← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 48

Sashe 27

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shareta yayi yashige daki, itama bayan sa tabi da kallo ranta na quna idan tatuna da zobunaan data gani
Tashi tayi tashige cikin daki tace" Nas kiban shawara, inaso nakawo qarshan matsalar gidan nan "
Nas tace" to yanzu kuwa Zan baki shawara, menene yake miki Wanda bakyaso?"
" Nas bayacin abinci na, babu magana Mai dad'i, kullum acikin aikin doka nake, karfe bakwai dede nafita nafara aiki, sannan kayanda Ummi takeso yadena sawa ta zubamin ido tana jira taga result amma har yanzu nagagara yin komai"
"Beauty maganar gaskiya itace kinada tsoro, kuma dole saikin dena jin tsoron sa sannan ne zaki gyara gidanki"
Tace "Nas haka Ummi ma tace"
"ato kingani, dole saikin dena tsoron sa, sannan tunda kinyi biyyaiya ai kin fita haqqinsa, tunda haka yakeso kema ki zama mahaukaciya, zaku fi dedetawa"
Nawal tace"a a fa Nas, Karki bani shawarar dazanzo ina kuka daga baya, kinga shawarar zuwa Abuja ga yanda ta qare mana
sannan shawarar zuwa makaranta haka kikasa nazo qarshe nahadu da Ummi nanma Abba yahauni da fada
Nas tace" Karki damu, ki gwada wallahi "
Daga nan sukai sallama
Tana kashe waya tace" goben wasan zai fara
Washe gari ta dinga jira yafita, bai fitaba, sai yamma yafita, yaje gidan Ummi
Tana ganin fitarsa tashige cikin d'akinsa, kayansa qananu Wanda suke crazy da riguna Wanda taganta da yaga ko kadan ce, tadinga debowa tana zubasu akan gado
Saida ta kwashe duk kayansa crezy sannan taje harabar gidan ta zubasu waje daya
Kitchen takoma tadauka fetir
tadaga bakin jarkar ta kwara musu
Sannan ta qyasta ashana ta banka musu wuta
Nan da nan wuta takama kaya taanaci
Adede lokacin yadanno hancin motarsa cikin gidan yaga hayaqi yana tashi, ga Nawal a tsaye a gefe
cikin sauri yabude motar yafuto yaqaraso wajan
Kayansa yagani yanaci da wuta
yace"kai kai kai kayana kika qonamin?

"
Tace" to menene amfanin su?

Banaso naga kana sakawa, sannan amatsayina na matarka, inada haqqin hanaka sakawa "
" nikike na fadawa wannan maaganr saboda rashin kunya?

Kewai mekike taqama dashi ne?

Bafa sanki nakeba inada wadda nakeso, bazakizo har gidana ki nemi ki dagamin hankali ba"
Dama ga haushin wannan zobunan daga gani adakinsa yana cin ranta, cikin bacin rai tace"to ni din cemaka akai inasonka?inada Wanda nake sosai nima mutum Mai tausayi da hangen nesa "
" Karki sake ambatar sunan wani a cikin gidannan, sannan abu na qarshe, yafara tafa hannunsa yace"nagaji da halin ki, ki tattara kayanki kitafi gida, saina nemeki "
Maganarsa tabata tsoro, amma data tuni shawarar Ummi data Nas saita dake tace" wallahi Babu Inda zanje, "
" Ok haka kikace?

"
Ta kalleshi tace" qwarai kuwa BAFFAH haka nace "
Yace" nikike kira da Baffah,?

"ya iyo kanta gadan gadan
Tana ganin haka ta kwasa aguje, shima yadoru a bayanta
Kasancewar da hijabi a jikinta sai hijabin yake ta tashin iska
Ko'a'ina wannan gudu zai tsaya?

Wani lokacin zakuna ganin posting kadan, saboda mkrnt danake zuwa, wataran kuma zaku iya jina shiru, amma insha Allah zanyi kokari naga ina turo muku ko yaya ne
pls sharhi Dan Allah
Mrs Usman ce
[2/4, 10:18 PM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
29&30
Cak yatsaya daga gudun dayake tareda juyawa gida, yana haki yana cewa saide ki nemi wani gidan amma ba nanba
Ita kuwa tsabar tsorata ko Juyowa batayi taga yana binta ko baya binta
Saiji tayi tayi karo da Mota, Allah yarufa Asiri motar bata gudu,shiyasa bataji ciwoba, sai haki take, takasa daidaita numfashinta, Dasauri tafuto daga cikin motar cikin mamaki ta kalleta"Nawal, keda waye kike gudu haka Kamar kinyi gamo?

"
Dago kanta tayi Dasauri jin muryar Ummi
Cikin haki tace" Ummi mutafi gida, zai dakeni "
Ummi tasa hannu ta dagota tace" Babu abinda zai miki, tashi mukoma gidan "
Bayanta takoma tabuya Kamar yana wajan tace" A a Ummi, mutafi gida Dan Allah "
Ummi de cikeda mamaki tajata tasata amota, suka juya zuwa gidan Ummin
*** ***** ***
Yana dawo wa gidan yasa dayyabu ya gyara wajan data bata, sannan yawuce d'akinsa tareda dafe kansa da hannunsa duka biyu, duk Ummi ce ta janyo masa wannan rainin awajan yarinyar nan, amma banda haka kisa hannu ki dauki sutura ki qona?

Wardrob dinsa yaduba yaga Babu komai takwashe qananun kayan sai manya
wani kayanma rabonsa daya waiwaicesu ya Manta
Yasan bazata wuce gidan Ummi ba, Dan haka bazai damuba
Dole yatashi ya nemawa kansa mafita, wannan zaman Babu Inda zai kaishi, yanada abubuwa dayawa dasuka tsaya masa arai, kuma yarasa dawa zai tattaunasu, yakamata ya nemi wani mutumin Mai ilmi sosai
daga nan yatashi yayi masallaci domin sallar magrib
*** ***** ***
Zaune suke afalo, Ummi nakan kujera Nawal na zaune aqasanta
Ummi ta kalleta "Nawal ki fadamin gaskiya, menene yahadaki dashi har kike wannan gudun?"
"Ummi nice nayi masa laifi, kayansa na qone masa, saboda banaso yana yawo acikin kayan, kuma banida qwarin gwiwar dazan iya hanashi, shiyasa nayi tunanin qonesu"tana qarasa fadar haka hawaye suka zubo mata
Ummi tace" to menene abin kukan kuma?

Ko akwai wani abu bayan haka?"
" Ummi cewa yayi natafi gida saiya nemeni "
Ummi tayi tagumi tama kasa magana
, Kallanta tasake yi tace" Nawal Baffah yataba biya miki haqqinki na aure?

"
Tambayar tayi mutuqar yimata nauyi, cikin sauri ta sunkuyarda kanta qasa
Nan take Ummi ta gane Babu abinda yafaru, sannan tace" Nawal ina wayonki yake?keda kike yar zamani, keya kamata kiyiwa mijin ki shiga Mai kyau ta daukan hankali harki jawo hankalinsa gareki, aishi ba dutse bane, dakinja hankalin sa cikin Ruwan sanyi zaki bashi umarni yabi, ciki harda hanashi saka kayan, ni kaina banaso yadinga wannan shigar Nawal, abin yana mutuqar damuna, yan'uwan mu dasuke yola dayawa daga cikin su gani suke zuba masa ido nayi kawai naqyaleshi, namiji Kamar yaro ne awajan matarsa Nawal, keda kanki zaki iya sarrafa abinki ayayinda yashigo hannun ki, to amma Babu damuwa, zanyi maganin abun, zansa sabira taje tadauko min wayarki, sannan kishiga daki Karki kuskura naqara ganin koda kafarki ne afalo, zansa agyara miki wani dakin kikoma can gaba daya, kada kifuto harsai nabaki umarni "
Cikin nutsuwa tace" to Ummi, mungode "
Sannan tatashi tashige dakin ummin
*** ***** ***
Yana zuwa gidan, Ummi taganshi fuska atamke, da alama akusa yake
Tea takesha yayinda take aiki a computer, yana zuwa yafada kan kujera tareda dora kansa akan cinyarta
Fuskarta Babu alamun Fara'ah tace"ina cinyar taka matar"
Kallanta yayi "yanzu Ummi laifi ne danna Dan kwanta?"
"Babba ma kuwa, kakoma wajan matarka, inkuma ciki kakesan komawa to
Ahankali yatashi yafara leqe leqe ko zaiga Nawal, ta kalleshi, sarai tasan ita yake nema, sai tace masa "yaya Nawal din take?"
Cikin ransa yace tofa
kenan batazo nanba?

Sumar kansa ya shafa yace"tana nan lafiya Ummi "
Kamar an tsikareshi yatashi yace" Ummi bari inje masallaci, saida safe"
Tace"toshikkenan ka gaishe ta, saida safenku "
Yana fita yatsaya ahabar gidan, to ina yarinyar nan tatafi?

Karfa ace gidan tatafi, to amma tayaya zatayi gangancin hawa motar haya bayan da aurensa akanta?
(waannn aure
Direct masallaci yaje yayi sallar isha'i, bayan an idar bai tashiba, saida yabari kowa yafice daga masallacin sannan ya qarasa wajan limamin suka gaisa, liman yace"muhammadu mungode sosai da kokari, ana yawan aiko mana da sadaka, mungode sosai, Allah yajiqan mahaifa
Cikin yanayi na damuwa yace"amin Malam, dama akwai abinda yake tafe Dani "
Liman yace" to inajin ka muhammadu "
" Wato Malam, wasu 'yan watanni dasuka wuce naje ta'aziyya kano, saina hadu da wata yarinya, tundaga lokacin nake mafarkin ta, kuma Allah da ikonsa banga fuskar ita wannan yarinyar ba, saide wani sashi na fuskarta,naji wasu yara daga bayanta sun kirata da Baby, wallahi Malam ina cikin halin damuwa, ina buqatar kyakykyawar shawara, saboda yarinyar tana yawan zuwamin cikin mafarki
Kwatsam rana daya sai mahaifiyata tahadani aure da wata, bana sonta, itama yarinyar bata sona, to tunda akai auren, Allah yasaakamin kishinta acikin raina, ina mutuqar kishinta, bansan dalili ba, yanzu hakama de maganar danake ma mun samu sabani da ita nace taje gida saina nemeta "
Liman yace" subhanallah, subhanallah, muhammadu akwai matsaloli Wanda dole kaine zaka gyara su da kanka, na farko muhammadu ba'a taba samun kishi saida soyaiya, muhammadu Allah yasaka maka qaunar matarka acikin ranka batare daka shirya ba, kana sonta, yakamata kajata ajikinka ka koya mata yanda itama zata soka, idan ka kwantar da hankalin ka ka rungumi abinda mahaifiyarka tamaka Zabi dashi sai kaga ta Sanadin haka Allah yabaiyana ma ita waccen yarinyar dakake mafarki, sannan kai namiji ne kanada damar dazaka iya auren mace hudu, bare guda biyu, saboda haka ka tsananta bincike akan yarinyar harka sameta, kahada su su biyu, zakafi samun nutsuwa acikin zuciyrka, kuma muma anan zamu dage dayima wasu 'yan addu'o'in "
Yace" Wato Malam, ba auren ne matsala ba, matsalar shine adalci, bazan iya musu adalci ba, ni kaina nasan cewa bazan iyaba, idan nace zanyi to haqiqa na yaudari kaina "
Murmushi liman yayi yace" karka damu, wanaan duk wani abu ne dayake hannun Allah, insha Allah ubangiji yana sane dakai, idan kayi addu'ah zai duba lamarin"
Shiru yayi, jikinsa yayi mutuqar sanyi, yace"to Malam nagode "
Liman yace" Babu komai muhammadu, ai Zan iya yima komai karka damu "
Daga nan yafuto daga masallacin jikinsa a mutuqar sanyaye
Direct gidansa yawuce, afalo ya zauna yadafe kansa da hannunsa
tareda lumshe ido, afili ya furta" tayaya?

Iname hakan tafaru Dani?

Me zance da Baby idan naganta?

Tayaya zanso wannan yarinyar bayan nariga dana mallaka wa Baby zuciyata da gangar jikina?

Fillon dake gefensa na kujera ya dauka yayi jifa dashi, da karfi yadaga murya yace "Baby!!!!"
Gaskiya dole nanemawa kaina mafita, wayarsa ya dauka yakira Yasir
"hello Yas"
"na'am mk yahutu"
"to alhmdlh za'ace"
Yasir yace"aikin daka turonifa yadade da qarewa, dama inaso kasamin lokaci nazo akwai maganganun danake so mu tattauna akai"
Yace"Ok Babu damuwa, but kafin nan inaso ka bincika min wata yarinya agaba da layinku take"
Yas yace"yarinya kuma mk?

Yaushe kayi aure?

Sannan....
Chapter 27 · 0% Book details