Sashe 46
Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya Sultan fa yana sona "
Baba yace" aini baki fadamin hakanba Nasrin, kuma mutanan nan ba kai tsaye sukace abasu ba, sunce min neman iri sukeyi, keda Sultan ku kukai kuskure dabaku kawo maganar gidaba, danhaka kiyi hakuri kawai Allah yasa hakane yafi alkhaairi "
Cikin sanyin jiki tatashi tashige dakinta, tunani tafara Wato tanan yarimah yabullo mata kenan, shine maimakon ma ya lallasheta harta yarda shine zai tashi yaturo manya?
Hawaye masu dumi suka zubo mata, meyasa zaiyi mata haka?
Meyake ji dashi?
*** ***** ***
"sahla abinda kikeso bana tunanin zai iyu"
Jikinta yayi sanyi, tace "meyasa zakace haka Sultan?
Bankai matsaayin dazaka soni bane?
Kokuma kaine bakada ra'ayin mace kamata?"
Yace "ba haka bane sahla, kinada komai, hankali nutsuwa, sannan kinada kyawun sura ta yanda kowanne namiji yaganki dole yaji kin masa, saide kinfi karfina, hakan yasa Tun farko banfara nemawa kaina matar da tafi karfina ba, saina nemi daidai Dani"
Gabanta yafadi tace "kana nufin akwai wadda kakeso?"
Yakalleta yace "wannan haka yake"
Tace "Sultan ina sonka, danhaka bazan hanaka auren wadda kakeso ba, amma mazai hana ka aure mu mubiyu?
Tunda Allah yabaka damar hakan, sannan ni kishiya bata dameni ba, karka Manta daga gidan sarauta nataso, Tun ina yarinya da kishiyoyi na bude idona, amma bazan takura ma, na baka dama kayi magana da ita, idan kana ganin Babu matsala nata bangaren shikkenan "
Tausayi ta bashi, Awannan lokacin wacce yarinya ce Mai kyau da aji kamar sahla zata baiyanawa namiji abinda yake ranta?
Sannan yafada mata akwai wadda yakeso still bata karayaba tace taji tagani tana sonsa ahaka
Ajiyar zuciya yayi, yace" to shikkenan sahla, insha Allah zanyi magana da ita, duk yanda mukai da daddare Zan kira ki "
Bata iya yimasa magana ba, kawai de ta girgiza masa kai tayi gaba, yayinda yabi ta da kallo, sahla nada komai, yarinyar baza'a fada mata kyawun diri ba
*** ***** ***
Bayan ya idar da sallar magrib yadauki wayarsa ya kira Nasrin, duk da cikin ransa yana shakkar yimata maganar Dan yasan halin mata da kishi
Tana dauka yaji muryar ta Kamar tana kuka yace "Nasrin lafiya?
Meyake faruwa?me aka miki?"
Tace "yaya Sultan dama yanzu nake shirin kiranka akwai maganar danake so muyi"
Yace "nima yanzu haka dawowa ta kenan daga wajan aiki, wata yarinya tatareni da wata magana shine nakeso nakiraki nafara jin ta bakinki sannan inyi mata bayani"
Tace "wacce irin magana?"
Yace "akwai wata yarinya wajan aikinmu daya da ita, sunanta sahla, ta fadamin cewa tana sona, idan Babu damuwa kuma zaki amince tanaso na aureku tare"
Murmushi tayi Mai ciwo tace "yaya Sultan kenan, daka sani daka amince mata ma kai tsaye"
"mekike fada haka Nasrin?
Ke dinfa?"
"yaya Sultan anyimin miji agida, shine maganar danace inaso nakiraka yanzu muyi,"
Yace "Innalillahi wai da gaske kike?"
"da gaske nake yaya, dazu ma suka tafi masu neman auren"
Yace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un waye hakan?"
Tace "sunansa yarimah Nasir, dan gidan sarkin gombe, abokin mk ne mijin Nawal"
Cikin mamaki yace "abokin mk?
Kuma kikace Dan gidan sarkin gombe?"
Tace "eh"
Yace "tab, to ai yarinyar danake fada miki yanzun qanwarsa ce, ta fadamin cewa itama yar gidan sarkin gombe ce, sannan ranar dana fara haduwa da ita a company nace mata ni mk ne yaturoni, sai tamin aikuwa tasan shi abokin yayanta ne"
Nas tace "to wallahi shine"
"ikon Allah, kice d'an sarki yamin qafa
Shi daya tashi sai yabi ta sama, matsalar da muke fuskaanta kenan yanzu kanason yarinya ka naso ka aure ta amma bazaka fara fadawa iyayen ta ba, saide kaje wajan yarinya, gashi yanzu inaji ina gani Zan rasaki"
Tace "zamu rasa juna de yaya Sultan"
"kiyi hakuri Nasrin, haka ubangiji ya tsara mana, dama can yariga ya rubuta cewa zamuyi alaqa da 'yan gida daya, Yaya da qanwa"
Hawaye suka zubo mata, batare data ce komai ba takashe wayar, tasan cewa yanzu kam tarasa Sultan, saide kuma wani bangaren na zuciyarta tanajin yarimah aranta, ajinsa yana birgeta, kawai wannan ikon nasane bataso, taga kuma abin Kamar a jininsa ne, yanzu yaturo mata mutane amma koya kirata wanne irin abu ne wannan?
*** ***** ***
Wajan karfe goma da rabi ya kira wayarta
Tana ganin kiransa ta amsa wayar jikinta asanyaye
Yace "gimbiya Sahla"
Cikin sanyin jiki tace "na'am, inajin ka, Yaya kukai?"
"kinsan Allah akoda yaushe yana tareda bayinsa masu hakuri, may be hakurin da kikai kika dauki qaddara kika sa aranki zaki iya zama da wata shiyasa Allah ya juya lamarin zuwa ga yayanki"
"bangane ba, me kake nufi?"
"sahla yayanki ya rigani, yama tura manyan sa ayi masa Tambayar auren ta,"
"kana nufin yaya Nasir ne yake sonta shima?"
Yace "hakane Sahla, kuma iyayen ta sun bashi"
Tace "ashe ni da yayata nake kishi bansaniba?"
"ai bakiyi kishi ba, dangana kikasa aranki, kuma sai Allah ya sauya al'amarin sa"
Tace "hakane, kayi hakuri, nasan yanda so yake, kuma nasan cewa kana sonta, amma inama albishir da cewa insha Allah zanbaka kulawa fiyeda wadda zata baka"
Yace "kinyi alqawarin hakan?"
Tace "insha Allah"
Ajiyar zuciya yayi, gefen kansa nayi masa ciwo, kuma yasan hakan baya rasa nasaba da wayar da yayi da Nasrin, fatansa daya Allah yakawo masa agaji
*** ***** ***
Kusan sau shida yana gwada kiranta amma yakasa, dazaran yayi dialing number saiya katse
Cikin ransa yace to kode tsoron yarinyar nan nafara ne?
Tun dazu nakasa kira?
Koda yake abinda nayi matan ne Kamar ban kyauta mata
Dakewa yayi yafara kiranta a karo na bakwai, a lokacin shabiyu saura amma idonta biyu, tarasa wazata fadawa damuwarta taji dadi, tayi kiran Nawal amma bata sameta ba
Adede lokacin wayarta tafara qara, tana ganin number taganeta, tashare taqi dauka
Yasake kira, still bata daukaba sai akaro na uku sannan ta dauka tayi shiru
Shima yana jin haka cikin ransa yace to tasamu labari kenan
Kwanciya yayi akan gadon yace "Zumata"
Tanajin sa tayi shiru, shima yasake cewa "Zumata dake nake fa kinyi shiru"
Zuciyarta ta karye, dab take da fashewa da kuka, cikin rawar murya tace "mezan maka kuma?"
Murmushi yayi yace "kiyi hakuri Nas, nasan nayi miki laifi, amma ga yarimah yana neman tuba awajan ki, Nasrin ina sonki, inaso kibani dama na nuna miki yanda nake jinki acikin zuciyata, Nasrin nazo har gida domin nasamu hadin kanki amma kinqi bani wannan damar, shiyasa na turo su, amma kiyi hakuri, yanzu ma idan kina buqatar nasake tsugunna miki saina sauka daga kan gado na nemi yafiyarki, "yana gama fadar haka yafara kokarin Saukowa daga gadon
Tanajin motsinsa ta cikin wayar, Ahankali ta fashe da kuka Wanda bata samu tayishi yanda takeso ba dazu
Yana jin kukanta yadafe kansa
yace" nashiga uku, wai ke bakya jin rarrashi ne
?
Adinga yimiki magana daya?
"
Tanajin ya hauta da fada ta tuno yaya Sultan, shide baya yimata tsawa ko kadan
Aikuwa saita sake rushewa da kuka
Girgiza kansa yayi, ya gyara muryar sa zuwa ta lallashi yace "Nas, Dan Allah kiyi hakuri kinji tawan?daga yau yarimah bawanki ne sai yanda kikai dashi, kidena kukan kinji Zumata?"
Ahankali ta rage sautin kukan nata, harta daina duka, sai ajiyar zuciya take
Cikin ransa yace tab akwai aiki agabana kenan
Saida yaji tadena kukan gaba daya sannan yace" nine nayi miki laifi ko?
"
Tace " um"
Yayi Murmushi yace "to na daina kinji?"
Ta daga masa kai Kamar yana ganinta
Yasake cewa " kinyi addu'ah?"
Tace "um"
Yace "to share hawayen Zumata Tun kafin nazo na share mikisu da baki na"
Maganar sa tabata kunya, amma saita share sanin cewa shidin Dan duniya ne
Dayaji shiru yasake cewa "kin share?"
Tace "um"
Yace "to shikkenan, saida safe ki kula min da kanki Zumata muachhh
Yasakar mata kiss ta wayar
Cikin sauri ta kashe wayar, tana Tambayar kanta dama haka yake
?ana ganinsa sumi sumi da shegen iko ashe haka yake?
Shima a nasa bangaren Murmushi yayi, yanzu de dole ne yakoyi lallaba mace kenan
Shida ake lallabawa anayi masa biyaiya yanzu saide yayiwa wata
*** ***** ***
Kayan bacci ne ajikinsu Wanda ake kira dashi da Babu...
Tana kwance ajikinsa bacci na neman daukarta , yayinda yake shafa gashin kanta, wayarsa tadauki qara
Dauka yayi tare da cewa "yarimah ya ake ciki?"
Yarimah yace "mk anwuce wajan ai"
Murmushi yayi yace "congrats angon Nasrin"
Tanajin haka tafara kokarin tashi daga jikinsa, yamaidata yahanata tashi
Saida yagama wayar da yarimah sannan Yakalleta yace "ya akayi Baby nah?"
Tace "kaifa nagama ganeka, na lura kwata kwata bakasan yayana da Nasrin, yanzu haka nasan dasa hannunka aciki"
Murmushi yayi yace "Baby nah kenan, Baby bazaki ganeba qawarki tanada hankali, yayanki yana nutsuwa, sabanin mu, mun tashi cikin mutane daban daban har hakan yasa wani lokacin mutum zai kauce hanya, yarimah nasan yanmata sosai, amma baso na aure ba, yanzu daya samu qawarki sai kiga adalilinta yadena wasu abubuwan, Kamar ni dakika hanani zane ajikina kika hanani saka kayan dabasu dace ba "
Kallansa tayi tace" kana nufin ka dena?
"
" qwarai kuwa Baby nah, bana ra'ayin su yanzu, kwata kwata ma basa cikin raina, nasan ummu da sauran yan'uwan mu zasuji dadin hakan "
Cikin murna tace" Alhamdulillah Allah na godemaka "ta rungume shi a jikinta sosai
Kissing din kumatunta yayi yace" Baby na irin wannan runguma haka ai saiki sa nasaki layi "
Itama kissing din nasa kumatun tayi tace" nikam yanxu bacci nakeji, kabarmu muyi bacci Dan Allah, yauwa yaushe zamuje gida?
"
Wata irin daria yayi yace" keda gida ai saikin samu ciki "
Cikin sauri tace" ciki?