← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 48

Sashe 17

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mezaije yamata?tokode sanar dashi zatai yaje amatsayin waliyinta, shiyasa tafara maganar ta naso ta gayyaceshi?

Tsaki yayi tareda juyawa ya Yarufe idonsa,cikin ransa yace"kuma fa muryar yarinyar akwai zaqi "
(jeka dai
ko banza akanta kafara karya aqidarka
taqin daga waya
*** ***** ***
Hawaye masu dumi suka zubo mata, shikkenan kuma tata ta qare, Wanda take taqama dashi dinma yaqita, amma duk da haka bazata iya auren Nuhu ba, gara abata wani daban Wanda bata taba ganinsa ba, dade abata Nuhu, idan ta auri Nuhu da tsaftarsa zataji koda tsaftar Gida da yaransa, hawayen idonta tashare, ta futo tsakar Gida tayi alwala, sannan ta koma daki tatada kabbarar sallah, raka'a biyu tayi bayan tayi sallama tasake maida goshinta qasa ta karanta (la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin) sau arba'in da d'aya, sannan tafara kuka tana fadawa Allah buqatunta domin kuwa duk Wanda ya karanta wannan addu'ah to manzon Allah yace bazai dagoba face an amsa masa addu'arsa
Sai tsakiyar dare ta kwanta, washe gari haka ta tashi kanta nayi mata wani irin mugun ciwo saboda damuwa, Abba taje tafara gaisarwa ya amsa mata fuskar sa Babu yabo Ba fallasa
Sannan takoma wajan umma tsakar Gida tafara tayata aiki, anan take sanar da ita abinda Abbanta yace dangane da kawo miji
Shiru tayi batace komai ba, tome zatace?

Wanda take taqama dashi din shima ya watsa mata qasa a ido, baabu Inda zataje tanemo wani mijin, zata jira har lokacin daza'a sake kiranta a tambyeta inyaso saita sanar dasu cewa subata koma wanene amma banda Nuhu
Umma tace "kinyi shiru"
Ahankali tace "naji ummah"
Sai azahar yaya Sultan ya shirya yatafi bayan yagama kwantar mata da hankali cewa insha Allah zata auri Wanda takeso
Abincin kirki takasa ci, duk idonta yafada yini daya kawai,
Da yamma tana zaune afalo mus'ab yashigo yace "yaya Baby Nuhu yazo"
Tana jinsa tayi banza ta share shi, qarshe ma tsakar Gida tadawo ta zauna, kusan minti talatin tadauka azaune atsakar Gida itadasu umma da mama, Yaya Salisu yashigo gidan yadubeta yace"ke ba Nuhu nagani a kofar gida ba?

Koba wajan ki yazoba?

"
Cikin haushi tace" ba wajena yazoba yaya, tunda in wajena yazo ai zai fadamin yaya "
Umma datayi shiru tana jinsu tace" ba wajan ta yazoba Salisu, wajena yazo, ai kasan bazawari nane"
Idonta ne yaciko da kwallah tatashi ta shige daki tadauko hijabi tasa tafice
Mama mariya tace "kuma de kun dauki Nuhun nan kunsashi aranku saikace wani dan'uwanku, tunda yarinya bataso aqyaleta mana, shi inbanda shegiyar jaraba da naci yau kakira mace gobe ka kirata kajera sati daya kana nemanta amma ita ko flash ai anan ma kadai zaisa kafara tuhumar kanka, amma saboda duhun kai Yaqi ganewa, ita yarinyar nan inkazo ruwan nera biyar ba baka takeba, ba kiranka takeba, ba text take makaba, amma kadage kai ala dole sonta kake?

Wallahi Inda wajan Najma yake zuwa rufe kaina zanyi inje ince karya sake zuwa kofar gidan nan"
Umma tace "to Mariya tunda bata sanshi ai saita kawo wani"
Tana zuwa kofar gida ta ganshi a tsaye, farin yadi ne ajikinsa itade tunda takeda Nuhu bata taba ganinsa da wani kalar kayan ba, kullum cikin farin yadi yake, kallansa tayi daga saama har qasa, idanunta yasauka akan hannun rigarsa yayi duqun duqun yayi baqi, haushi yakamata, ba ance tunda bata sonsa meya hana ta fada masa ba? yau kuwa za'ayi ta taqaare, tace "sannu Nuhu"
"yauwa my heart"
Tace "Nuhu, akwai abinda nakeso nasanar dakai, maganar gaskiya Nuhu, ni bantaba sonka ba, kayi hakuri banajin Zan iya aurenka, abu ne me girma awajan mace ta kalli d'a namiji tace bata sonsa, zaiyi wahala mace ta fadawa namiji haka, amma tunda kaga nabudi baki nafadama hakan agabanka baqaramin rashin so nake maba, nanunama ta hanyoyi da dama yanda zaka gane amma kakasa fahimtata, hannunta tahade waje daya
Dan Allah Nuhu kafita daga rayuwa ta, bakamin laifin komai ba, haka kawai Allah bai sakamin sonka acikin zuciyata ba, "
Daaga nan tawuce gida tabarshi a tsaye
Batafi minti biyar dashiga gidaba saiga Nura yashigo da leda ahannun sa, yabawa umma yace" umma gashi inji Nuhu wai yaya Baby ta Manta, natane "
Umma ta karbi ledar
Mama mariya tace" Allah yarufa Asiri, aida kabar masa kayan sa, d'an me naci"
(mamafa tadage
*** ***** ***
Washe gari Nuhu yadawo, wannan karon dayazo kiranta yayi awaya, tana gani tayi rejecting, haka sukai tayi har sau hudu sannan ta daga ana biyar
Yace "Malam Nawal nazo ina kofar gida"
Tace"akwai abinda nakeyi, meyahanaka kira ka fadamin cewa zakazo idan ina nan shikkenan idan bana nan basai kazo ba?

"
" kiyi hakuri minti goma yayi yawa kindawo gida "
Tace" dama ai ko baka fadaba "
Umma tasamu afalo tazo zata wuceta tace" ke ina zaki?

"
Ciki ciki tace" kofar gida Zani wajan Nuhu "
" yawwa nina Manta ma ga kayan daya aiko miki dasu jiya can a dakin Abban ki, takalmi ne da mayafi sai kuma mayuka da turare"
"umma kibadasu kawai ni banaso"
Daga nan tafice kofar gidan, ko gaisawa basuyi ba tace masa "gani"
Ya kalleta, "malama Nawal naji bayananki, ko menene dalilin dayasa bakya sona?"
"haka nan, haka Allah yasa"
"nima naga alamomin dakike nunamin, amma ban kawo komai arainaba, sai naayi tunanin yanayin ki ne haka, sannan ni inason ki Nawal, wallahi duk sati saina kaiwa malamai kudi sumin addu'ah akanki,
akan Allah ya tabbatar mana da alkhaairi"
"Innalillahi, Nuhu kace har wajan malamai kake kaini, to in Allah ya yarda Babu abinda zai sameni"
"ki saurareni Nawal, bawai da wata niyya naje wajan Malamai ba, nafada miki manufata"
"Nuhu, kaida kanka kace ka fahimci abinda nake nunama, kaga kenan kasan cewa bana sonka, amma shine kaqi rabuwa Dani, to daga yau nakawo karshan alaqarmu, Babu wani me tunani dazakace masa kaje wajan malamai akan wai Allah ya tabbatar mana da alkhaairi, saide in da wata manufar Nuhu "
Yace" to duk meya kawo wannan maganar ne?, kode agida ance za'a miki aure ne shiyasa kikace bakya sona?

"
" nikuwa waye zaimin aure yanzu Nuhu, nifa nafadama kawai kai dinne baka minba "
Yace" toni ina sonki, kuma bazan rabu dakeba, sannan abinda baki saniba shine Tun jiya da kikamin wannan maganar nazo nasamu Abba ya fadamin komai, Dan haka yanzu nafara zuwa wajan ki, bazan dena zuwa wajan ki ba sainaga abinda hali yayi, muzuba mugani "(
karfin hali)
Tace" Ok haka kace?

"
Yace" haka nace Nawal, inason ki bazan raabu dakeba, sannan zuwa bazan fasaba, tunda ni ina sonki ban damu daki soni ko Karki soniba, muyi tayi NI DAKE, Allah yabawa Mai rabo sa'ah, abinda nasani shine bazan taba rabuwa dakeba "
Cikin Baqin ciki tace" to insha Allahu Allah yafika "
Daga nan ta fada gida
Tana shiga daki ta dinga kuka, idanunta sukai jajir, kanta har sarawa yake, Wacce irin masifa ce wannan?

Dame zataji? da wulaqancin mk koda nacin Nuhu
Najma ce tashigo dakin taganta tana kuka, ta zauna agefenta tace" Baby kiyi hakuri, komai yayi farko zaiyi qarshe, kidinga addu'ah insha Allah zaki dace, ni kaina banji dadin hukuncin da Abba ya yanke akanki ba, amma insha Allah bazai baki Nuhu ba "
Cikin kuka tace" nagode sosai Najma "
Haka ta kasance Awannan gida har tsawon sati biyu, Abba yana hankalce da ita, yana kuma jiran takawo masa wani amma shiru kakeji, duk tunani yayi mata yawa, ta rame, idan tazauna ita kadai banda tunani Babu abinda take, haka zata zauna tana tunani inama ace ta auri mk suna Rayuwar su gida daya, koda ace baya sonta zata koya masa yanda zai sota, data tuna wulaqancin daya mata kuma sai fuskarta ta canja zuwa bacin rai, gashi bata zuwa makaranta bare tasamu tadan rage kewa, har yau ko Nas takasa bawa labari, tunda me faruwa kaam tariga Data faru, Babu wata shawara da Nas din zata sake bata ayanzu su aikata ta har afasa auren itada Nuhu, tunda abayama sun gwada wata dabarar abin bai yi musu dadi ba
*** ***** ***
Hankalinta yana kan computer dake ajiye agaban ta, idanunta sanye da medical glass, farar mace ce Mai kimanin shekaru hamsin aduniya,cikin sauri take typing a computer kai bazaakace tana kallan wani wajan daban ba, agefen ta wata matace azaune hannunta dauke da waya tana dannawa, suna mutuqar kama da juna, saide dayar bata kai me aiki a Cumputer tsawon shekaru ba
Cikin sauri yafuto hannunsa dauke da lemon steam na gwangwani, Rigace crezy ajikinsa fara me had'eda hula, duk gaban rigar atsatsage yake,
wandon jikinsa jeans me launin dark blue shima din crezy ne
Wucewa yazo yi ta Gabanta Kamar bega baquwar dake tareda ita ba
Hankalinta yana akan typing din da takeyi tace"BAFFA"
cak yadakata daga tafiyar da yakeyi
Still Hankalinta yanakan computer tasake cewa "Go and change your clothes"
Kallan kansa yayi tundaga rigar jikinsa har kan wandonsa cikin shagwaba yace"Ummi what's wrong whith wannan kayan?
Chapter 17 · 0% Book details