Sashe 37
Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yace "Babu damuwa wallahi, a hakanma mune da godia
, nagode sosai ranka ya dade, insha Allahu goben Zan dawo, shima saiya tsugunna har qasa yabata hakuri"
Mk yace"shikkenan zaka iya tafiya "
Hon yasake godia sannan yafuto daga falon yana tunanin irin wannan karfin iko na mk, bashi akaiwa laifin ba sannan ita wadda za'a bawa hakurin bata nan saida dawo, ya naji yana gani de baza'a saki yaron nasaba harsai tadawo kenan
Haka de yagama zancen zucinsa yawuce wani wajan da nufin goben zai sake dawowa
*** ***** ***
Kamar yanda suka tsara washe gari kuwa tayi shirin dawowa Abuja, wannan karon ummah da kanta tabata magungunan sanyi dakuma daka, Wanda zata dinga sha da madara, Tun awajan tahada wani tasha da kanta
Ummah ta girgiza kanta, wato yanzu dayake tanason mijin shine Tun kafin atafi akasha wani, ta kirashi awaya ta sanar dashi zataje gidan Malam suyi sallama kuma zata tahoda Najma da Nasrin, yace Babu damuwa zaisa yasir yayi musu duk abinda suke buqata
Tana zuwa gidan Malam bayan sun gama gaisawa tace masa ya temaka ya yi mata rubutu Wanda zata bawa Baffah yasha, akan Allah ya dauke hankalinsa dasaka wannan kayan, dama duk wasu sauran halaiya Wanda basu da kyau
Malam yace gaskiya wannan tunani ne Mai kyau, tana zaune yayi rubutun yabata, sannan tamai sallama tatafi
Sai wajan azahar sannan yasir yazo daukar su, saitaji Kamar kartabar gidan, amma haka sukai sallama dakowa
Kai tsaye Airport yakaisu, Najma sai baza ido take zata shiga jirgi, Yakalleta yace "basa banba, yau kuma munga ta kanmu"
Tace"wallahi kuwa, saide mutum ya dauke idonsa idan bayasan gani"
Yace"mukuwa ina zamu dauke ido, ai gara mukalli rabonmu "
Kallansa tayi kawai tareda girgiza kanta
Acikin jirgin ma haka sukai tayi, yafad'a tafad'a
Har suka sauka lafiya gidan Ummi, cikin jin dadi tataresu, tagabatar musu da abinci, yasir ya kira mk ya sanar dashi cewa sun qaraso
Basu dauki lokaci Mai yawa ba sai gashi sun shigo falon tareda yarimah Nasir, dakuma Anwar harda Hon.
Nawal tana ganinsa cikin ranta tace ikon Allah, kaga wani Kamar Anwar
Zama sukai akujerun falon mk ya nuna wa Hon.
Nawal yace, "Mai unguwa ga wadda yayiwa laifin nan yaje yanemi yafiyarta"
Tun kafin Hon yayi magana sai ganin Anwar sukai agaban Nawal yana bata hakuri
Ummi dake gefe tace "A a wannan ba shine yaron daya jefar miki da waya a school ba?"
Cikin sauri yace "nine, nine wallahi
Kuma insha Allah nayi alqawarin Mai kama da itama bazan qara kallah ba"
Itama Nawal din Murmushi tayi, tasan cewa gaskiya jikin Anwar yayi la'asar
tace"babu komai na hakura "
Mk yace" to shikkenan Mai unguwa, zaku iya tafiya, but kada kamanta de kaje dashi har gida kubawa iyayen ta hakuri, shi yaron naka yasan laifukan daya aikata mata "
Hon yace" angama yallabai, insha Allah ba zamuje gida bama sai munje munbasu hakuri "
Daga nan yace zasu iya tafiya
Suna fita, yaja yasir da yarimah Nasir part dinsa nada, ya cewa Ummi abawa sabira abinci takai musu
*** ***** ***
Abba da Malam suna tsaye a kofar gida, suna ganin yanda ayyukan ginin suke gudana, Salisu yafuto daga gida zai wuce kasuwa, kawai sai ganin wata Babbar Mota sukai tatsaya agaban gidan, gaba daya su ukun mamaki yakamasu waye yazo kuma?
Kokuma baqi sukai?
Basu gama wannan tunanin ba, Hon yabude Mota yafuto, shima Anwar yafuto, fuska duk ta kumbura saboda duka
Gaban Hon yafadi, ganin mutanan daya ciwa mutunci kwanaki yau gashi yazo neman yafiya wajansu
Suma mamaki ne yaqara kamasu, Mai yakawo Mai unguwa saleh dogo gidansu?
Sharhi
Comments
Share
Dan Allah
Mrs Usman ce
[2/13, 3:14 PM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
43&44
Ummi ta kalli Nawal tace "Amma Nawal sainaga Kamar kinsakewa yaron dayawa, bai cancanci ace lokaci daya kinyafe masaba, mutumin daya nemi ya lalata miki idanu"
Murmushi tayi Mai kama yaqe tace "Ummi menene Rayuwar ma gaba dayan ta, yau idan mune gobe bamu bane"
Ummi tace"wannan hakane, amma sanyin halin ki yayi yawa Nawal, sukuma maza ba'a yi musu haka, idan yayi miki abu yau yaga kinyi shiru gobe ma yaga kinyi shiru to jibi abinda yafi haka zaiyi miki, duk da nina haifi Baffah Nawal bana baki shawarar kiyi masa wannan hakurin, hakuri idan yayi yawa akwai cutarwa aciki,irin haka anayiwa mutum abu yana shanyewa wataran bazai iya shanyewa ba saide yafadi daga nan kuma ace mutum yanada wani ciwon Kamar hawan jini "
Tace" hakane Ummi, insha Allah Zan gyara "
" A a Nawal nasan ba de nawa zakiyi ba, tashi kije kikai wa mijinki a abinci "
Tace" to"
Tareda dayin kitchen
*** ***** ***
Hon.
Mai unguwa ya kalli d'ansa, shima Anwar din ya kalleshi nan take kowa yagane laifin daya aikata shi Hon.yana ganin su yagane cewa sune mutanan da sukaje wajansa yayi musu korar kare
Shikuwa Anwar tunanin irin cin mutuncin daya yiwa Nawal yayi, Inda wata yarinyar cefa bazata yarda ba saita rama
Kawai daga mari ya qullaceta aransa saiyi mata abubuwa yake Kamar wata namiji, akan namiji dan'uwansa yakamata ace yayi haka bawai akan mace ba
Yafesa mata shaltos, yabigeta da niyya, ya take mata waya, sannan yanzu haka kawai batare datayi masa magana ba ya tsokaneta da niyya, kuma ko uffan bata ce masaba, lalle idan bai nemi yafiyar iyayen ta da ita kanta ba haqiqa Allah bazai Barshi ba
Hon.
Mai unguwa yace "ina tunanin wannan shine mai gidan, mu qarasa"
Suna Qarasawa Abba yabata fuska
Salisu kuwa fuska yayi yakawar dakai gefe
Liman ne kawai yayi Murmushi yace "barkanku dazuwa"
Cikin kuskurin kunya Hon.
Yace "yawwa sannu baba
, nan ne gidan muhammadu lawan ko?"
Liman yace "eh nan ne," yanuna masa Abba tareda cewa "gashi ma a tsaye, Mai yake tafe daku??"
Cikin sauri Anwar yace "neman yafiya"
Abba bai saki Fuskarsa ba yace"kuje munyafe "
Malam yace" A a haba muhammadu, baqonka annabinka inji bahaushe, "ya kalli Salisu yace" shiga gida ka dauki musu abin zama "
Salisu baice komaiba yajuya yashiga gida sai gashi ya dawo da Babbar tabarma
Anan kofar gidan suka shimfida musu kowa Yazauna
Mai unguwa ya gaida Malam da kansa, sannan ya gaida Abba
Bayan sun gaisa ya kalli Anwar yace" basu hakuri "
Cikin ladabi dakuma tsantsar nadama yace"dan Allah baba kuyi hakuri, nazo har gida inaso ku yafemin akan abinda na yiwa Nawal, haqiqa nasan cewa na cutar da ita, amma nabata hakuri kuma tace tayafemin, sannan kuma ina qara baku hakuri bisa abubuwan dasuka faru "
Sai a lokacin Abba yasaki ransa" Babu komai tunda itama da kayiwa laifi tace ta yafema ai shikkenan "
Mai unguwa ya kalli Malam yace" baba Dan Allah nima ina qara baku hakura bisa abinda na aikata muku lokacin dakukaje gidana, nafiso shi yaron daya aikata laifin yafara neman yafiyarku sannan ni, domin kusan cewa lalle yasan ya yi laifi kuma yazo yabaku hakuri, Dan Allah naroqeku nima ku yafemin, bansan cewa yarinyar da Anwar ya aikata wa wannan abun matar uban gidana bace, da ko hanyar databi ma Anwar bai isa yabiba
Amma munje har can Abuja suma sun tabbatar mana komai yawuce, sannan daga can ko gida bamujeba muka iyo nan "
Malam yace" Babu komai ai, dama koya zuba mata shaltos ko bai zuba mata ba dole Allah ya rubuta zata makance na Dan wani lokaci, ta wata silar daban, Dan haka muma munyafe muku, Allah yashiryeshi yakiyaye gaba "
Mai unguwa yasake duqar da kansa Kamar ba honorable Mai cikakkiyar izza ba yaqara yimisu godia sannan suka tashi zasu tafi, yadubi Abba yace" insha Allahu saqona yana nan zuwa gareku, idan kunyi waya dasu mutanan Abujan ace ina gaishe su
Abba yace "A a bama buqatar komai, kuje kawai"
Suna tafiya Malam yace "wannan shi ake kira gaba da Gabanta, kagade yanda mukaje har gidansa ya wulakanta mu, Inda ya sauraremu a lokacin aida baizo yanzu yana qaramar murya ba"
Salisu yace"Malam kaji wai harda cewa idan anyi waya da mutanan Abuja agaishesu, soyake yacefa idan anyi waya da mk a gaishe shi, Dan yasan sunzo har gida sunbada hakuri"
Abba yace"emana, siyasarsa yake so yakare kawai"
Malam tace "yanzu ai gashinan dole tasa d'annasa yasan darajar mutane, koma me sukayi masa a abujan bazai dameniba, ko banza anqara koyawa dansa tarbiya dakuma sanin haqqin d'an adam"
Haka sukai ta mamakin wannan al'amari, Wato kudi da iko sunyi a rayuwa, idan kana dasu bakada damuwa ta wani fannin, inba kudi da iko ba waya isa yasa Hon Mai unguwa saleh dogo yazo har qarqashin talakawansa da sunan neman yafiya?
*** ***** ***
Abincin ta tsaya tahada shi yanda ya kamata, sai farin ciki take wannan ne karo na farko da zata zubawa mk abinci yaci da sunan sunason junansu
Dauka tayi ta nufi part dinsa da Abincin, Tun kafin ta qarasa take jiyo,tashin surutunsu suna zancen ball
Ahankali ta tura kofar falon ta shiga, duk suka juyo suka kalli kofar, yana ganinta yahad'e rai Kamar yanda suke ada can
Mamaki yakamata, amma saita share tayi musu sallama tareda ajiye Abincin, cikin Murmushi tace "toga abinci," tafara kokarin zuba musu
Nas yace"gaskiya ne kin kyauta, yau zamuci Abincin amarya, dama tunda akai bikin ayyuka basu barmu munzo ba "
Shide mk yana zaune baice da ita uffan ba, sai wani qara had'e rai yake
Murmushi tasake yi tafara zuba Abincin a plate, tsintar muryar sa tayi yace" Barshi, jeki kawai "
Cikin mamaki ta kalleshi, jikinta yayi sanyi, tace" kace kanason abinci "
" cewa nayi sabirah ta kawomin a binci, ki tashi kije kawai"
Tasake kallansa Babu damar tambaya, saboda yana magana sai bata rai yake yana qunci
Tatashi tsam, tafuto daga falon batare data qara cewa komai ba
Tana fita, Yarimah ya dubeshi yace"menene abin bacin rai Dan zata zuba mana abinci?