← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 48

Sashe 19

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"
Nawal ta miqa mata wayar, tana karba tace" gashi kuwa har screen yafashe "
Jakarta ta zuge tadauko wata waya qirar iphone tabata tace" ga wannan wayar Babu komai acikin ta, zaki iya cigaba da amfani da ita kibada sadakar wannan dayar, nima Baffah ne yakawomin lokacin da zaizo "
Dasauri tace" a a wlhy kibarshi nagode, wallahi Babu damuwa Zan iya amfani da tawama ahaka,"
Ummi tace" a a, Nawal, Inda tare nake da Baffah to zai iya marinki, saboda bayaso kokadan yaga ana ja'inja dani"
Ahankali tace "to ngd sosai, Allah yasaka da alkhaairi," cikin ranta kuwa cewa take gara na karba inba hakaba kafin mu sauka saita gama fadamin komai na Baffah
Da kwatance da Komai suka qaraso gidansu, tareda ita suka shiga gidan , Umma da mama mariya na ganin ta tareda baquwa suka karbeta hannu bibiyu,amma umma kam tambaya ce fal ranta, jira kawai take matar tatafi
bayan tayi sallah tace" zata tafi amma tanason ganin maigidan
Aka tura Saif yaje yakira Abba amajallisa, har falon umma Abba yaqaraso yaga baquwar fuska, cikin Murmushi tace "Alhaji dama inaso ne zamuyi wata magana"
Abba yanemi waje ya zauna yace "to baiwar Allah gashi kuma bansan kiba"
Murmushi tayi tace "Sunana Halima Jamal Baba, ni mutuniyar Adamawa State ce, naga 'yarka Nawal ne amakaranta yanzu, Wato Alhaji gaskiya kayi kokari kuma ka jajirce akan tarbiyar yarka, nima hakan ne yad' au hankalina akanta harna biyota gida inaso kabawa d'ana Baffah auren ta idan Babu damuwa, bazan boye maba dana bayaji, amma inaso sanadiyar yarka yazama abin alfahri agareni, "
Ta ajiye masa number wayarta taci gaba da cewa" wannan itace number ta, kuma na baka dama kayi bincike akaina Kamar yanda shari' ah ta fada, zaku iya tuntubata daga baya domin naji duk abinda kuka yanke "
Tana gama magana taayi musu sallama tatafi
Ina fatan zakumin uzuri duk lokacin dakuka jini shiru kunsan jiki da jini
Sharhi Dan Allah
Mrs Usman ce
[2/2, 1:47 AM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
21&22
"To Baffah nawa nake dashi inba kaiba?"
Kansa dake masa barazanar rabewa biyu yadafe
, jiri-jiri yafara daukan sa yatafi luuu zai fadi tayi saurin tashi ta riqoshi tareda zaunar dashi akan kujera
Idanunsa sun kad'a sunyi jajir, yafara furta kalmar "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un" sai kuka
Kuka yafara Kamar qaramin yaro
Ita kanta Ummi jikinta ne yayi mutuqar sanyi, al'amarinsa yayi masifa tsoratata, rabon dataga kuka a'idon Baffah ita kanta ta manta
Kuka yake sosai yadafe kansa da hannayensa duka biyun, cikin hawaye ga idanu yayi jajir yajuyo ya kalleta "why Ummi?

Ummi meyasa?

Meyasa zakimin haka?

Ummi akwai yarinyar danake so, akwai yarinyar da d'anki abin sonki yake mutuwar so Ummi, ina cikin tashin hankali kullum sai nayi mafarkin ta, naqi sanar dakene saboda inaso saina nemota, haba Ummi, meyasa Dan Allah?" yasa tafukan hannunsa Yarufe idonsa dasu Idanunsa naci gaba da tsiyayar hawaye
Adede wannan lokacin tafuto daga cikin dakin Ummi, Gabanta ne yafara faduwa ganin wani hadadden gaye yana kuka tuquru, ko shine Baffan?

Ta tambayi kanta
Tsananin mamaki yakamata Babba Kamar wannan yana kuka
Ummi ce tadago taganta, cikin sanyin jiki tace"zoki zauna Nawal "
Jin ankira sunanta akusa yasa yadago kansa yazuba mata wani kallo me kama da harara,still idanun nasa na zubar da hawaye, gabansa ne yafadi Wanda shi kansa baisan ma'ana da dalilin hakanba, kuma arasa waza'a aura masa sai wannan ficiciyar yarinyar dazai iya karyawa Tun adaren farko
Adarare taje kusa da Ummi ta zauna tareda sunkuyar da kanta
Ummi ta dubeshi "Baffah, naji bayaninka, kayi hakuri Umminka tamaka laifi, tayima aure batareda saninka ba, nayi tunanin Zan iya zartar maka da kowanne hukunci ne amatsayina na mahaifiyar ka, amma kayi hakuri"
Wani sabon hawayen ne yazubo masa, yasaka hannu ya share, "A a Ummi, kiyi hakuri ba haka nake nufi ba, kin kalli zancena ta wata fuskar ne, kiyi hakuri"
Quri Nawal tayi da ido tana kallansa harya gama maganar, Gabanta yana faduwa da sauri
Tausayinsa ne yakama Ummi, tace"shikkenan, Allah yayima albarka, bansan cewa akwai yarinyar da kakeso ba,amma yanzu ma lokaci bai qureba, duk lokacin daka sameta, zaka iya auren ta, amma yanzu de, ga yata Nawal nan, Baffah ka riqemin ita amana, "
Wani irin qullutun Baqin ciki ne yazo wuyan Nawal, kowa yanada Wanda yakeso amma antashi anwani hadasu da juna, jin cewa yanada wadda yakeso yasa mk yafado mata arai, batasan lokacin da hawaye suke silalowa daga idanuwanta ba
Jin bece komai ba yasa Ummi tasake cewa "Kayi alqawari?"
Still baiyi mata maganaba yadaga kansa
Hannunta ta miqa masa tace "bani"
Ahankali ga idanu jajir yace "ban siyoba"
"baka tabaamin qaryaba, banaso kafara, qaryar bata dace dakai ba kwata kwata," tasake miqa masa hannu batare datace komai ba
Ahankali yasa hannu cikin cikin wandon jeans din jikinsa yadauko wata akwati yar qanqanuwa irin wadda zobe yake zuwa aciki, yadora mata atafin hannunta
Budewa tayi taga zoben Dan qarami dashi yayi kyau, atsakiyarsa akai harafin 'n' din, saika zuba ido sosai zaka gani
Ta kalleshi tace yayi kyau sosai, gashi ka karba kasaka mata, hakan zai nunamin cewa alqawarin daka daukamin nacewa zaka kula da ita yana nan "
Zuciyarsa Kamar zata fashe saboda haushi, ya karbi zoben yariqe baiko kalli Inda takeba
Ummi ta dubi Nawal tace" 'yata share hawayen ki, kiyi hakuri kinji, tashi kije yasaka miki zobenki "
Hawaye ne yazubo daga idonta Ahankali ta tashi taje gabansa ya tsugunna, amma ta kasa kallansa, wani irin kwarjini yaamata, yanzu wannan Babban ne mijinta?take tambayar kanta
Ummi ta kallesu tace" menene haka Kamar wani me laifi dame neman yafiya?please kutashi tsaye mana"
Ahankali ta miqe tsaye, shi kuwa saida yadebi wasu seconds sannan yatashi tsaye shima
Ummi tace "Nawal bashi hannu"
Ahankali tadaga farin hannunta dayaji zanen fulawa tamiqa masa
Ganin Ummi tana wajan yasa yakai hannunsa yakama nata hannun, wani irinsa zirrrr yaji tundaga kansa har tafin qafarsa, duk rungume rungumen mata da yakeyi bai tabajin hakan akan kowaba sai akanta
Tafin hannun nata laushi, Ahankali yafara tura zoben harya gama saka mata, yana gamawa yasaki hannun nata, yakama hanyar fita daga falon
Ummi tace "ina zakaje?"
Cak ya tsaya a Inda yake, bai juyo ya kalleta ba yace "Ummi Zan fita ne"
"kadawo ka zauna, koka Manta kai Ango ne?, sannan idaan zaka fita matarka yakamata ka fadawa"
Baqin ciki ne yakama shi, Kamar zai fashe da kuka haka yadawo ya zauna yakawar da kansa can gefe, kwata kwata Yaqi kallan Inda take ma
Har azahar haka suke wannan zaman kuramen, Ummi tana lura dasu kuma ba tayi musu maganaba ta qyalesu, tasan cewa rashin sabo ne kawai, zuwa Dan wani lokacin zasu saba
Ummi ta kalleta tace" Nawal tashi kizuba mana abinci, Karki zubawa Baffah da yawa, bayasan cin abinci "
Cikin nutsuwa tace "to" ta tashi tanufi kitchen din
Kamar yanda Ummi tace haka tayi, amma tana tsugunnawa agabansa da abinci yamiqe tsaye
Ummi tace"ina zakaje?

"
" masallaci zanje Ummi" abinda yace kenan
Tace" idan ka'idar kadawo gida "
Bece da ita komaiba yafice, haka kuma yana idarwa yadawo ya zauna yayi tagumi
yana kallan tv
Shide wannan zama kawai Dan dole yake yinsa
*** ***** ***
"umma ashe Najma batada lafiya, saida nazo yanzu naga jikin nata"
"Nasrin wallahi kinganta nan tunda Baby tatafi takwanta jinya, zazzabi yarufeta, datawo nan ta kwanta a'inda Baby take bacci"
"Allah sarki, Allah yabata lafiya, Umma yaya wajan Babyn kuwa?

Inata kiran wayarta akashe"
"eh nima Tun dazu nake kiranta bata shiga, amma nasan idan tabude wayar zata kira mu"
Jinjina kai tayi tace"Allah sarki Baby, toshknn umma bari natafi gida, "
" to Nasrin ki gaida mamanku, ga wannan kikai mata "tabata wata leda
Tace" to umma sai anjima "
*** ***** ***
Har dare suna zaune kowa yayi shiru, yana zuwa sallah Ummi zatace yana idarwa yadawo
Har qarfe tara na dare suna zaune suna kallo
Amma shikam kawai yana kallan photon cikin ne, amma baya fahimtar komai, Baqin ciki ne cike da ransa fuskarsa Babu alamun annuri atamke
Ummi ta kalleshi "Baffah adakina nace Nawal ta zauna kafin kadawo, tunda kadawo gobe saikuje ka nuna mata dakin naka, saiku sake gyara shi zuwa yanda kukeso"
"No Ummi kawai kibarta anan din zaifi,"
"wai Baffah meyake damunka ne?

Cemaka akai itama yarinyar tanaso ne?"
Cikin ransa yace"tanaso mana, idan bataso ai bazata yardaba, shi Dan bai saniba ne, aida bazai yarda ayi ba, ciki ciki yace mata "Ummi bansaba kwana da kowa bane ad'akina, bayan hakama d'akin yamana kad'an"
"duk wannan uban dakinne zakace yamuku kadan?

Saikace wata giwa?"
Shiru yayi baice komaiba
Sai cika yake yana batsewa
Ummi ta kalli gefen da Nawal take zaune, sai taga har tayi bacci
Ta maida Kallanta gareshi tace "laa Baffah kaga yarinyar nan har tayi bacci, d'an meqamin ita daki"
Dasauri ya kalleta saboda jin furucinta
Tace"yi sauri mana yarinya tana bacci a kujera kar wuyanta yayi ciwo"
Takaici ne yakamashi, wai Ummi daga ganin yarinya duk tabi ta rikice
Tashi yayi sai qunci yake yaje kanta ya tsaya, amma bashi da niyyar tabata
Ummi tace "mekake jirane?"
Kallanta yayi yaga hankalin ta ma yana kan tashar datake kallo
Hannun rigar jikinsa yafara tattarewa Kamar Wanda zaiyi wanki
Sannan yakai hannu zai dauketa, hannun nasa bai sauka ko'inaba sai akan hips dinta, cikin sauri yajanye hannunsa daga wajan
Sannan yadauketa cimak yayi dakin Ummi da ita, Kamar yanda ya zata haka yaji, batada wani nauyi, to dama wannan ficiciyar yarinyar ina zataga wani nauyi
Saida yakai ta har kan gadon Ummi sannan ya kwantar da ita, garin d'ora kanta akan fillo hular datasa akanta tafadi gefe, dogon gashinta yazubo akan hannunsa, gashin nata yabi da kallo yaga sai sheqi yake kuma da alama zaiyi santsi
Cikin sauri yajanye dayan hannunsa daga jikinta, Wanda gashin yazubo mata ma yawatsar dashi Kamar yaga wani abin qyama
Tambayar Data fara zuwa kansa itace, meyasa gashinta yake haka kode ba bahaushiya bace?
Chapter 19 · 0% Book details