← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 48

Sashe 23

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yarinyar datake university?"
"ki qyaleta"
Tace "aqyaleta haka ta zauna Babu makaranta?"
Babu kunya yasake cewa "eh"
Ummi bata sake yimasa magana ba, Nawal takawo masa abincin, ta ajiye masa batare datace komaiba
Shima baice da ita uffan ba, Ummi duk tana kallansu, anan tasake tabbatar wa gara tamaidasu wani gidan su kadai
Ko 5 spoon baiyiba ya ajiye yatashi yace "Ummi gudnight"
Tace "to Baffah saida safe"
Baifi minti talatin datafiyaba, Ummi tasata tayi wanka, tabata humra Mai qamshi tashafa, sannan tasaka kaya madaidaici, dede bacci, takama hannun ta sukayi part dinsa
Saida suka je har falo sannan ta nuna mata d'akinsa tace "ga dakin naku can,
kije ki kwanta saida safe
Jikinta ne yayi sanyi, haka tafara tafiya salalo salalo, har taje bakin kofar dakin tajuyo taga Ummi tana tsaye, Ahankali ta tura kofar dakin tashiga, Ummi kuwa tana ganin shigarta dakin tajuya part dinta ranta fess
Tana shiga dakin taga duhu ya gauraye, gashi ya qure esi bayan sanyin da ake na duniya,maida kofar tayi tarufe, duk abinda ake yana jinta domin kuwa ba bacci yakeba, Tun daren shekaran jiya rabonsa da bacci Mai dad'i daya fara zai farka
"ke me yakawo ki cikin dakina?" ta tsinci maganar sa
Tsorone yakamata, cikin sanyin jiki tace "Ummi ce takawoni"
"kijuya kificemin daga daki"
Zuwa yanzu kam muryarta tafara rawa tace"dan Allah kayi hakuri, "
Tashi yayi zaune, yakunna wutar dakin, haske ya wanzu adakin taganshi muraran Babu kaya da gashi sai gajeren wando, murdaddan jikinsa takalla, ga qirjinsa duk gashi tayi saurin kawar da idonta
Cikin bacin rai yace" zaki fice ko saina taso?

"
Hawaye suka zubo mata tace" to ina zanje?

"
" kifice kibarmin dakina, ke bayan d'akinama kifice daga part dinnan Gaba daya "
Tsugunnawa tayi awajan, tafara rusa kuka," wayyo Allah na yaya Sultan nashiga uku kazo ka ceceni"
( Sultan ga ranarka
Baqin ciki da taqaici suka kamashi, saikace Wanda yadaketa take kira masa wani qato yazo ya ceceta yace"ke bari kiji, ba Sultan ba,ko Sarki zaki kira saikin barmin dakina " ya yunqura zai sakko daga gadon, tana ganin haka tatashi tana goge hawaye tafice daga dakin tareda jawo masa kofarsa
Yace" fine"tareda kashe wutar dakin ya kwanta
Tana zuwa falo tayi kwanciyar ta akan kujera, saide daqyar baccin ya dauketa saboda tsoro, tasaba kullum gata ga ummanta take bacci
Ana kiran sallar asuba tafice daga part din tatafi dakin Ummi, a lokacin Ummi tana kan sallaya kawai sai ganin Nawal tayi, tace "Nawal yanaganki Tun yanzu?

Lafiya kuwa?"
"Ummi lafiya kalau, yatafi masallaci ne, shine nataho nan"
Ummi tayi Murmushi tareda girgiza kanta kawai
Gari nayin haske bayan sunyi break Ummi ta kalleshi tace "Baffah jeka hado kayanka zaku komai gidanku"
Cikin sauri Nawal ta kalleta
Shima cikin mamaki yace "Ummi gida kuma?

Menene laifin nan din?"
"to idan kagama Tambayar tawa bari ni naje nadeboma kayan naaka, tunda ban isa nafadama ba"
Miqewa yayi batare dayayi magana ba, daga hado kaya yaje ya zauna har Ummi tafara tunanin binsa sannan yashigo falon dauke da troly guda daya ya tsaya akansu batare daya zauna ba, hannunsa daya dauke da jaka, dayan kuma ya turashi cikin aljihun wandonsa
Ummi ta kalleshi tace "kayan Nawal suna cikin motar ka, kaje kakai gidan dakake ajiye baqi, nan zaku koma da zama, muma gamunan zuwa"
Fita yayi daga falon ransa duk ba dadi
Ummi ta kalli Nawal " 'yata kiyi hakuri da halin Baffah, watarana zai sauya, temako daya nakeso kimin shine kitayani daidaita Baffah, duk abinda kikaga Babu agidan kiyi masa magana, Karkiji shakkarsa mijinki ne, tundaga ranar da' aka daura muku aure kun zama daya, zaisan sirrin ki zakisan nasa, ki temakamin Baffah yadena wasu halaiyar tasa "
Zancen zuci tafara, wai tayaya kowa yake cewa nasashi yadena wasu abubuwan, tayaya zan iya?meyasa suke son doramin abinda ni nasan ba lalle na iyaba?

Domin tabawa ummi qwarin gwiwa sai tace"to Ummi insha Allah"
Daganan Ummi tabata magungunan tsimi, dana infection tace ta dinga amfani dashi, itade kawai takarba ne, amma idan tasha ma amfanin mezai mata bayan d'aki ma ana korarka bakada ikon kwana aciki
Har gidan Ummi tarakata, a lokacin dasukaje baya gidan, sannan tasake yimata fada akan tayi wa mijinta biyaiya, daga nan tayi mata sallama tatafi gida
Ummi na tafiya taga duk gidan yamata fadi, wayarta tadauka takira Najma sukaita fira, har taji ranta yadan saki,suna sallama taga ba'aja mata ko sisi ba
Inbox dinta taduba tagani ko wanine yayi mata transfer amma bataga komaiba saika data dataga wata number ta turo mata
Alokacin takira number akaqi dauka
Afili tace to may be bonus aka bani
annan ta fita harabar gidan tana kallan tsari da kuma yanayin gidan
Gidan yayi kyau, kuma ya birgeta sosaai, harabar gidan tanada girma sosai, bakin gate ta kallah tahango maigadi yanajin redio, ta qarasa suka gaisa, sannan tadawo ciki, can wajan gefe wajan bayan dakunansu ta duba taga wani Dan qaramin swimming pool, cikin murna tace "laaaaa tareda qarasa wa wajan da gudu, tana zuwa tafara wasa da Ruwan, kafarta ta tsoma aciki cikin sauri tajanye saboda sanyin dataji
Awannan wajan anan ta wuni, sai wajan yamma lis sannan ta koma daki
Da daddare batayi girki ba, saboda tagaji, kawai lemukan da tagani a fridge su tasha ta qoshi, ta kunna kallo tayi kadan sannan taje dakin da aka saka mata kayan ta tayi wanka ta kwanta
data fara jin tsoro zata leqo ta window ta kalli dakin maigadi, idan tahango hasken fitilarsa saita koma ta kwanta, haka taitayi har bacci ya dauketa
Shikuwa bai dawo gida da wuri ba, sai dare, daya dawoma ko dakin datake bai nemaba yawuce d'akinsa ya kwanta
Da asuba tana idar da sallah tafara karatun qur'ani har gari yayi haske, qur'anin ta dauka tafita waje tanata zagayawa tana tilawa
Cikin baccinsa yaji qira'ah kai dad'i tana rera karatun qur'ani adede satin window dinsa
Idanunsa cike da bacci yajawo wayarsa yaduba time 7:41
Ahankali yatashi zaune, shibe koma bacci ba shikuma baitashi ba
Kansa yadafe da hannunsa, Tun shekaran jiya yakeso yayi bacci amma damuwa ta hanashi, yanzu yau yasamu baccin yafara daukar sa amma ita kuma wannan ta hanashi
shide bashi da damar hanata karatun qur'ani
Dole sai hakura yayi da baccin yatashi yashige toilet, daga nan yayi wanka yafice daga gidan gaba daya
Da yamma tana zaune tafara tunani, ta wacce hanya zata shirya Baffah?

Tasan de masu irin wannan halin hanya ta farko itace kadinga tunatar dasu, to amma tayaya?

Shida baya zama agidan?
dole bari zatai sai ranar dayake zaune agida saita fara gabatar da makaman yaqinta
Washe gari dasafe ma karatunta ne yatadashi daga bacci, gashi idan yatashi daga bacci zaiyi wahala ya koma a lokacin, Already yayi sallar sa tun asuba Dan haka kawai yatashi yayi wanka yafara duba wasu document, a cumputer
Yanajinta har zuwa lokacin data gama karatun
Itama anata bangaren bayan tayi wanka taci abinci, sha biyu saura a lokacin, ta duba waje taga duka motocin gidan suna nan, alamun yana nan yau bai fita ko inaba, browsing tayi tadauko wa'azin da ake magana akan kule-kulen yanmata
Shikuwa yana d'akinsa a lokacin yagama aikin dayake zai kwanta yayi bacci zuwa azahar
A lokacin takunna tv tajona wayarta tayi connecting sannan takunna wannan wa'azin ta qure volume yanda zai iya jiyota
Bacci yafara daukar sa yaji gida Kamar zai fashe da qaran wa'azi
Yadauki fillo yatoshe kunnuwansa dashi, amma still bai daina jiba, cikin sauri yatashi zaune yace"yau nashiga ukuna
, yarinyar nan ita kadai ma ciwon kai ce, yau bazata taba bari na na rintsa ba
Da asuba karatun qur'ani,yanzu kusan sha biyun rana ta kunna wa'azi,
ko kasheni takesonyi ne?

Cikin bacin rai yafuto daga d'akinsa da gashi three quater Mai laushi,Babu riga ajikinsa sai vest, murdaddan jikinsa yafuto fili
Adede lokacin daya qaraso Mai wa'azin yake cewa Kuma maza kuji tsoron Allah, kudena damuqar matayan daba naku ba, ko hannun mace ka riqe hakan haramun ne, bare kuma ka rungumeta kasata a qirjinka batare da aure ba
, sannan kuma yanmata kuriqe mutuncin kan...

Yana qaraso wa wajan yadauketa cimak yadora ta akafadarsa yayi bayan dakin su da ita
Harbe Harbe tafara tana cewa "kasaukeni, wallahi nadena, Dan Allah kasaukeni, kayi hakuri"
Amma ko Saurarar ta baiyi ba, saida yaje bayan dakin su kawai ya wullata cikin swimming pool dinnan yajuya, ga sanyin da akeyi agari, shi kansa Ruwan yadau sanyi, tanajin ta cikin Ruwan ta shid'e
Tafara karkarwar sanyi, tana kira "ka temaka min,zan mutu"
Tana kokarin futowa santsi yajata takoma ciki can qasan Ruwan, aikuwa sai ruwa yafara shiga hancinta da bakinta bul-bul-bul, daga nan tasume
Shikuwa yakusa shiga falo yaji shiru, yadena jiyo ihunta, Kamar wasa yajuya ya kalli wajan kawai sai yaga Babu yarinya Babu dalilinta
Gabansa yayi mummunar faduwa, cikin sauri ya furta Innalillahi...
Chapter 23 · 0% Book details