Salisu ne babba, saina biyu Sultan, saikuma yar' autarta Nawal
Saikuma mariya suna kiran ta da mama mariya, Tanada 'ya mace babba sa'ar Sultan ce, suna kiranta da anty Maryam, tana aure a zamfara state, saikuma Najma, wadda take sa'ar Nawal ce, tabawa Nawal wata biyu, sai nura dakuma saif, sai mus'ab Dan qaramin yaro
Rayuwar gidan tana tafiya ne cikin kwanciyar hankali, hakan kuma yasamo asali ne daga wajan umma, batada fada, kwata kwata batasan tashin hankali, mace ce me mutuqar hakuri
Yayinda mama mariya takeda Jan magana, abu kadan za'ayi amma tadinga magana akansa kenan
Gaba dayansu 'yan kanone, suna zaune a rijiyar zaki, Abba ne yake tare da mahaifinsa unguwa d'aya, Wanda aka sani da Malam, shine limamin unguwar su, Babban malami ne sosai, masani ne akan abubuwa dayawa, sosai yake shiri da Nawal
Fari ne tass, shima Abba saiya dauko farin sa, cikin ikon Allah kuma gaba dayansu yaran Abba babu baqi, kowa kamarsa daban amma farare ne gaba dayansu, yayinda Nawal tayi Kamar ummanta, babu abinda tabari na umma, kawai baqin umma ne batayiba, saboda umma baqa ce, tana doguwar fuska, girarta acike take, baqa sid'ik, tana da hanci madaidaici, amma _lips_ dinta _pink_ ne, kuma sirara, kasan cewar umma maza tafara haifa saiya kasance tanason 'ya mace, sai kuwa Allah yaabata, sukuma Salisu da sultan tunda aka haifeta suka dauki son duniya suka dora mata, kowa soyake yasata farinci acikinsu, sune suka saka mata suna BABY, daga nan kuma kowa yadena cewa NAWAL yake kiranta da Baby har 'yan unguwa, qannanta kuma nura da saif da mus'ab suke kiranta da YAYA BABY
Suma kuma yan dakin mama mariya suna santa, musanman Najma, sun shaqu sosai, basuyi halin uwarsu ba, nura da saif kuwa dayake sunada tsawo saiya kasance sunfi su Nawal girma, idan ka gansu saika dauka sune gaba da Najma da Nawal din
Nawal tanada matuqar hakuri, Dan wani lokacin har mamaki take bawa ummanta
Sau tari za'a yimata abu, Wanda zakayi tunanin zata rama, amma tana budar baki saide tace tayafe maka, shiru shiru ce baabu ruwanta, saide inka kaita maqura bata iya fishi ba
Daga ita har Najma shekararsu goma sha tara, amma Allah yayi mata sura me kyau da daukar hankali, agidama umma bata barinta ta zauna da qananin kaya saboda Allah yayi mata baiwa, Ga kyau Ga diri, tana hips manya, idan tana tafiya saika dauka tanayi ne Dan Jan hankalin ka, amma kuma kokadan ba hakan bane, yayinda _boobs_ dinta suke madaidaita
Amma a gareta ba haka tasoba, saboda tana qaunar qananun kaya, tanason sakasu koda yaushe, shiyasa take dabara tasaka qananun kaya saita dora baqar abaya akai tatafi makaranta, haka kawai takeson shigar qananun kaya
Mahaifinsu Alhaji Muhammad ma'aikacin gwamnati ne, amma yadade da ritaya, kawai yanzu yana karbar kudin fansho ne, Wanda kudin qalilan ne, na gidan ma bai wadacesu ba
Salisu bashi da aure, yana Dan neman kudi ne a kasuwa kawai, saikuma sultan yana wajan uban gidansa a lagos, yana koyan harkar canji, bashi da mutunci, Tun baby tana qarama baya bari atabata yaqyale, yana harka da samari masu ji da kansu, kuma suma sun sanshi saboda bashida kirki
Dukansu sunyi karatu saide babu aikin yi
Anty maryam kuwa daga candy akayi mata aure
Najma da Nawal suna candy suma suka zana jamb kowa yaci acikinsu, gashi baba bashi da karfin dazai dauki nauyinsu su biyu, Dan haka yace kowa ya hakura acikinsu, mama mariya tahau masifa tana cewa yan Dakinta ne bayaso suyi karatu, inba haakaba yabawa Najma mana, tunda yan dakin safiyya sunyi karatu harsu biyu
Haka yayi shiru yarabu da ita, amma shi kansa acikin ransa yafison Nawal tatafi, haka ka wai Allah yadora masa son yarinyar acikin ransa
Saide daga bayama da abin yafara zama tashin hankali kawai sai Najma tace ita hakura taci girma tabarwa qanwarta, kawai Abba yatura Nawal din
Wannan ne silarta tazuwa makaranta, Wanda Acan tahadu da qawarta Nasrin, tanada hankali sosai da sanin yakamata, lokaci zuwa lokaci suna ziyartar juna,
_Back to story_
Washe gari haka kowa yatashi jiki babu qwari, Umma idanunta har nauyi suke mata saboda rashin bacci
Abba kuwa Tun sassafe yafita yanata zagaya gari wajan abokansa neman bashi
Dakuma tallar gonakinsa da filaye guda biyu ko za'a sami masu siya
Daya daga cikin dillalin de yace masa zaiyiwa wani Alhaji magana idan zai siya zaizo yakarbi takardun sai suje suga wajan
Sai wajan shad'aya da kwata yadawo Gida, duk yagaji Ga yunwa tana damunsa kansa har ciwo yafara, Ga kuma tunanin Nawal datake asbiti, shi Salisu da Malam sun tafi neman sanin Anwar dakuma iyayensa
Kansa yasunkuyar qasa yana tunani, yana kuma addu'ah Allah yabasu ikon cin jarabawa
"Salamu alaikum"
Abba yadago kansa yace "wlkslm sannunku"
"yawwa sannu baba, masu karbar kudin wuta ne, _bill_ zaka bamu"
"to bari adauki muku"
Yatashi yashiga Gida yadauko yakawo musu
Dubawa sukai daya daga cikin su yace "baba wannan ai baka biya na wancen watan bama, amma yanzu babu damuwa kakawo dubu shida da dari biyar kawai"
Cikin haushi Abba ya kallesu "shi kudin wutar ne dubu shida harda 'yan kai?"
"eh baba, ai ahakanma anyima sauqi sosai"
"to bari kuji, ni banida wata dubu shida dazan bayar, ga _transformer_ can kafin ku qaraso nan gidana, zaku iya zuwa tundaga jiki ku tsige layin gidana a jikinta(
Kunga nan gaba basai kun tsaya agidana ba, kawai tsallakeshi zakuyi,
(kunga laifin Abba?

Waye Anwar?

Yaya makomar su Abba dangane da kudin dasuke nema?

Anya kuwa sultan bashi da alaqa da Anwar?

Dan Allah sharhi
inaso naji hasashen da kukeyi masoya nah
Amnah El Yaqoub
[1/26, 11:28 AM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE...
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to *Itz sadeek* wannan shafin ma nakane kai kadai, zaka iya hana fan's na *Khaleesat haidar* karantawa
Saboda tsabar baqin ciki suna tafiya ahanya amma babu me cewa komai, kowa takaici ya isheshi, Malam kuwa kukan zuci kawai yakeyi, yau shine aka watsowa kudi, suda ake zuwa wajansu ace su taimaka da addu'ah idan lokacin zabe yazo, ko kuma adauki kudi a turasu zuwa saudia domin suyi addu'ah akan Allah yasa suci zabe, yauga irin mutanan nan waninsu ya watso masa kudi
Abba kuwa kokadan baiji haushin abinda Sultan yayi ba, saima kunyar mahaifinsa dayakeji akan rashin kunyar da akayi masa da girmansa da mutuncinsa, shikkenan de yanzu rayuwa tazama sai inkana da kudi ne kakeda daraja
Tsaki Salisu yaja "Malam wannan shine abinda nake fadamuku Tun farko, da munje _police_ _station_ Tun farko da haka bata faruba"
Abba yace "ai yanzu ma bamu makaraba Salisu, nikaina banji dadin abinda yayi manaba, aqalla yakamata ace ya sauraremu, ko kuma yakira shi yaron yaji ta bakinsa, amma babu komai, da Allah muka dogara ai"
Shikuwa Sultan baice "A" ba acikin maganganunsu, haushi kawai yakeji akan dakatarwar da Abba yayi masa
Basu tsaya ko'inaba sai _police_ _station_ mafi kusa dasu, suna zuwa Abba da kansa yayi musu bayani, bayan sungama yin _report_ din Abba yace yanaso atura case din nasu zuwa _court_ cikin sauri
Sultan ya kalli Abba, cikin ransa yace lalle ran Abba yabaci, tunda har yayi maganar _court_ .
Chapter 6 · 0% Book details