← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 48

Sashe 18

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"
" kakoma ka canja nace, kokuma kafasa fita Inda zaka je "
Kamar zaiyi kuka ya tsaya, shi baiyi gaba ba, shi baiyi bayaba
Matar dake kusa da ita itama ta kalleshi sosai, cikin fuskar harara tace " Use muhammadu"(Sannu Muhammadu)
Kallanta yayi,da niyya yayi ya qyaleta, yatsani matar nan tazo gidansu
Ahankali yadawo yazo Gabanta ya tsugunna fuskar nan atamke yace" Walijam yafendo "(ina kwana yafendo)
Saida ta harareshi sannan tace" Sejam kalau"
Be qara yimata magana ba yamiqe yayi hanyar fita
Sake tsinkayar muryar ta yayi tanajin cewa "ban'isa dakai ba kenan"
Kallanta yayi "Ummi Babu Inda zanje, part dina zanje nahuta i am tired"
"dawo ga ayyukan office nan agabana sunmin yawa, kazo ka dauki wani kayi"
Dawowa yayi ya zauna badan yasoba yadauki takardun dake Gabanta yana dubawa, bayasan aiki cikin weekend ko kadan, yafison ranakun aiki kawai ayi aiki, ranakun hutu kuwa ahuta
Saida tagama typing din sannan tarufe computer ta dubeshi "akwai takarda da aka turomin daga Bayero university kano, akwai taro daza'a gudanar na murnar bude sabon department dinsu, so ina ganin kawai kaje, kaga nima saina huta,"
Kallanta yayi yace "Ummi kano?"
"eh kano"
"Ummi kiyi hakuri, amma bazan sake zuwa kano ba,
gaisuwar dakika turani kwanaki ma masifa tazamemin"
"subhanallah wacce irin masifa kuma acikin gaisuwar?"
"kede Ummi ki shirya kije, amma nide inkinganni alahira kai ni akai"
Tsaki tasaki kawai tarabu dashi
Shima da yaji tayi shiru kawai saiya tattara takardun gabansa yafice daga falon
Yana fita yafendo ta dubi matar da aka kira Ummi tace "wai yanzu Addah haka zaki zubawa BAFFA ido kina kallansa?yaro yagirma harya gaji da girma baabu aure
"to yafendo yaya zanyi?

Baffa yafara fin qarfina,"
"ga shawara Adda, mezai haana kimasa aure"
"to yafendo dawa?saide ko nahada shi da Bintu tawajanki"
"Adda Bintu da masifa muhammadu da miskilanci da rashin son raini wataran gidansu kamawa zaiyi da wuta"
Ummi tace "to Allah yashige mana gaba"
*** ***** ***
Wasu mutane ne suka aiko ana sallama da Abba a kofar gida
Abba na fita yaga wasu magidanta sunkai su hudu, ya basu hannu suka gaisa
Babban cikin su yace"Alhaji mune wakilan Nuhu, yazo ya samemu yayi mana magana akan cewa zakayi wa yar wajan ka aure, kuma kai ara'ayinka shi kakesan bawa, shine yace muzo
mu nema masa auren, shi yana so ma abin karya wuce wata biyu "
Abba cikin ransa yace" to banda abin Nuhu basai agidan yarinya ance katuro ba"
Amma afili yadubesu yace "eh to akwai de yiyuwar wannan maganar din, amma de dadan sauran lokaci bha yanzu ba, afada masa insha Allahu idan abin yataso za'a nemeshi, ina jiran ita yarinyar ne akwai abinda nake sauraro daga gareta, idan naji shiru sai azo ayi maganar daga baya"
Cikin Fara'ah suka sake bashi hannu suma suka gaisa, sannan sukamasa sallama suka tafi
Abba yajima a kofar gidan kafin yashiga gida, Eh lalle yau ya tabbatar cewa Nuhu soko ne
Inbanda soko gidan iyayen yarinya aisune suke faraba cewa aturo
*** ***** ***
Bayan kwana biyu Nasrin ta kirata awaya, cikin sauri ta dauka"Nas nah, kwana biyu, Kamar kinsan ina nemanki,"
"beauty kenan idan kina nemana meyahana ki zo gidanmu, kullum saide nazo, wannan zumuncin inaga denawa zamuyi"
"haba Nas kiyi hakuri, ina cikin damuwa ne, akwai maganganu dayawa, ciki harda hanani zuwan makaranta da akai"
"menene yake faruwa?"
"Nas Abba aure zaimin, Nuhu zai bani, yanzu haka bana fita ko'ina , school din yace ya cireni"
"Innalillahi qawata Nuhu kuma?

Kinga kishirya kizo muhadu a makaranta yau, saimu tattauna anutse, gashi yau ana taro a mkrntar baki gaba, harda sarki ma yazo, ga baqi sosai harda turawa wallahi"
"Allah Nas?"
"wallahi beauty, kema kisamu kifuto harkya dansha iska,"
"to Nas karfa asamu matsala a hanani zuwa"
"kinjiki da wata magana, cemusu zakiyi zakije school ne?

Kicewa umma zakizo gidanmu shikkenan kawai"
"to shikkenan Nas bari nashrya"
"Amma fa Beauty kiyi kwalliya, Dan wallahi bakiga dalibai ba kowa yayi kyau"
"to Nas saimun hadu"
Tana kashe wayar dama tayi wanka, kawai Mai tashafa, ta bude jikinta da turare, wani less dinta ta dauko orange, da akai mata dinkin doguwar riga,gaban rigar anyi mata breast cup,
Dinkin yahau jikinta, yayinda ta nannad'e dogon gashinta tamaidashi Kamar ribom , tayi daurin dankwali Mai hawa hawa, tafitar da ribom din gashin nata
waje, sosai ta tsara kwalliya tayi masifar yin kyau tayafa mayafi da yaar qaramar jakarta, Kamar gaske taje wajan umma tace "umma kwana biyu Nasrin bata zoba, zanje naduba ta ko lafiya "
Umma tazuba mata ido tanaso tagano gaskiyarta, bataga alamun komaiba, Dan haka tace" to saikin dawo "
Tana fita bata jira adedeta a kofar gida ba, saboda tana tsoron baba yazo, cikin sauri tatafi bakin titi tatare wani tahau
Tana zuwaa school din takira Nas awaya, bayan sun hadu Nas tace" wow, wai beauty kinga yanda kikai kyau kuwa?"
Wallahi yau kike a beauty dinki, saide kuma kin rame"
"badole narame ba Nas, Nuhu yasakoni agaba"
"bani labari meke faruwa"
Nan take Nawal tabata labarin komai
"kiyi hakuri Beauty , Allah zai kawo mana mafuta, ki kwantar da hankalin ki, zomuje wajan taron"
Tafiya sukai wajan da ake taron, sai daga nesa suke hango sarki, tareda manyan baqi, pictures Nasrin tafara yimusu awayarta, sosai sukai kyau
Suna daga gefe a tsaye suna kallo Nas tace" Beauty bari naje nasiyo mana kek nadawo, kijirani
Tace "to Nas saikin dawo"
Kallan yanda aka qawata wajan kawai takeyi, Ahankali tafara zagaya wa kafin Nas tadawo,mutane ne suka fara tashi alamun harma angama taron
Dan haka ta dauki wayarta zata kira wayar Najma, hankalin ta nakan wayar kawai sai jitayi tayi karo da mutum, har wayar hannun ta tafadi qasa, dagowar dazatai kawai sai taga Anwar
Gabanta yafadi, tsoro yakamata, amma saitaqi nunawa, Ahankali tace masa "sorry
Shi kuwa yana ganin ta yaganeta, dama ga haushin dukan da yayanta yayi masa
Cikin fishi ya nunata da hannu yace "ke makauniyar inace ke?

Kina tafiya bakya kallan gabanki??

Duk da tana cikin tsoro Ahankali tasake cewa" kayi hakuri "
Kafin yayi gaba saida yasa qafa yatake mata wayar, sannan yatafi
Cikin ranta tace" kanka akeji, ta sunkuya tasa hannu ta dauki wayarta "
Duk abinda suke akan idonta komai yafaru, yarinyar tanada hakuri, shi da niyya ya bigeta saboda yana kallan gabansa ita kuma hankalin ta yana kan waya, amma duk da haka itace ta bashi Haquri,sannan bata nuna bacin ranta akan take mata waya dayayi ba
Duban direbanta tayi," munzaali kana ganin abinda nake gani kuwa?"
"nagani hajiya, wallahi naga komai"
"Yaya kaga yarinyar?"
"ai tayi sosai hajiya, billahil lazi Kamar wankan inji"
Murmushi tayi tace" sai nake gani tunda sun samu sabanin halaiya itada Baffah Kamar zasu zauna lafiya "
Cikin girmamawa munzaali yace" aaa sosai hajiya,wannan zata dauki komai "
Cikin takun nutsuwa matar tataka ta qarasa gareta tace "Qawata wayar taki tafashe ne?"
Dasauri ta juyo sukai ido hudu da wata mata, daka ganta kaga bafulatana
Murmushi tayi, abinda yafara futowa daga bakinta shine "ina wuni?"
Wani irin dadi taji yakamata, tace"lafiya kalau, gidanku anan kusa yakene kikaimu muyi sallah?

"
Kafin tayi magana Nas ta dawo, tace" Beauty ina kika shiga sai nemanki nake?

"
Tace ina nan Nas, ai kinga har antashima kawai Zan tafi gida"
Ita de Nas taga mace akusa da ita, bata tambyeta ba, tadubi matar ta gaishe ta, sannan tacewa Nawal" to sai munyi waya, ga kek din naki, ki gaida umma "
Tace" to Nas "
Tana tsaye tana kallansu cikin birgewa, daga gani qawaye ne makusanta
Ta kalli matar tace mata "to Muje"
Tafiya suka fara yi, matar ta dubeta tace" kinga ga Mota can Muje saiki masa kwatancen gidan "
Tace" to, amma cikin ranta mamaki take, wacce irin macece wannan, dole sai a gidansu zatayi sallar?

Yanzu idan takoma gida Abba yace ina suka hadu matar tace makaranta yaya zasu qare dashi?

Shknnn ita kuma tasan kawai yau asirinta yagama tonuwa
Direban ne yazo da sauri yabude musu motar gidan baya, matar ta dubeta tace "shiga "
Ahankali ta shiga, tana shiga qamshi yaratsa hancinta, ga sanyin esi daya cika motar
Itama ta shiga dreba yaja suka fara tafiya
Suna kan hanya matar ta kalleta tace "sainaga Kamar wayar taki zata iya samin matsala,"
Murmushi tayi kanta na qasa tace "a a hajiya, Babu komai wallahi"
Cikin sigar wasa tace "lala ba sunana hajiya ba, sunana Halima, amma d'ana Baffah yana kirana da Ummi, kema zanso ki fadamin hakan, Yaya sunan kine?

Ahankali tace" Ummi sunana Nawal "
Murmushi Ummi tayi tace" Nawal daurin dankwalin naki yamin kyau, duk lokacin dazan fita unguwa idan Zan daura dankwali d'ana Baffah qwacewa yakeyi yace shizai daura min, yanaso yadinga min kwalliya "
Cikin ranta tace yau nagamu da uwa Mai jarabar son danta
Zance daya biyu sai ta saka shi ciki?

Amma kawai sai tayi Murmushi tace" Allah sarki "
Ummi tasake cewa" muga wayar taki?
Chapter 18 · 0% Book details