← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 48

Sashe 36

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ni wallahi bansaniba kuma kaga shima bai fadamin ba "
" aikuwa Tun ranar dayazo washe gari akazo akaga gidan da irin gyaran da za'ayi masa "
Dakatawa tayi da tafiya tace" to yanzu ina zamu zauna?

"
Nura yace" kede kitaho mana, gashinan angama bangaren mama, anan muke kwana, amma Babu komai aciki, kawai sai kaya da katifu, sauran kayaiyakin suna maqota "
Tace" Ok yanzu naji batu"
Suna shiga gidan Najma tataho da gudu suka rungume juna, mama mariya tace"Baby mutanan Abuja sannu da zuwa "
Tace" yauwa mama, ina wuni "
" lafiya kalau Nawal, saiki kazo kuma kika ganmu kaca kaca ana maida mana gidan namu na 'yan gayu "
Murmushi tayi kawai, tafada jikin ummah
Ummah tace" to Allah yakawo mu kuma, shikkenan ke kullum bazaki girma ba Nawal"
Tace "Ummah na dade banganki ba, ina yaya Salisu?

Yaya Sultan yaje rannan, har kaya yakawomin"
Ummah tace "to naji Baby, dagani kije kici abinci kihuta"
Najma tace"wallahi kuwa, tashi Muje "
takama hannunta suka wuce daki
Suna zuwa takawo musu abinci sukaci, Tun kafin su gama cin abincin takira Nas tace mata tazo, aikuwa nan da nan tace gatanan zuwa
Bayan sun gama cin abinci, tatashi tayi sallah
Bata dade da idar da sallah ba Nas tazo, anan suka baje kolin fira
Nas ta kalleta tace"Beauty gaskiya yanzu ne kike a Beauty, kin wani qara haske da cika, menene sirrin ne, me mk din yake baki?

"
" Hmm mezai bani kuwa banda kulawa, ko daki natafi to shima saiya bini, wani lokacin har kunyar Ummi nakeji "
Najma tace" gaskiya dole kiji kunya kam, bazaka sakeba, amma Baby dakika samu labarin shine mk wanne irin murna kikai kekuwa?

"Najma kenan, kuka nai tayi naqara godewa Allah, saina tuna lokacin danake kuka nake cewa ni bana sonsa, ke Awannan lokacin innasan mk ne har aji kaina?

Ai gyara kawai za'a fada"
Daria sukasa gaba dayansu, Nas tace"to yaya labarin makaranta?

Nasan zai barki kici gaba"
"uhm bazan d'orawa kaina ba Nas, nasan bazai barni ba, idan nace zai barni ma tona yaudari kaina"
"Amma mutum kamarsa yakamata ace yabarki kinyi karatun ki, tunda yana shiga waje dadama, sannan yahadu da mutane dayawa, kinga idan kinyi karatun ki Kema zaki goge mijinki yashiga dake ko'ina"
Tace"Nas kenan, bakisan kishin mutumin nanba, kafin yagane cewa nice matar da yakeso, watarana yajini ina waya da ummah nake cewa ni dama Nuhu na aura, wallahi Nas haka mutumin nan yasamo sabon Mai gadi maisuna Nuhu, yadinga saka shi aiki, kuma sai yazo kaina ya tsaya zakiji yace Nuhu zonan, Nuhu yi kaza, Nuhu yi kaza, Yaya Sultan dayakaimin ziyara ashe yaganmu, wallahi cikin dare ina bacci yatasoni waina fada masa inane gidansa yakaini can
kiji fa wata masifa, cikin dare wallahi "
Me Najma da Nasrin zasuyi inba daria ba, Najma tace" tab lalle kice kunashan drama agidan nan naku, Inda nice wallahi ce masa zanyi ga gidan can agaba, muyita tafiya muna zagaye gari zuwa asuba saimu koma gida
Tace" A a cemasa nayi yaya nane, shine kuma daga nan yasakko "
Nas tace" tab, a a to me wannan Baqin kishin bazai barki kiyi karatu ba, saide Inda rabo, "
Tace" hakane kam, zan fara lallabashi da zancen harya amince wataran "
Najma tace" wayaga boy, saikace wani jariri saikin lallabashi ma sannan?

Daria tayi tace "to Najma zauna nan ina zaune wata tazo ta qwacemin shi, Dan Allah idan Zan tafi kubini Muje ko sati daya ne kuyi min"
Atare suka hada baki sukace "sati?

Nas tace" bada niba, ba zanje idona ya makance ba, dade baku gane juna bane sai Muje "
Tace" haba Dan Allah, baku taba zuwa bafa, kuma nima yanzu ina gidan Ummi "
Najma tace" kema Baby kinsan Abbah bazai yardaba, ina laifin ma kwana biyu "
Tace" gaskiya a a kwana uku ko hudu"
Suma sukace saide kwana biyu, dole haka ta hakura tabarsu a kwana biyun "
*** ***** ***
"yarimah dafatan kashigo qasar"
"eh nashigo dazu mk"
"Alhamdulillah, akwai wani Yaro danake so akawoma shi, bashida hankali ne, shine nake so kakaishi Barikinku
akoya masa hankali"
"Kamar ya?

Me kake nufi?" bangane akoya masa hankali ba "
" to idan yanada hankali ai bazai taba Baby naqyaleshi ba, shiyasa nace Zan turo maka shi "
" Baby BabyBade wannan yarinyar dakake mafarkin ba?

"ka ganta ne?"
Yace"itafa Nas, naganta, kai itace ma yarinyar da Ummi ta aura min bansaniba lokacin inayi Dubai, labarin de da tsawo Nas "
" Ok to mk Babu damuwa, katuromin shi muga ko zai samu hankalin cikin yini daya"
Yace"Ok Nas,"
*** ***** ***
"yanzu Alhaji kazo ka zauna kayi tagumi baka dauki wani mataki ba ahaka kake tunanin zai sakar mana yaro?"
Hon.

Mai unguwa saleh yadaga kansa yadubeta "hajiya yaya kikeso nayi ne?

Na tabbatar akwai abinda Anwar yayiwa mk inba hakaba bazai kamashi ba, sai yau nayi DANA SANI akan turbar dana dora yaron nan, abinfa zai iya shafar siyasata"
"to yanzu Alhaji kai kana zaune, kamata yayi katashi kabi jirgi kaje ka bashi hakuri yasake shi, Alhaji karsu kasheshi ko suyi masa wani lahani"
"hajiya ba zuwanne matsala ba, kunyar hada ido nake da yaron, saboda yana ganin mutuncin kowa duk da cewa shine gaba damu"
"to yanzu Alhaji yaya za'ayi?"
"yanzu dare yayi hajiya, amma gobe Zan shirya dasafe sai naje naganshi"
Tace"to Allah yasa adace, Allah yasa ba wani abu suke masaba, kai wannan masifa dame tayi kama "
*** ***** ***
Da daddare bayan ta kwanta kasa bacci tayi, kawai tunanin sa take yi, jitake idan bataji muryar sa ba Kamar bazata iya baccinba, har wajan sha daya shiru bai kirata ba, ita kuma batada number sa, haka takira Ummi suka sake gaisawa a wayance ko Allah zaisa yana gida amma haka sukai sallama da Ummi ma batayi mata maganar saba
Haaka de tayi addu'ah ta kwanta, amma zuciyarta fal da tunanin mijinta
Shima a nasa bangaren tunanin ta yake, amma yana tareda yarimah Nasir ana gwadawa Anwar hankali, suna zaune a gefe suna fira, yayinda ihun Anwar sai tashi yake, amma ko ajikinsu
Sai wajan sha biyu saura yace "arabu dashi, shima saboda ya bashi tausayi ne yaron, duk kamarsa ta kauce, yasha wahala sai nishin azaba yake
Awajan yarimah Nasir yabarshi shikuma yayi gida, bayan ya kwanta yakira layin ta, a lokacin sha biyu da rabi, na dare, tayi bacci, saida yayi mata 7missed call amma bata jiba, haka ya kwanta cikeda damuwa
Da asuba tana idar da sallah tadauki wayarta taga kira har sau bakwai, ta duba number taga ansa muhammadu
, cikin mamaki tace "muhammadu kuma?

To waye yayi min saving number da muhammadu?

Wata zuciyar tace kode mk ne?

Kai tsaye tunanin ta yabata gaskiya, danhaka ta kirashi
Yadauka cikin Shagwaba yace" Baby nah shine kika qyaleni jiya kikai baccinki ko?

"
Murmushi tasaki, cikin ranta tace ashe shine,afili tace" lokacin daka kira nayi bacci ne wallahi, amma kayi hakuri kaji me Babban suna?

"ta qarasa maganar cikin sigar lallashi
Yace" naji, amma ki fadamin kinyi mafarkina?

"
Tace" A a banyiba, kaifa?

"
" Baby haka kawai ma ina mafarkin ki bare yanzu, ai kinsan dolene "
Tace" nima nayi mafarkin ka yau "
" da gaske?

To fadamin naki "
" nayi mafarki kana kwance aqirjina "
" wayyo Baby Allah zakisa nabiyo ki yau "
" lala lala, kazo ina?

Kayi hakuri nima fa gobe ne Zan dawo"
"to Baby duk kece ai kika rikitani, kinga gara nazo na tabbatar miki da mafarkin ki," shagwaba yafara yi Kamar ba mk din data saniba, "uhm uhm Baby nide kawai kisan yanda zakiyi Dani Allah kuwa kokuma ki Ganni"
Murmushi tayi tace"to ta yaya Zan iya yima wani abu bayan bama tare?

"
" idan muna tarema nasan bazaki iyamin komai ba, bayan rannan ma haka kika cikamin kunne da kuka, har masu aiki kike kira"
Cikin shagwaba tace"toba kaine ba"
Yace "to naji, tuba nake, nasan yanzuma kin warke, ina yan biyu nah?

" Kamar ya?

"
" Ok bakisan yan biyu ba?

"
Tace" bansani ba, suwaye yan biyu "
" toki bari idan kindawo saina nuna miki su "
" um um Dan Allah ka fadamin "
Yace" gasunan ajikinki, masu laushin nan "
Cikin sauri ta rufe idonta, tace ka kwanta kayi bacci saida safe, dif takashe wayar
Shima Murmushi yayi tareda rungume wayar ya koma bacci yana jin Kamar itace atare dashi
*** ***** ***
Zaune suke afalon baqi, su su biyu, baqar jallabiya ce ajikinsa da alama yanzu yatashi daga bacci
Yadubi Hon.

Yace" Mai unguwa naji abinda yake tafe dakai, kuma insha Allah zansa asaki danka, but bani yayiwa laifi ba, Mai dakinace, kuma batanan tayi tafiya zuwa kano, sai zuwa gobe ne akesaran dawowar ta, saide kadawo gobe kabata hakuri idan ta hakura shikkenan saika tafi dashi gida, sannan kuje kubawa iyayen ta hakuri
Hon.
Chapter 36 · 0% Book details