← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 48

Sashe 13

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariyar yaqe yayi, shi yana ganinsa da tsawo gad'an haskensa amma shine take masa haka
Yace "to ai inde sunyi kyanki to banida damuwa, sai abu na biyu shine tarbiya, kinada tarbiya, Ga kuma uwa uba hakuri, Allah ya hore miki hakuri
kasancewar yana mura sai Jan hanci yake
gashi babu tissue ahannunsa, kasan kana mura kuma zaka je wajan budurwa zance saikazo da tissue kodan handkerchief,
yaci gaba da cewa saikuma Breast, Allah ya hore miki su nidama kuma inason na auri mace Kamar hak...

Bai qarasaba majina tataho ta hancinsa
Tana gani tafara yamutsa fuska
, zuciyarta tafara tashi, Nuhu wanne irin qazami ne, amai taji yataho mata, cikin sauri ta daakatar dashi tace "Nuhu Zan shiga Gida, aiki nake ka katseni," daga nan tayi wuf ta shige cikin Gida
Tana shiga Gida mus'ab Dan autan Mama Mariya yashigo yaje wajan ta yace "yaya Baby"
Tayi zatan abin arziqi zai fada mata tace "na'am mus'ab"
Yace "naga hancin Nuhu da majina
Haushi yasa ta dafe kanta da hannunta
tace "Mus'ab wuce kaban waje"
Sum Sum yaron yafice daga falon
Tayaya ma zata auri Nuhu bayan qannanka ma sunsan halin qazantarsa
Da daddare taje wajan umma tace "umma kinada dari biyu kibani nasai kati Zan kira yan school dinmu
"kiduba gefen waccan kujerar kidauka"
Tace "to" sannan tadauka tafice daga gidan, kasancewar akwai shago akusa da gidansu nan danan tasiyo tadawo, yau umma a dakin Abba take, shiyasa ta bari saida tazo bacci sannan ta kirashi, amma abu daya ake fada mata shine layin bayakan waya
Tashin hankali ne ya bayyana afuskarta qarara, duk wannan murnar datake zata kirashi hakan yatashi abanza kenan?

Number Nasrin takira, bugu uku tadauka tace "Beauty ya kike yagida?"
"lafiya lau Nas zaki shiga school ne gobe?"
"eh Zan shiga insha Allah, meyafaru?"
"inaso ne zamuyi magana Mai muhinmanci, saimun hadu goben kawai"
"toba damuwa Beauty saimun hadu"
Kashewa tayi taci gaba da kiran number, saide takira yakai sau talatin, amma amsar de guda dayace, haka ta hakura tayi addu'ah ta kwanta bacci cikeda damuwa
Washe gari karfe tara ta shirya tsaf cikin hijabi dogo har qasa, fuskarta fayau babu kwalliya, sai powder kawai Data shafa, ta lakuci Vaseline tashafa a lebenta, sai pink lips dinta yayi mutuqar kyau sai sheqi yake
Wajan umma taje tace "umma natafi school"
Kallanta tayi, Kamar de tahanata amma sai tayi shiru ganin ta qwallafa ranta akan karatun "to saikin dawo"
Tana fita ta tsaya a kofar Gida har saida Allah yakawo Mai adedeta sannan tahau, sunzo dede Inda tahadu dasu Anwar tacewa Mai adedetan "bawan Allah yisauri Dan Allah," saboda jitake Gabanta yana faduwa sosai, Kamar zasu sake tareta
(in banda abinki suda basusan ki bama kullum fuska cikin niqab tayaya zasu ganeki
Cikin qaramin lokaci ta isa makaranta, Nasrin na jiran ta agaban hall din tana zuwa tace" Beauty yazuwa haka babu niqab?

"Hmm wallahi Malam ya hanani sakawa, Tun lokacin da abinnan yafaru"
"gaskiya ne Allah de yaqara kiyaayewa,"
Basufi minti ashirin da shiga hall dinba malami yashigo, aikuwa kowa sai Kallanta yake saboda basusan fuskar ba
Ita kuwa da tasan kowa ko a jikinta, har malamin yagama karatu yafara tambayoyi amma cikin maza ne kawai suke amsawa, mata sunyi shiru
Malami ya kalli wajan mata yayi musu wata tambayar nanma shiru
, aifa karkaso kaga ido wajan maza,Nasrin tayi qasa da murya tace "nikam babu abinda nafahimta wallahi, bazan daga hannu nabada amsa ba daidai ba, ke Beauty inkin sani kifada masa
" nasani Nas, amma wallahi tsoro nakeji, gabana faduwa yake, banaso ayita kallo nah
"lalle Beauty aikuwa yin shirunki shine zaisa adauka mata jakai ne wallahi"
Malami yaji shiru yasake cewa babu amsa?

Cikin faduwar gaba tadaga hannu, aikuwa sai ido yadawo kanta
Malamin yace "inajin ki"
Maimakon ta bashi amsa saita tata shi taje wajan sa ta karbi makar hannunsa tariqe shide yanata ganin ikon Allah, bayani tafara yi da baki, amma kokadan taqi kallan bangaren maza
Hall yayi tsit, kowa ita yakeji, sosai tayi bayani sannan tafara rubuta example, tana sake yin bayani, dukda muryar ta tana danyin rawa haka de tadaure tayi
Tabawa malamin makarsa, aikuwa me za'ayi inba ihu da tafi ba, sosai ta birge kowa, saboda ba kasafai ake samun mata masu irin wannan jajircewar ba
Tana zama wata dake bancin bayaansu tatabota tace "Nawal ga wani abokina yaturomin text yanzu wai yana sonki
Kai ana budiri a jami'ah
Ga malami a aji amma wasu saqon soyaiya suke turawa
Murmushi kawai tayi mata batare datace komai ba, suna fita daga lacture Nasrin tace" Beauty yau kinyi kokari, kin bawa kowa mamaki, inajin ki wacce magana kikeso muyi?

"
Cikin nutsuwa tace" Nas nakasa cireshi araina "
Zaro ido Nasrin tayi cikin murna tace" wow, yau Beauty anfada soyaiya, fadamin waye shi?

"
"MK"
Mamaki yakama Nasrin, "wai kina nufin mutumin daya biya kudin aikin ki?"
Daga mata kai tayi, idonta na kawo ruwa
"to dama kin hadu dashi ne Acan qasar da aka miki aikin idon?"
" ban hadu dashi ba, Tun lokacin danaji yana magana da baba nake tunanin sa, naji kawai yana birgeni duk da banganshi ba, nafada wa Najma tacemin wai qilama yanada aure, yafi karfina, narabu dashi, wai ko a 'yar aiki bazai daukeniba
, nasamu number sa awajan baba danaji yace zai kirashi yayi masa godia, shine nasaka number a wayata nadinga kira jiya taqi shiga, karshema layin bayakan waya haka aka nunamin, Nas ina sonsa wallahi, koda ace yanada mata wallahi Zan iya zama dashi, koda shi bayasona ni ina sonsa, ki temaka kiban shawara, Yaya zanyi?

"
Ajiyar zuciya tasauke, ta saka hannu ta goge mata hawayen idonta" kiyi hakuri Beauty insha Allah, Allah zai kawo mana mafita, kinsan garin dayake ne?

"A a Nas bansaniba"
"Ok kinde san likitan dakuka je Albania tare dashi ko?"
"eh nasan shi Nas"
"yaya sunansa?"
Nawal tace "doctor babangida"
"shikkenan kiyi hakuri, yanzu tunda bamuda wata lacture tashi Muje"
Kallanta tayi "ina zamuje Nas?"
Kai tsaye tace mata "Asbitin Malam Aminu"
*** ***** ***
Kasancewar Abba yana gidan Malam shiyasa kwata kwata bai nemi Nawal ba, kuma yasan cewa safiyya bazata barta taje ko'inaba harsai yayanke hukunci akanta.

Malam ya kalleshi yace "muhammadu ya ake ciki dangane da karatun su Nura?

Yaya kukai da mutumin?"
Abba yace "Malam nakira wani abokina dayake koyarwa a A.B.U zaria, nayi masa magana akan yarana maza guda biyu dasukai candy bana, inaso ya temaka ya nema musu admission, yakumace insha Allah zaiyi kokari yaga sun samu gurbin karatun, sannan yafadamin kudin registration dinsu,saboda haka naqara dubu talatin akan nakowaccee shekara incase ko zasu iya qarawa, na turawa Sultan kudin registration din Nura da Saif gaba daya na shekara hudu, nikuma zanci gaba da daukan nauyin kudin Mota dana abinci da sauran abubuwan buqata, amma maganar kudin registration de idan lokaci yayi sai suje wajan Sultan, saikuma Najma idan anfara yin jamb saita sake rubutawa itama idan Allah yasa taci jamb din saita shiga B.U.K
Ita kuma zan turawa Salisu nata kudin registration din, itama idan lokaci yayi sai taje wajan sa ta karba
Malam ya jinjina kai yace "muhammadu kayi tunani Mai kyau, amma ita kuma Nawal dinfa?

Banji kayi maganar nata karatun ba"
"Malam ina sane da ita, akwai abinda nake tunani akanta tukunna"
Malam yace "to alhmdlh,wasu mutanan suna dauka haihuwar 'ya mace wahala ce, amma basusan ta Sanadin ta zaka iya samun alkhaairi ba, kagade abinda yafaru Ga Nawal, gashi Sanadin ta yanuwanta ma zasu tafi makaranta, yanzu de abinda Zan fadama shine, kaje kasa afara gyarama gidanka, sannan filinka daka siyar kanemi wani kasiya kamaida abinka, sauran kudin kuma saikaci gaba da amfanin yauda gobe dashi"
"to Malam insha Allah, daga nanma Zan wuce wajan masu saida kayan gyaran asiya akai gidan inyaso sai afara gyaran dawuri, sannan kaima Zan turo maka wani kudin, Zan qara dubu Hamsin akai asayi abin sadaka ayiwa wannan bawan Allah, Dan yaron nan daga ganinsa yana buqatar addu'ah "
Murmushi Malam yayi,cikin ransa yace" kome yagani a tattare da yaron yake cewa yana buqatar addu'ah?

Afili sai yace "to muhammadu, Allah ya shige mana gaba, nagode"
Daganan sukai sallama Abba yatafi
*** ***** ***
Cikin Murmushi yace "A a Nawal yanmata yau kece a office din namu"
"eh wallahi doctor nice ya ayyuka"
"aiki da godia, ya wajan Abbanki?

" yana nan kalau, "daga nan tayi shiru
Nasrin sai zungurinta take amma takasa magana sai shine yace" meke tafe daku ne, ko zuwa kukai mugaisa "
Tace" am likita dama...

Dama..

Munaso kafada mana garin...

Ganin taana neman yimusu 'baran' 'barama ta zubda ajin mata
yasa Nasrin tace "doctor jiya wai Abbanta yazo yakarbi number wannan mutumin awajan ka, to shine suka dinga kira taqi shiga, shine tacewa abban nata zatazo da kanta wajan ka idan kanada wata number kabamu". (kai kai zuri
Murmushi yayi yakalli Nawal "kinaso ku gaisa ne kema?"
Murmushi tayi batace masa komai ba, yasake cewa "ai hakan yanada kyau kinsan manyan mutane may be baya qasar ne shiyasa baku sameshi ba (fada matade
Yaci gaba da fadin" Amma gaskiya banida number sa, wannan dinma awajan shugaban asbitin nan nasamu, "
Nas tace" ikon Allah, toshknn doctor mungode, amma shikam awanne garin yakene?

"
Yace" wallahi bansaniba, amma akwai abokin aikina dasuka fita germany gyaran kafar wani yaro Wanda shi wannan yaron qanin abokin shi mk dinne saide na tuntubeshi naji ko yasan Dan inane"
Cikin murna tace "to Doc.

Mungode"
Wayarsa ya janyo yakira dayan likitan yasaka ta a handsfree yanda zasuji komai, ana dagawa yace "abokina ya ayyuka?"
"aiki alhmdlh wallahi gashi muna ta fama"
"masha Allah, dama akwai wasu bayin Allah ne sun kira number mk basu sameshiba shine suke tambaya wai shi din Dan wanne gari ne?
Chapter 13 · 0% Book details