← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 48

Sashe 1

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
NI DAKE...
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Daga marubuciyar :
DANA SANI
(Ahmad & Feenah)
BURINAH
(Amal & Daddy)
WAZAN ZABA
(Iman & Aliyu)
SHALELAN BABA
(Haneef & Haneefa
Shalele & Shazali)
And now
NI DAKE...

Is loading...

Wannan karan alqalamin namu yadawo kano
Ya Allah kabani ikon kammala wannan littafi lafiya, Kamar yanda na kammala sauran novel dina lafiya, ya Allah ka bamu ikon yin amfani da abinda yake cikinsa Mai kyau, Allah kahaneni rubuta abinda yake ba daidai ba
Labarin *NI DAKE* qirqirarran labari ne dana zauna na tsara abina dakaina, banyi da nufin tazarci akan kowa ba
Ban yarda ajuyamin littafi na ta wata sigar ba, nafada nasake fada duk wacce tasake kwaikwayon basirata tajuyamin littafi to Allah zai mana sakayya tsakanina da ita, dake nake wadda kike kwance kina karanta min littafi sannan ki juyamin shi da wani sunan daban, Allah ya gani idan nafara posting din littafi banda lokacin kaina kullum sai nayi posting saboda inaso nagama shi akan lokaci, banda lokacin dazan tsaya yin karatun novel balle ma ace basirar wata na sata,kin juyamin littafi na na SHALELAN BABA, to yakamata ki dakata daga kansa
,kema ki nemi taki basirar, nasan cewa saqona zai isa gareki tunda kina bibiyata
*Dedicated* *to* _FATIMA Y ADAM_
masoyiyar dukkan books dina, shafin farko nasadaukar dashi agareki kiyi yanda kikeso dashi, saqonki ya iso gareni yanda bakyason littafina yaqare idan kina karantawa, ko abinci bakya iya ci, nagode da soyaiyar ki agareni, Allah yasa nima saqona ya isa gareki
Bissmillahir-rahmanirraheem
Tafiya take cikin nutsuwa Kamar de yanda tasaba, baqar abayace a jikinta,duk da rigar tanada Dan fadi hakan bai hana surar jikinta baiyanaba, yayinda fuskarta take sanye da niqab shima baqi, idan kaganta dole zakayi tunanin wata balarabiya ce yar qasar saudia, kasancewar suma haka suke tasu shigar
Agogon dake daure ahannunta ta kalla Dan nera dari hudu, hannun nata na kalla fari tas dashi tareda dogayan yatsun hannunta zara zara
Tana gama ganin _time_ cikin faduwar gaba ta furta "subhanallah" sannan taqara sauri ganin takusa makara
Zaune suke akan Mota Kamar kullum, susu uku ne, kullum tazo wucewa sai sunyi mata magana ta share su, idan zasu kirata sau dari haka take sharesu sau dari, yi take Kamar ma da qasa suke magana ba itaba
Daya daga cikinsu ne yace
" _Dude_ ga yarinyar nanfa yar renin hankali tana isowa"
Wanda aka kira da _Dude_ yace "kuna bani mamaki sau dayawa wallahi, saide magana, bazaku iya zuwa gareta gaba da gaba kuyi mata abinda kukaga dama ba"
Na ukun ne yace "a a fa Anwar, ni gaskiya kwarjini yarinyar takemin, bayan hakama bamusan ita din ko 'yar wacece ba"
"yar wacece kuwa Data wuce yar gidan Malam Shehu, takalmin kafarta kadai zaka kallah shine zai tabbatar maka dacewa talauci yasamu matsugunni agidan iyayenta"
gaba dayansu suka kwashe da daria, tareda tafawa, daya daga cikinsu yace " _oh boyyyyy_ " irin na tantiran yan iskan nan
Adede lokacin tazo saitinsu zata wuce
Anwar yaduro daga kan motar dayake kai yace _let_ _me_ kuga yanda Zan mata yau, yau saina yaye wannan abin _face_ din nata, munafukai ne irin wannan yaran, su suna qare maka kallo, amma kai bakada damar ganinsu
Zuciyarta daya tana tafiya, sai ganin mutum tayi agabanta Kamar wadda aka jefoshi, kadan yarage qirjinsu yahadu
Masifar tsoro ne da ita, lokaci daya gabanta ya tsananta faduwa, idanunta yayi wuri-wuri, cikin zazzaqar muryarta tace "A'uzubillahi...

Idanunta yakallah farare kar , qwayar cikin idon datake baqa saita qara qawata cikin idanun nata
Shida kansa saida yahango tsakanin tsoro a 'idonta
" keni shaidan ne dazaki nemi tsari dani"
"to waye zaiyi abinda kayi yanzu inba shaidan ba"?

Nunaata yayi da hannu yace "Karki kuskura kisake dangantani da shaidan, inba hakaba wallahi sai nayi miki abinda bazaki taba mantawa dani ba har abada"
Gabanta ne yaci gaba da faduwa jin wannan furucin nasa, Ahankali tace "Allah yahdika...

Kafin takarasa ya fizgi hannunta yace" Wato ke ina magana kina maidamin ko"?

Cikin sauri ta fizge hannun ta, ta matsa gefensa zata wuce, yasake shan gabanta yakai hannunsa zai yaye mata niqab dinta
Abinka da mutum Mai hakuri, kuma aka qureshi aka kaishi bango, itama hakance ta kasance awajanta, batayi wata wataba tadaga hannu ta sharara masa kyakykyawan mari
Cikin tsananin mamakinta yadora hannu akumatunsa, lokaci daya Idanunsa yakada yayi jajir, yau mace ce ta mareshi, macenma wannan qanqanuwar, wadda daga gani ba 'yar kowan kowa bace face 'yar baqaqen talakawa
Cikin fishi tace "angaya maka ni 'yar isakace, ko angayamaka ni irin shashakan yanmatan dakuke hulda dasu ne?

To Zan iyayin komai domin kare mutuncin kaina kagane?

Tana fadar haka ta matsa gefensa ta wuce cikin sauri tana qarasawa bakin tete domin tare _keke napep_ zuwa makaranta
Gaba daya jikinta 'bari yake, hatta hannunta datayi marin dashi karkarwa yake, Innalillah..

Meyakaita marin namiji, namijin ma marar mutunci irin wannan datake masa kallan d'an tasha
Gaba daya a tsorace take, domin kuwa idan Mota tayi qwaqwqwarar _Hon_ zata iya zurawa aguje
Tana wannan tunanin me adedeta ya tsaya agabanta
"Hajiya ina zaki je"?

Cikin in-ina tace B..

B..

BUK zaka kaine _new site_
Yace"hau Muje"
Cikin sauri tashige tazauna tana sakin ajiyar zuciya, shi kansa me adedetan saida yajuyo ya kalleta cike da mamaki
** *** **
Daria suke masa gaba dayansu, daya daga cikinsu yasaka hannu abakinsa yasaki fito
Yace "aisai kadawo, dama mena fadama?

Kullum kaine kake cika mana baki akan yarinyar nan, yanzu gashi ka karbi rabonka, yarinya qarama ta wanka ma mari, kuma katsaya agabanta kakasa tabuka komai sai riqe kumatu
Tsaki nabeel yaja yace" Dan Allah jazy kadena wannan maganar kaifa dama can nalura tsoron yarinyar kake, yadubi Anwar yace gaye kawai kabasar kazo mu wuce, Allah yasomu babu yara, da tuni ta watsar mana da _class_ "
Cikin jin zafi yace" nabasar fa kace nabeel, ni wannan yarinyar zata mara?

Tana nufin taci banza kenan?

Inaaa _Impossible_
Motarsa yashiga yajata atsiyace yabar wajan, yabude _friends_ din nasa da qura
Jazy ya kalli nabeel yace "gaskiya ran gayen nan yabaci dayawa"
Nabeel yace "ai dole, kaikuwa mari fa"
"gaskiya ina tausayin yarinyar nan, _because of_ bazaidau qaramin mataki akanta ba,"
Kafada nabeel yad'aga tare fadin
" _Whatever_ "
*** *** ***
Dede gate din yasauketa ta bashi kudinsa tashige cikin sauri
kai tsaye _department_ dinsu ta nufa, saide tana zuwa taga _already_ _lacturer_ din Yarufe kofar, dama haka dabi'arsa take, muddin yarigaka shiga da minti biyar to zai rufe kofar ne saide kayi hakuri
Agogon hannunta ta kallah ta dafe kanta
11:16 shadaya yakamata ace tazo, yanzu gashi taqara har minti goma sha shida
Wasu yanmata ne atsaye abakin kofar hall din sunkai su biyar, daya daga cikinsu tace "wallahi malamin nan baisan darajar mata ba, inba hakaba yabarmu atsaye, anbashi hakuri Yaqi kulamu"
Watama tace"ke bashida aure fa, shiyasa yake rashin mutunci "
(kunsan yanmata _most_ _of_ _them_ dinsu dazaran malami yahanasu shiga hall yanzu zakuji sun fara cewa baisan darajar mace ba
musanman malamai marasa aure)
Wata kuma taci uban gayu tadaga murya yanda zai iya juyosu tace" Malam innallaha ma'assabirin "
Duk yana jinsu ya sharesu
Itama ganin sun cikata da surutu bama tajin abinda yake fada yasa tajuya takoma daya bangaren ta tsaya ajikin _window_ tana saurarensa
Shikuwa yana ganin ta yayi mata alama da hannu akan tashigo hall din, saboda daga ganinta zakasan tafisu nutsuwa da sanin darajar karatu
Aikuwa nan kallo ya koma sama, dalibai aka fara qus-qus
duk yana ganinsu kawai ya girgiza kai, shide yasan bata wata manufa yayi hakan ba, saboda yarinyar fuskarta ma arufe take bare ace kyanta yagani ko kuma wata sura ta jikinta yasa yabarta tashigo
Haka yaci gaba da bayani har lokaci yacika sannan yafita
Qawarta ce taqaraso wajanta tace " _Beauty_ meyasa bakizo da wuri ba kinsan halin malamin nan, koda yake danma naga ke yau Allah yadoraki akansa"
Ajiyar zuciya tasaki "besty wallahi matsala aka samu ahanya, _that's_ _why_ nazo _late_ ,"
"ok to kinga tashi Muje musai wani abun muci sai nayi miki bayanin Inda yayi mana bakya nan"
Tace "to besty na Muje"
Lemo suka siyo Limca Dan nera dari
suka samu waje suka zauna sunasha dayar tanayi mata bayani
Wayarta ce tayi qara qirar VIVO
Fara yar qarama, tana ganin me kiran taja tsaki tareda _rejecting_ _call_ din
"Beauty kina bani mamaki, meyasa bazaki bashi dama bane shima adama dashi?

Cikin _serious_ _voice_ tace Nasrin, Dan Allah kidenamin maganar wannan mutumin, wallahi bana sansa, ko ganinsa bansan yi"
Murmushi tayi tace" toshikkenan qawata, wai kenan yar jami'ah ko?

Taqarasa maganar cikin zolaya
Tace" uhm ina abin yake besty, _level_ 1 din?

"
Dukkaninsu suka saki Murmushi har time din shigar wani malamin yayi suka koma _hall_
*** *** ***
_Angaya maka ni 'yar isakace, ko angayamaka ni irin shashakan yanmatan dakuke hulda dasu ne?

To Zan iyayin komai domin kare mutuncin kaina kagane_ ?

Wani irin wawan tsaki yasaki tareda fatali da kwalbar lemon dake gabansa, _glass cup_ din dake kusa da lemon yafadi aqasan _tiles_ din falon ya tarwatse
Maganganunta ne suke masa yawo a qwaqwalwarsa, cikin masifa yace "Baki isaba!!!!

Qaran cup din daya fashe ne yadauki hankalinta zuwa falon, cikin takunsu na manyan mata Wanda suka jiqu da naira ta qaraso wajansa tace" _my_ _son_ , kaida waye "?

Huci yake shi kadai batare daya bata amsaba
Ajiyar zuciya tasauke tareda zama akan kujera itama sannan tace" nasan cewa kaida wata yarinyar ne, Anwar wai sai yaushe ne zaka nutsu kayi hankali Dan Allah?

Karka Manta fa mace ce ta haifeka, a kullum bakada Burin daya wuce kaci zarafin mata, sannan matan ma Wanda basujiba basu ganiba, 'ya' yan talakawa, karka Manta matsayin mahaifinka agarin nan, abu daya zakayi yataba masa siyasar sa, koba haka bama duk abinda kayiwa 'yar wani shi za' ayiwa taka, koma fin haka,sannan.....

"Sadaqallahul Azeem"
Dasauri tajuya takai kallanta gareshi, ta sunkuyar da kanta batare Data cigaba da fadan datake yiwa yaron ba
Yace "Hajiya kina kokari wajan yiwa Anwar nasiha, bakya gajia abin har mamaki yake bani," yadubi Anwar yaci gaba da fadin " _my_ _son_ , kayi abinda ranka yakeso kaji ko?
Chapter 1 · 0% Book details