← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 48

Sashe 5

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abba yace "saif kaje gidan Malam kafada masa abinda yake faruwa, mu zamu wuce asbiti, saiku samemu Acan" ya kalli mama mariya yace "mariya ki kula da gidan"
Najma ta kalleshi, "Abba Dan Allah zanbiku,"
Sanin shaquwar datake tsakanin sune yasa baiyi mata musu ba, gaba dayansu suka futo daga gidan, bakin titi sukaje sukatare adedeta guda biyu suka tafi
Saif yana zuwa gidan Malam yatarar dashi tareda dalibai masu daukar karatu
Saida ya tsaya suka gama sannan yamatsa kusa dashi yayi masa bayanin komai, Malam ya jinjina kansa yace "ikon Allah, to bari muje asbitin, Allah yabata lafiya, saif yace" Amin Malam "
** *** **
Yanda take rusa uban kuka takama hannun umma da yaya Salisu ne yasa dayawa daga cikin jama'ar asbitin hankalinsu yayo kanta
Umma tace" sai shegiyar rauta kikewa mutane, ba zakiyi shiru kiyi addu'ah ba, kukan naki ne zai dawo miki da idon?

"
Salisu yace" haba umma, kiyi hakuri dan Allah "
Najma da nura ma suka fara bata hakuri
Suna yankar kati kai tsaye suka turasu wajan ganin doctor,Kamar yanda tayiwa iyayen nata bayani shima haka tayi masa, daga nan ya turasu wajan wani doctor din yafara duba idon nata
Takwas saura saif yaqaraso shida Malam
Tawaya suka kira su Abba sannan suka fada musu dede Inda suke, suka qarasa
Gaba dayansu azaune suke akujerun dake wajan, kowa da abinda yake saqawa acikin ransa, Salisu tunani yake akan ko wanene wannan yaron, sai Inda karfinsa yaqare akansa, saboda bazai taba yiwa qanwarsu qwaya daya tal aduniya haka yazuba ido yaqyaleshi ba
Wayarsa yadauko daga aljihun gaban rigarsa, yakira Sultan, yana dauka yace "Sultan akwai damuwa fa"
Shima daga bangarensa yace "wacce irin damuwa kuma ana zaune lafiya"
Yace"wallahi wani yaro ne yawatsawa Baby shaltos a'idonta, yanzu haka maganar danakema tace bata ganin komai, duhu kawai take gani, muna asbitin Malam Aminu, gasu Malam nanma duk sunzo "
Yace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, saikuma yadawo yace" bantan uba
, kace akwai Yaqi, gobe Zan biyo Mota nataho Gida "
Salisu yace" a a karkai gaggawar zuwa kabari muga yaya zata kasance tukunna, yanzu de akwai likitan dayake duba idon nata, basu futo bade har yanzu "
" yaya Salisu alalatawa qanwarmu ido kace inzauna?

Baby fa, Babynmu yaya Salisu, me wannan yarinyar zatayi da za'ayi mata wannan abun, nasan halin Baby yaya, ba zatayiwa wani mummunan laifin dazaisa ayi mata hakaba, yarinyar da magana ma bata dameta ba, Yaya Salisu sai kun ganni kawai "yana gama magana yakashe wayarsa
Malam yadubi Salisu yace" Salisu kunyi sallah ne?

Abba yace "ai Malam gaba dayanmu ma, babu Wanda yayi sallah, daga magrib har isha'i,"
Malam yadafe kansa, "kash, tokuje kuyi sallah, ni saina zauna"
Haka akayi kuwa, gaba dayansu suka tafi, shikuma yazauna da carbi a hannunsa yana ja, tareda zubawa dakin da aka shiga da Nawal ido yana tunani
Bayan sun dawo daga sallah ma saida suka dade azaune sannan likitan yafuto, gaba dayansu suka nufeshi, jikin kowa yayi sanyi saboda ganin fuskar likitan babu wani annuri
Malam ne yace "likita yaya ake ciki dangane da jikata?"
Ajiyar zuciya yasauke "gaskiya baba akwai matsala, idanunta sun riga dasun samu matsala _, I am sorry to_ _said_ bazata sake ganiba, _because of_ _Chemical_ din da'akai amfani dashi wajan zubawa idanun nata yanada qarfi sosai, yataba Ruwan idanunta sosai, Inda Allah yarufa Asiri ma akwai sauran ruwa acikin idanun nata, amma da babu ruwan gaba daya to gaskiya saide muyi kokari mucire qwayar idon saboda kada tafada ciki, "
Cikin kuka
tace" Innalillahi yanzu likita shikkenan yar'uwata tarasa idanun ta?

Shikkenan bazata sake ganiba?

Tadena ganinmu kenan?

"cewar Najma
Malam ma yace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, saida ya maimaita hakan sau uku, sannan yace yanzu likita babu wani kokari dazaku iyayi akan idanun nata?"
" um akwai abinda za'a iyayi akai, idan anyi mata aiki da yiyuwar idanun nata su dawo, ya danganta da irin ciwon mutum, ciwo ciwo ne, wani anayin aikinsa Naira million daya, amma wannan inada tabbacin za'a iya yimata a Naira million daya da dubu dari da sittin "
Cikin faduwar gaba Abba yace" million daya likita?

Yaro ina zamu samu wannan kudin?

Kutaimaka kuyi mata wannan aikin likita, Ahankali saina dinga biyanku, wallahi tallahi ko Zan saida kadarata gaba daya kudin bazasu kai hakaba "
" baba ba laifi na bane, Inda inada damar yimata aikin babu ko sisi wallahi zanyi mata, nima ma'aikaci ne Kamar kowa, sannan ba aikine da mutum daya zai gudanar dashiba, kuma wannan shine gaskiyar maganar dana fada muku ko ina kukaje hakan take inde aiki kukeso Mai kyau, amma idan baku yarda ba zaku iya tuntubar Babban asibitin ido na qasa dake Kaduna, inyaso sai ayi mata aikin Acan "
Malam yace" yaro munji, baqin zancenka mukai ba, maganar anan guda dayace, ina za'a samu wannan kudin?

Tayaya zamu samesu?

Ta wacce hanya?

Yace "kuyi addu'ah baba, sannan kuma ku nema, Allah yaana tare daku," daga haka yayi gaba yashiga wani dakin
Umma tace "Alhaji ina ganin kawai mubar asibitin nan, mukoma gida, haka tata qaddarar take"
Salisu yace "umma wacce irin magana ce wannan?

Muje mu nemo yaron daya yayi mata hakan, yazo yabiya kudin, ko kuma hukuma tayi mana maganin sa"
Girgiza kai Malam yayi "duk ba wannan ba, Dan Allah kuyi shiru mu nemawa kanmu mafita"
Idanun Najma jajir tashige dakin da aka kwantar da Nawal
Umma ma bayanta tabi, duk suka shiga dakin kowa yanemi waje yazauna, kowa yayi shiru,
Tana kwance amma hawaye ne yake tsiyaya daga idanunta
Malam ya dubeta yace" 'yata Nawal, kifada mana menene yake faruwa?

Ya akai haka tafaru?

"
Shiru tayi babu amsa, kawai hawayen baqin ciki ne yake zubo mata
Umma da idanunta sukai jajir saboda kuka tace" ka rabu da ita Malam, kabarta tayita zubar da hawayen, tunda dama ance sun qare idan tazubar dasu gaba daya ai shikkenan, "taana gama fada hawaye ya silalo daga idanunta
Malam yace" a a kukanta ko rashin kukanta ai babu abinda zai sauya qaddarar ubangiji "
Yasaka duban Nawal din" fadama na abinda yake faruwa "
Hannuwanta guda biyu tasa tashare idanunta sannan tace" duk ranar dazan tafi makaranta sai sunmin magana, bantaba kulasu ba, wata rana har munafuka suke cemin, waini ina ganin su subasa ganina, bantaba tanka musu ba, shine jiya wani daga cikin su Mai suna Anwar yazo yasha gabana yasa hannu zai yayemin niqab d'ina, nikuma zuciya ta d'ebeni namareshi,baimin komai ba a lokacin, sai yau suka tareni zasu watsamin _Acid_ , Allah bai basu damaba shine suka riqeni suka fesamin shaltos...

Yaqarasa maganar cikin kuka
Malam yace "subhanallah, subhanallah, Nawal
Tace" na'am "
" wai shi wannan niqab din wajibi ne ko sunnah ?
, incede babu kod'aya?

To daga yau namiki katangar qarfe tsakanin ki dashi
, kibar fuskarki abude kowa yagani, duk Wanda bazaice masha Allahu ba yayi miki wata maganar kice ((Li'ilafi quraishi))
inace shikkenan zance ya wuce?
haba Nawal, ina tarbiyarki take?

Meyakaiki marin namiji?

Nawal Inda wani nefa kai tsaye pyade zaiyi miki, kinga shikkenan yarusa miki rayuwa, yayi miki tabonda har jikokin ki sai sun samu labari, meyasa Tun farko baki sanar Dani suna bibiyar kiba?

Kinga da hakan bata faruba, dana hanaki bin hanyar kwata-kwata, awanne Gida yake?

Ko bakisan gidansu ba?

"bansan gidansu ba Malam, nide nasan koda yaushe a wannan wajan suke zama, anan nake ganinsu kullum"
Cikin huci yace"amma wannan yaron daya sake yazuba miki _Acid_ dinnan wallahi sainaje har Gida nazubawa uwar Data haifeshi "cewar Salisu
Malam yace" a a Salisu, ba'a maida sharri da sharri, ya maida dubansa Ga Abba, "yanzu yaya za'ayi?

Yaya zamuyi asamo kudin ayi mata aikin?

Abba yace" Malam, banida Inda Zan samu wannan kudin, ko dubu hamsin baza'a samu awajenaba bare zunzurutun kudi har nera million daya da dubu dari da sittin, saide asaida gonakina, ahada da gidan damuke ciki, "
" Abba Dan Allah karka saida gidanka akaina, nasan haka Allah yaso yaganni shiyasa yamaidani hakan, Abba idan ka saida gidanka ina zamu koma?

Mutafi Gida kawai Abba, Allah yasakamin, nabarshi da ubangiji, nasan zaiyi mana hisabi "
Saif yace" ke komai da anta'baki saikice hakuri hakuri, shima wannan din anufinki hakurin za'ayi?
Chapter 5 · 0% Book details