← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 48

Sashe 45

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace "A a Muje, tunda muka zo banga ko'inaba"
Cikin rad'a yace "pls Baby"
Tace"kabari mudawo"
"kinyi alqawari?"
Tace "nayi"
"kindeyi alqawari"
Tace"me Babban suna nayi "
Daga nan yatashi aka gama shirin, sannan suka fita yawo, waje waje sukaje yadinga nuna mata, tana manne ajikinsa, wajan daya birgeta su tsaya suyi photo
Kowa ya gansu saisun birgeshi
('yar'uwa Karki yarda ki raba daki keda mijinki, koda ace kinada kaya dayawa kwaso wasu kidawo nasa dakin, koda fada kukai tunda kuna daki daya hakan zaisa dolen dole mijinki yamiki magana idan yanemi wani abun yarasa, amma kika bari kowa yana nasa dakin Hmm i pity you sister
wallahi saide kiji tashin motar sa wataran
*** ***** ***
Tun bayan wayar dasukai da ita yarasa sukuni, karfa yaje da gaske take bata son nasa
Toda yaya zaiyi kenan?

Kai yasan ma wasa take kawai Dan yaji haushi ne yasa tafadi haka, meyasa ita bata sonsa bayan yanmata dayawa suna sonsa?

Sannan meyasa yake gani a idonta cewa shidin baya birgeta?

Yanzu yaya zaiyi?

Kada yaje yasamu Mai martaba da magana aje gidansu tafuto fili tace bata sonsa
daga nan kuma shknn mutuncinsa zai ragu a idon mutanan masarautar su, ace yatura mutane a Inda yasan cewa ba'ayi dasu
Gara yaje ya nemeta suyi magana gaba da gaba, yasan a hakibar dayake ciki, duk da zuciyarsa tana zargin cewa Nasrin batada Wanda takeso, kawai tafada ne
Dan haka cikin sauri ya kira mk yayi masa bayanin halin da ake ciki, sannan shima yaqara bashi hakuri tareda fatan alkhaairi
Number yasir ya nema ya kirashi, yace ya temaka yaturo ya bincika masa adress din gidansu Nasrin yaturo masa
Shikuwa yasir gidan bincike
nan da nan yasamu daga wajan Najma yatura masa komai
*** ***** ***
Kamar wani Wanda take da tabbacin zai sota tanarke masa tana magana tanata shagwaba, tace"kuma yanzu idan katafi yaushe zaka dawo kafara aiki?

"
Saida yadan daga kafada sannan yace" eto may be this week insha Allah "
Tace" ka tabbatar zaka dawo?

"
Kallanta yanayin datayi masa maganar yayi, yarasa meyake damun yarinyar nan tunda yazo company take ta shige masa
Allah yasa de ba abinda yake tunani bane
Ajiyar zuciya yasaki yace" insha Allah Zan dawo "
Tace" to shknn, sai munyi waya, zan kiraka idan kaje, sannan kacewa su mamanku wata qawarka tana gaisheta "
Yace" gimbiya de, gimbiya aita wuce qawata, saide nace gimbiya Sahla tana gaisheta "
Murmushi tayi tace" kaga ni Babu wata gimbiya, ka daukeni Kamar kowa "
Yace" to shknn, sai wani lokacin "
Itama tace" toba damuwa saina kira "
Daga nan takoma cikin Company shikuma yafuto
*** ***** ***
Tunda yasako hancin motar sa layin gidan da aka tabbatar masa da cewa shine nasu Nasrin yake hango wata yarinya a tsaye da wani a kofar gida gabansa yayanke yafadi
Ahankali yake tuqa motar har yaqaraso kusa dasu, shikam yana ganin su amma su basa ganinsa kasancewar glass din motar me duhu ne
Magana yafara yi shi kadai, tabbas wannan yarinyar itace a tsaye da wani, kenan da gaske take da tace akwai wanda takeso, tayaya ma zata kulani bayan tana sauraron wannan gayen?

Babu abinda Zan fada masa, dole ma nasan yanda zanyi nashawo kan yarinyar nan taqarfi da yaji Dan inba hakaba saide naga ankawo min IV nabikinsu
Handle din motar yakama zai futo saikuma yafasa, yajirasu suka gama firarsu da yaya Sultan, har sukai sallama akan idonsa
Sultan yazo ya wuce tagaban motar amma baima kalli motar ba
Shikuwa yarimah yana wucewar Sultan yayi sauri yabude motar yafuto yadoru a bayanta
Dab da zata shiga ya cinmata sai ganin mutum tayi agabanta
Yaune karo na farko data taba ganinsa cikin kaki na soja
Matsawa tayi zata wuce cikin gida yasake shan Gabanta tareda kama hannunta yariqe, Baice da ita komai ba yazuba gwiwoyinsa biyu aqasa yace "please Nas Dan Allah ki daure ki aure ni"
(tab ! yau maza sun ragargazo
Abinnan na kullum de
ai kun gane
Amnah
[2/21, 10:51 AM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
53&54
Hannun ta taqwace tace"kasakarmin hannu na, nadade da fadama gaskiya "
Hannunta yasaki yayi shiru, sannan yamiqe tsaye ya kad'e jikinsa
Yakalleta yace" waike me kike dauki kanki ne?

Kinsan waye ni?

Kinsan girma da martabar danake dashi?

Bana tsugunnawa saide a tsugunna min akwashi gaisuwa, nazo gabanki na tsugunna inaso ki aure ni, cemiki akai banda masu sonane kome?

Ba komai yasa namiki hakaba saidan nafita haqqinki,"
Yanunata da hannu
sannan yace" ki kiyayeni "
Haushi ne yaqara kama Nasrin, lalle ma mutumin nan,
ashe tuban muzuru yayi
ta kalleshi tace"
To tunda kanada Wanda suke sonka menene zaka tsaya a wajena?

Ai saika kai kanka can "
Yace" Ok haka kikace?

"
Tace" eh, kaje wajansu, amma ba wajena ba "
Shima cikin bacin rai yace" aikuwa wajan ki zanzo, kuma aure dole yarinya "
Yana fadar haka ya barta a tsaye awajan,tareda shigewa cikin Mota
Kallan bayan motar sa tayi, tasaki Tsaki sannan tashige cikin gida, Allah da taso tausaya masa, amma tunda taji yace akwai masu sonsa sai taji ranta ya sosu akan wannan furucin nasa, to wai ma miye nata najin haushi akan yace ana sonsa?

Yana driving amma kawai Tsaki yake saki, yayi tattaki yataho tundaga Abuja har kano saboda yarinyar nan amma ko Ruwan nera biyar bai samu ba bare yasamu abinda yakawo shi wajan ta
Qarshe ma duk bada kan dayayi duk yatashi abanza
Wayarsa yadauka ya kira mk, a lokacin yana office yana tsaka da aiki, yadauki kiran
Yarimah yace" mk naje wajan yarinyar nanfa amma Babu nasara
Kai intaqaice ma bayani ma da wani Yaro naganta, sannan har tsugunnawa nayi agaban ta amma ta watsa min qasa a ido "
" to meyasa bazaka nuna mata a aikace ba "?cewar mk
Yarimah yace" MK wannan yarinyar fa ba Kamar sauran yanmatan dana hadu dasu bane, dana riqe hannun tama qwacewa tayi "
" to meyasa bazaka jata kushiga cikin gidan kayi musu bayani ba?

"
Zaro ido yayi, yace" A a mk kafini iko
, saikace wata baiwa ta?

"
Mk yace" to shikkenan Nas ka zauna kallan ruwa...

Shima dayan saurayin nata bari na kirashi ince ya matsa number"
Cikin mamaki yace "kasan shine?"
"yes yayan Baby nane"
Yarimah yace"tab, akwai qura, dannaga gayen yahadu gaskiya, zansan abinyi yau d'innan insha Allah "
Mk yace" ok" tareda kashe wayar
(wai nikam mk abayan wa kake ne
*** ***** ***
Ummi ta dubesu tace "haba Alhaji, kuma yanzu fisabilillah saboda wannan kuka taso tundaga kano?

Aini da kun fadamin ma bazakuzo ko'inaba"
Abba yace"haba Hajiya ai yaba kyauta tukwici, yaro yayi abin alkhaairi dayawa Babu abinda zamuce daku sai godia, ta silarsa Nawal tasamu lafiya, ga gyaran gida, ga kuma aiki daya samawa yara, kinga ai dole muzo muyi muku godia "
Murmushi tayi" ai Alhaji Allah yakamata ku godewa, kuma mu dama iyaye a kullum addu'ar mu shine Allah yabamu yaya nagari, mace ko namiji inde nagari ne ai sun zama abin so ga kowa, Allah zaku qara godewa daya baku Nawal amatsayin 'ya, domin kuwa taa Sanadin ta ne komai yafaru "
Yace" wannan gaskiya ne, ai shima muhammadun mun kirashi zaamu sake yimasa godia amma kuma bai daukaba "
Ummi tayi Murmushi tace" to ai gara dabai daukaba Alhaji, ai anzama daya, shi Salisu yana tare da Yasir ko?

"
Abba yace" eh shi Salisu tareda Yasir zasu dinga yin komai, shikuma Sultan yana nan "
Tace" eh haka yake fadamin da mukai waya, Allah ya temaka yayi jagora "
Liman dayayi shiru yace" yanzu hajiya ashe ke iyalin Alhaji Kabeer ce amma kika kasa sanar damu lokacin dakikaje gida "?

Tace" to baba ai gara kar a bayyana din, Inda ace nafada muku aida saboda mahaifinsa zaisa kubashi yarinyar, amma yanzu da aka baiyana gaskiyar komai ai gashi ba'aji kunya ba daga baya "
Malam yace" wannan gaskiya ne, Allah yabawa yara zaman lafiya, ya basu zuri'ah tagari "
Cikin farin ciki Ummi tace" Amin amin Malam "
*** ***** ***
Washe gari jiniya da kuma qaran sarewa yacika unguwar su Nasrin
Mutane dayawa suka futo domin ganin abinda yake faruwa
Motoci ne kusan guda shida manya masu tsadar gaske
Wata farar Mota aka budewa wani mutum dattijo yafuto sai kirari ake masa, sai baza binjima suke ana gyara kintsi dakyau
Iso sukasa ayi musu, yaron dayayi musu jagora zuwa gidan da kansa yaleqa yafara kwala sallama
Baba mahaifin Nasrin yafuto, yana ganin wannan manyan baqi fuskarsa tacika da mamaki yaqaraso yana sannunku da zuwa, barkanku da zuwa
Nan da nan yagabatar musu da abin zama, babu bata lokaci wannan dattijon yafara magana "sunana Alhaji Ahmad Is'haq, wazirin qasar gombe, munzo neman iri ne wannan gidan, yarimah yagani kuma yanaso, dan haka Mai martaba yabamu dama muzo munewa yarimah auren yarka,"
Baba yace " wallahi anbashi
, nide a iya sanina yarinya batada kowa, a fadawa Mai martaba ahakan ma mune da godia "
Waziri yayi qasa da murya yayiwa wani dake gefensa magana, nan take aka dauko kudi dami biyu
sannan wasu fadawa guda biyu suka tashi da gudu suka bude bayan Mota aka futo da akwatuna guda biyar aka jeresu agaban baba
Waziri yadubi baba yatura masa damin kudin gabansa yace"ga kudi da akwatuna nan amatsayin kayan nagani inaso, sannan Mai martaba yana jiran amsar ka ta lokacin da kakeso azo ayi aure "
Baba yace" afada masa yarinya anriga anbashi, duk lokacin da fada ta shirya za'a iya daurawa "
Wazirin yace" masha Allah, Allah yayi maka albarka, masarautar gombe tana godia, daga yau za'a hana yarinya fita ko'ina, akwai bayi da za'a turo mata su fara kula da ita kafin zuwan ranar da masarautar gombe zatazo tatafi da ita "
Baba yace" Allah yakaimu, Allah yaja da ran sarki"
Daga nan suka tashi suna daga Babbar riga har saida Waziri yashiga Mota sannan suma suka shiga suka tafi
Wajan biyar saura tadawo daga makaranta, tunda tashigo layin su taga sai Kallanta ake
Gabanta yafara faduwa kadan
Tana shiga gida taci karo da akwatuna atsakar gida
Babanta ya kirata daki yayi mata bayanin komai tace"Baba yarimah kuma?
Chapter 45 · 0% Book details