← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 48

Sashe 7

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dan sandan ya kalleshi yace "Alhaji, naji Kamar sunan Wanda kafada mana kace mai unguwa"
Abba yace "eh _honorable_ Mai unguwa saleh dogo nake nufi"
"ayanda muka shigar kace yaronsa ne ya yiwa yarinyar ka laifi, shine kakeso kotu tabima haqqinka, shin Dan Allah baba Zan iya sanin takamaimai abinda yake faruwa?"
Abba yadubeshi yakwashe komai yafada masa
Dan sandan ya girgiza kansa sannan yadubi Abba "Alhaji azahirance wannan _civil case_ ne, _case_ ne tsakanin kaida shi, tunda _issue_ ne akan 'ya'yanku, kanada damar dazaka kaishi kowace irin kotu, daga nan har kotun qoli, to amma abinji shine, zai dauki lauya kaima ka dauka, shifa Babban mutum ne, Dan majalissa, ayanda ka fadamin yanzu kace asbiti suna buqatar million daya da dubu dari da sittin, toshifa mutumin nan yanada linkin wannan kudin, cire wannan kudin acikin asusun bankinsa ba komai bane, kukuwafa baba?

Yanzu haka nasan cewa fafutukar yanda za'ai kusamu wannan kudin kukeyi, yayinda yadauki lauya kuka dauki lauya zai sakar musu kudi ne qarshe shari'ar tatafi awofi, kai inma ba'a juya maganar takoma kan 'yarku ba, ace itace take zuwa har Gida nemansa shikuma ya aikata mata haka, waya daya zasuyi wannan _case_ din yatashi daga _civil case_ yakoma _criminal, case_ din yakoma tsakaninka kaida gwamnati, yan siyasa abin tsoro ne a yanzu Alhaji, yayinda suke nema awajan ka zasu isheka da dadin bakine, amma idan suka samu to zance fa yariga daya wuce, akan maganar kotun nan suna kwance agida zasusa aje har asbiti a lalatawa yarka rayuwa, inma bata mutu ba, shikkenan daga nan _case_ yaqare, ni aganina kuyi hakuri Alhaji, _honorable_ Mai unguwa saleh dogo, baqaramin azzalumi bane, kubarshi da Allah kawai, saboda in kunje kotu ma, kotun tasuce, amma idan baku yardaba, shikkenan, nima kaina me shige muku gabane akan tura _case_ din kotu "
Malam yayi ajiyar zuciya,yace" cuta kam angama cutarmu, haqiqa honorable ya zaluncemu, amma babu komai, munjanye wannan maganar, Allah yanaji, kuma yana gani "
Shima Dan sandan yace" toshknn baba, Allah yashiga tsakanin na gari da mugu "
Suka amsa masa da amin, daga nan suka wuce Gida batare dasun waiwayi asbitin ba
*** *** ***
*Washe gari*
Najma kiramin Besty na a wayarki, Tun shekaran jiya rabona da ita, banji muryar taba
Najma tace "to ai kema Ga wayar taki nan, jiya su nura sun kawo miki ita, nakunnata ma naga sunmiki charge saina kashe ta"
"to kunnamin kikiramin ita"
Najma na kunna wayar ta kalli yar'uwar tata "Baby akwai _pattern_ fa, yaza'ayi?"
Hannunta ta meqo "bani nazana kozan iya, aibashida wahala"
Najma tabata wayar, tazana baiyi ba, tasake zanawa _still_ baiyiba, tasake yi akaro na uku shima Najma tace baiyiba, daga qarshe de meqa mata wayar tayi, tace zanamin 'N', harafin sunana ne akai
Najma na zanawa yayi, ta shiga wayar takira mata qawarta Nasrin, hannunta takama tasaka mata wayar tace to gashinan tashiga
Nasrin nadauka tace "Beauty nayi fishi, Tun rannan nake kiranki wayarki akashe, bayan kuma nafada miki Zan kiraki, kinsanfa inbanji muryarki ba, babu zaman lafiya
ta qarasa zancen nata cikin sigar zolaya"
Wani qulltun baqin ciki ne yatokare mata maqoshi, idanunta suka cika da qwallah tace "Allah sarki Nas kiyi hakuri, kekam kinada damar ma dazaki Ganni" ta qarasa maganar cikin rawar murya
Nasrin tace "kekike nufi Nawal?

Zaiyi wahala takirata da Nawal, saide in maganar dazata mata Mai muhinmanci ce, kawai Beauty take cemata Tun lokacin dasuka fara haduwa
Taci gaba da fadin, meyasa naji muryarki Kamar tana rawa?

Kokun tashi daga kano ne?"
"idan tashi ne aida dadi Nas, bana gani Nas, idanuna sun sami matsala bazan sake ganinku ba, tana fadar haka ta rushe da kuka
Najma ta fizge wayar takama yimata fada, sannan tasa wayar akunne tace "Nasrin, Baby batada lafiya, yanzu hakama muna asbiti, wallahi wanine ya saka mata shaltos a idanunta, amma ana nan ana neman yanda za'ayi suyi mata aiki"
Lokaci daya Nasrin tafara hawaye, shaltos Najma, yanzu shikkenan Nawal bata gani?wannan wanne irin rashin imani ne?

Zuciyar Najma tafara karyewa, muryarta tafara rawa alamar zatai kuka tace "to ya zamuyi" daga haka takashe wayar, sai kuka, ita kuka Nawal dinma kuka, tana kukan tafara yimata bala'i, wai ke Baby ba zakiyi shiru ba?

Kinasane ance babu ruwa a idonki amma shine Tun dazu sai kuka kike, dame zamu ji ne, su Abba sunacan hankali atashe suna neman kudi, memakon ki kwantar da hankalin ki ta yanda suma zasuji dadi shine kike kuka, sannan Karki Manta har yanzu Abba baice dake komai ba, akan wannan abinda yafaru, kuma nasani kema kinsani dole sai yamiki fada sosai akan wannan marin dakika yi, saboda haka kuka banaki bane, Addu'ah kawai zamuyi "
Cikin kuka tace" Najma kemafa kukan kike"
"to Baby Dan ina kuka shikkenan kema saiki kama kuka? _please_ kiyi shiru, takama qanwar tata tarungume ta, kowa yana sharar hawaye
** *** **
Yana zaune atsakar gida yazubawa dan'uwansa dake kwance ido yana kallansa, abin duniya duk yataru yayi masa yawa, ace wai kasha wahala kayi karatun amma samun aiki ya gagara, har tausayin kansa yake da iyayensa idan yayi duba da irin Rayuwar da sukeyi
Wayarsa ce tayi qara, yadauko ta daga aljihun gaban rigarsa, _number_ dake kiransa ya zubawa ido yana kallo wannan ba _number Nigerian_ bace, _number_ wata qasar ne, dauka yayi da sallama abakinsa
Daga daya bangaren akace "Yas yakake"
Yanajin ance Yas yaharbo jirgin mamallakin muryar
Cikin girmamawa Kamar ba sa'ansa ba yace "MK ai ban ganekaba wallahi, naga ba _number Nigerian_ ba, kuma nide nasan cewa banda kowa awata qasar"
Cikin miskilancinsa Kamar anyi masa dole yace "Kamanta ni kenan"
"Haba mk baka Manta daniba, tayaya zanyi kuskuren mantawa dakai?

Yaya aiki?

Ya Abuja?

Dafatan dai komai lafiya yana kuma tafiya Kamar yanda yakamata"
"yasir bazaka sauyaba, na tambayeka amsa kawai zaka bani, Eh namanta ka, kokuma a a banmantaka ba"
Murmushi yasir yayi, Wato har yanzu abokinsa yana nan da d'abi'arsa ta rashin son surutu
Afili yace "to ban mantakaba mk"
Ajiyar zuciya yayi "naga saqonka ta _Email Already_ angama komai, yanzu hakama akwai taron danake san turaka zuwa _Algeria_ ka wakilceni"
Yace " _Algeria_ de da nakeji ana fad'a?"
Shima yace " _Yes_ "
"to mk ba zuwanne matsala ba, akwai qanina dabayajin dadi, yakai _one_ _month_ yana kwance wallahi, kullum ana fama a asbiti amma abin saide godiyar Allah"
"subhanallah, haba Yas meyasa baka sanar daniba?"
"haba abokina, tayaya daga haduwar mu zanyita fadama matsala"
"meyake damunsa?"
Yas yace "jijiyar qafarsace tasamu matsala, baya iya takawa"
"wanne asbiti kuke zuwa?"
"asbitin Malam Aminu, yanzu hakama gobe zamu koma ganin likita Kamar yanda muka saba zuwa"
"bansan Asbitin ba, _but_ zaka Ganni gobe insha Allah,"
"amma mk baka qasar fa, Dan Allah kayi zamanka"
Anasa bangaren shima kawai girgiza kansa yayi Kamar yasir din yana gabansa tareda kashe wayar
Mama dake gefe ta kalli yasir tace "wayene kuma mk kuda bakwa rabo da lalata suna?

Yace" mama wannan shine Muhammad Kabeer, abokinane, tare mukai karatu dashi a _America_ , saudaya yataba zuwa kano shida babansa, shima dole baban nasa yayi masa sun kai ziyara gidan marayu, shine yazo muka gaisa dashi, tosai rannan yazo gaisuwa shine yaqaraso muka gaisa harma yace natura masa takarduna, tofa shine yanzu wai zaizo yaga jikin Mu'azzam nace masa ya zauna basai yazoba tunda baisan asbitin ba, sannan kuma bamaya kasar
Mama tace "wai wanne asbitin ne baisaniba?

Asbitin Malam aminun?

Yace" wallahi mama baisaniba, sau biyufa yataba zuwa kano, zuwansa da babansa, dakuma zuwan dayayi rannan, saikuma wannan da zaiyi na uku, "
" Allah sarki, a a kyaleshi yazo, aiba'a hana mutum aikin lada, Allah yabarku tare kuma yabar zumunci "
Yace" amin mama "
*** ***** ***
"muhammadu"
"na'am Malam"
"yaya kukai da mutumin da yace zaisai filin naka?

Abba yace" Malam ai mungama magana dasu sun riga da sun sayi guda daya dubu dari uku, Ga kuma Sultan yakawo dubu dari da ashirin shima Salisu dazu yakawomin dubu talatin kaga yazama dari hudu da hamsin kenan,"
Malam yace" toga wannan kahada dasu "
Abba yace" baba yaya zaka takura kanka har haka, kaima akwai dawainiyar Gida fa "
" kada kadamu muhammadu, idan banyimaba wazan yiwa?

Karbi Dan Allah dubu dari biyu ne babu yawa, kahada dana wajan ka yazama dubu dari shida da hamsin, kaje kakaiwa likitan gobe da safe, kasake roqar alf
arma akan suyi mata aikin, idan Allah yaqara hore mana kodaga bayane sai acika musu sauran "
Lokaci daya Abba yafara kuka, yarungume baban nasa yanayi masa godia, Malam yace" babu damuwa d'ana, Allah yakiyaye gaba, kaje gida kahuta haka nan "
Abba yana zuwa yafadawa ummah Halin da ake ciki, sosai ta nuna farin cikin ta, sai yanzu hankalin ta yafara kwanciya akan rashin lafiyar autar tata.
Chapter 7 · 0% Book details