← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 48

Sashe 28

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin sauri yace "Yas" ya Dakatar dashi
Sannan yaci gaba da cewa "sunanta BABY, yarinya ce qarama, tana saka wannan Baqin abun a fuskarta, inaso ka tattaromin baya nanta cikin one week"
Yana gama magana yakashe wayar, sannan yafara tunanin ina ita kuma wannan yarinyar tayi?

My fan's kuyi manage da wannan, da ace Babu posting aganina gara asamu ko kadanne
Dan Allah masu labe kufuto kuyi sharhi pls
Amnah El Yaqoub
[2/6, 10:44 PM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
31&32
Yaci gaba da tunanin
To yanzu idan bataje gidan Ummi ba gidan uwar wa zata tafi?

To kode gidan tatafi da gaske?
, gata yarinya ce shi yaro baya qarya tsaf zataje ta zayyanewa iyayen ta komai tace yace saiya nemeta, sukuma su zagi Ummi suce Tun aure baije ko'inaba har ansamu matsala
Shikuma Ummi tasakoshi agaba
To yaya zaiyi tunda liman yace yakamu dason matarsa
dole hakuri zaiyi ya rungumi qaddara, inyaso saiya hadata da Babyn, amma ba haka yasoba, domin kuwa bai tsarawa kansa cewa zai hada Babynsa da wataba
Tsam yatashi ya yi daki ya kwanta, yana tunanin yanda zai shawo kan lamarin zuwa gobe
*** ***** ***
Washe gari dasafe tsaf ya shirya cikin qananun kaya, riga green wadda ta kamashi saiya dora milk din suit asama, saikuma wando jeans
Kai tsaye gidan Ummi yanufa, a lokacin tana zaune afalo tana break fast ita kadai
Kusa da ita yaje ya zauna jikinsa yana gogar nata, Yace"Ummi walijam "(ina kwana)
Ahankali ta ajiye cup din dake hannunta, tashafa kansa tace" sejam kalau Baffah nah, where is your wife?

"
Gabansa ne yafadi, kansa yasara, da gasken de bata nan din kenan, hannunsa yasa yadafe kansa
yace" Ummi wai yarinyar nan batazo nan gidan ba kenan?

"
Yi tayi Kamar batasan komai ba tace" tacema zatazo ne?

"
" no bata fadamin ba, Ummi yarinyar ce batajin magana wallahi, laifi tayimin shine nace tatafi gida saina nemeta "
Ummi tace" ikon Allah, to kaga kenan kai da kanka kabawa kanka amsa, tunda cewa kayi tatafi gida, may be tatafi gidan ne, "
Cikin shagwaba yace" to Ummi meyasa ba zatazo nanba saita kama hanya taje ta shiga wata motar tana hada jikinta dana wani"
"ikon Allah, Baffah nanfa ba gidansu bane, tayaya miji zai sallami yarinya ita kuma takama hanya tatafi gidansu?"
"to Ummi ba 'yarki ceba, zata iya zuwa mana"
Ummi tace"to batazo ba, da menene yahadaku har abin yakai haka?

"
" Ummi yarinyar nan takama kayana ta qonesu duka, batasan kudin dana kashe akan kayanba, takama ta babbakesu,
sannan naayi mata magana waini yarinyar nan zata kalli tsabar idona tace Dani BAFFAH "
" to menene aciki danta qona kayan?

Ka fadamin sau nawa ina karbe irin wannan kayan awajan ka amma kabada oder wasu?

Kaga yanzu ma kanada right din dazaka sake wasu, may be tunanin ta bazai iya daukar ganin mijinta kullum yana yawo ana kalle mata jikinsa ba, shiyasa ta qona
Sannan yarinyar nan tunda akai aure baka zaunar da ita kafada mata cewa bakasan a kiraka da Baffah ba, kamata yayi Tun farko kafada mata cewa ni sunana Muhammad, Ummi na tana kirana da Baffah, amma gayu yasa namaida sunana zuwa MK
Saboda haaka kaga ni anan ma banga laifin yarinya ba, Dan tace Baffah, koda cewa tayi me sunan baban Ummi,
ba zanga laifin ta ba
Baffah ka kiyayi kanka da Rayuwar nan, ada de nasanka da tausayi amma zuwa yanzu nasan cewa d'ana ya sauya, ya koma marar tausayi, Baffah ina sane da cewa Babu abinda yashiga tsakanin ka da yarinyar nan na auratayya, idan kai bakada lafiya ita yarinyar haka take?

Shiru yayi Kamar ruwa ya shanyeshi
Kuna zaune gida daya bazaka saukewa yarinya haqqinta ba?

To yanzu ai shik
kenan komai yazo qarshe, tunda ka sallameta zuwa gida kaga ai saitaji dadin auren wani, tunda batada iddar kowa akanta, yamaka kyau "
Ahankali yace" Ummi kiyi hakuri, nima bayin kaina bane, amma insha Allah zangyara, za'a bata haqqinta "
Tace" zancen yaushe kuma?ai magana ta qare "
" kiyi hakuri Ummi, yanzu ni zanje saudia, akwai binciken danasa yasir yayi min, inaso nayi addu'ah akan Allah yasa adace, ita kuma nasan zata dawo ai"
Ummi ta kalleshi galala
sannan tace"shi aikin har yakai ka tsaya ka nemi matarka muhinmanci?

"
" Ummi nace miki zata dawo "
Tace" to shikkenan, tunda batada zuciya Allah yadawo da ita lafiya "
Shima Babu kunya yace " Amin "
Sannan yaja abincin datakeci Gabansa shima yaci kadan, yamiqe yace" Ummi nina tafi, sai zuwa jibi Zan dawo insha Allah "
Ummi tanata kallan wannan qarfin hali irinna Baffah tace" Baffah tonyi jata?

"(ina zaka)
Yajuyo yace" Ummi nace miki saudia Zani, addu'ah ce zata kaini inaso nayiwa abin d'awafi "
Tace" to, Allah ya temaka "shima yace amin, sannan yafice
*** ***** ***
Washe gari bayan ta tabbatar Baffah baya garin, ta tura sabira itada driver sukaje gidan suka daukowa Nawal wasu daga cikin kayanta, da wayarta, Ummi ta karbi wayar takasheta, sannan ta kaiwa Nawal kayanta daki, jikinta harya qara kyau saboda babu abinda take, kullum tana daki, fatarta har wani sheqi take, wani lokacin nede take taya Ummi cike wasu takardun, dataimakon Ummi, haka abubuwa 'yan qanana saita dinga koya mata tana rage mata su
Bayan tabata kayan tasa sabira ta gyara mata wani daki kusa da ita tace takoma can da zama, idan takama dole Ummin zata shigo da kanta, sannan tabata wayarta tace gatanan amma kada ta kunnanta, domin kuwa ta hanyar wayar kadai ma Baffah zai iya bibiya yasan Inda take
Abangaren Baffah kuwa
Tunda yaje saudia kullum yana masallaci yana addu'ah Allah yasa aikin daya bawa yasir adace
Allah ya bayyana masa Baby cikin gaggawarsa bata shaidan ba, idan kuma Allah yasa tayi aure, kokuma anrasata to Allah yacire masa sonta daga zuciyarsa yasaka masa son matarsa sosai, domin samun kwanciyar hankalinsu
Sosai ya tsaya yayi addu'ah, sannan yafara haramar dawowa gida
Ummi kuwa sabira ta aika wajan wata aminiyarta datake oder kayan mata daga Sudan, aka hado mata magunguna masu inganci dakyau, babu kunya take zaunar da Nawal adaki ta gwada mata yanda zatayi amfani dasu, idan kuma nasha ne da kanta take hada mata tabata tasha, tunda Nawal najin nauyi harta saba
Banda lokaci data ware take koya mata kissa iri iri da kalamai masu dadi duk najan hankalin Baffah
Lokaci kadan kuwa taqara sauyawa, abubuwa suka qara yawa, baccin ta takesha idan Ummi bata nan tana wajan aiki, babu ruwanta da gyaran gida karfe bakwai
, sabira tanayin komai.
*** ***** ***
Washe gari yadawo, kai tsaye gidansa yasauka, amma abinda ya bashi mamaki shine baiga Nawal tadawo ba
Babu abinda yadauka agidan kai tsaye yawuce gidan Ummi
Ummi tana ganinsa tace"oyoyo da mutanan saudia, ashe kadawo?

"
Zama yayi agefen ta yace" Ummi nadawo yanzu "
Tace" to mutanan saudia maraba,
yanaganka haka?ina tsarabar tamu?

"
Cikin ransa yace ita Ummi baabu ruwanta Tambayar tsaraba ma take
afili yace" Ummi wacce tsaraba nida naje addu'ah "
Tace" ai jinake kataho min da zam zam insha inyi alwala in yi sallah akan Allah ya baiyana min yata Nawal "
Cikin sauri ya kalleta yace" Ummi wai kina nufin bata dawo ba?

"
" bata dawoba Baffah, sannan nakira wayarta akashe, may be lokacin daka koreta da wayarta tatafi, ni tsoronama kada iyayenta suzo sucimin mutunci
Kansa yadafe da hannu
yace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Ummi yanzu yaya za'ayi?

"
" abinda za'ayi shine ka shirya kaje kabawa iyayenta hakuri kadawo da ita gida, Dan nikam bazan iya tunkararsu da wannan maganar ba, ido da kunya
Yace" to Ummi nida a wanne garin takene taka maimai?

Ummi tace"Lahaula wala quwat, yanzu Baffah dama tunda akai auren nan baka shirya muku tafiya kunje gidan iyayen yarinyar nanba?

"
Sumar kansa ya shafa, yayi shiru
Taci gaba da cewa" Amma kuwa Baffah wannan abun kunya da yawa yake, to idan kaje gidan me zakace musu?

Shiru yayi, daqyar dai yace"Ummi ba dad'i tone tone "
Tace" Baffah ai dole na tona
, kana zaune da mace bakasanma inane garin su ba "
Yace" kiyi hakuri, ki fadamin sai naje nabasu hakuri tadawo d'akinta
" to Baffah tunda ka dage 'yar kano ce, zanturoma adress din gidansu saika shirya kaje "
Saida tafadi haka yatuna da maganar Nawal datake cemasa yayanta gidansa yana kano, yace" to Ummi nagode, zan shirya gobe da safe naje, saboda yanzu nagaji "
Tace" kai kadai zakaje ne ko tareda gurds?

"
" nikadai zanje, zanbi flight din dazai fara tashi insha Allah "
Tace"to Allah yakaimu, idan kaje kabasu hakuri sosai Dan Allah"
Shiru yayi mata baice da ita komai ba
*** ***** ***
Washe gari karfe tara agidan Ummi tayi masa, a lokacin itama tafuto tsaf zata tafi wajan aiki
Zuba masa ido kawai tayi tana kallansa ganin yanda yayi wata irin masifar yin kyau, yadi yasa Mai mutuqar tsaida light blue, yasaka hula baqa da Baqin takalmi, sai Agogon sa qirar gucci shima baqi , sai gyara Babbar riga yake
Ummi tace "Baffah?

Yaushe rabonka dasaka irin wannan kayan kuwa?

Anya kuwa kaga kanka a madubi kaga sai yanda kayi kyau?
Chapter 28 · 0% Book details