← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 48

Sashe 11

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"
Saida Sultan yayi ajiyar zuciya sannan yace" wallahi Usman ina fad'ama qanwata ya lalatawa idonta, yarinyar fa har makancewa tayi, mu kaje gidansu muka sanar da ubansa Allah shine mutumin nan yayi mana korar kare
Usman yace" Bala'i, anya kuwa Anwar yasan cewa ita qanwar ka ce?

"
" inma bai saniba idan yaganni yaganta ai dole zai gane, saboda sonake na tisa qeyar yarinyar, na sata agaba Muje tarama abinda yayi mata da hannunta, munje munkai qara wajan yan sanda, amma wani daga cikinsu yabamu shawara akan mujanye case din, saboda Mai unguwa sale zai iyayin komai akan hakan, kuma idan mukaje kotu za'a iyayin watsi da qarar, shine nakeso na kamashi itama ta lalata nashi idon kaga anyi 50 50 kenan
yayinda ubansa yakaimu kotu kaaga anan dole a saurari qarar, tunda mu yanzu idan muka kaishi babu abinda za'a yi masa
Amma kaji usy wai ahaka Abba yake cewa narabu dashi "
" kata'i, shine abinda yafuto daga bakin usy
sannan yace "Sultan wannan ai ba abin yafiya bane, idan ku kunyi shiru ai anbashi damar dazai sake yiwa yar wani haka"
Sultan yace "kaima de kafada"
"Amma Sultan baka kyauta minba dabaka kirani munje tare daku gidanba, narantse da Allah dakunje Dani inba saina wankawa Mai unguwa sale mari ba
saide yasa adaureni,"
Sultan yace "abinda nasoyi kenan Abba ya katseni"
Usy yace "wallahi Anwar bayanan, yaje Uganda, amma inde yadawo Zanzo har Gida nafadama"
"Usman lagos zankoma, Abba yace natafi, sannan itama yarinyar yanzu suna Albania anayi mata aikin idon Acan, sai sundawo sannan zanzo naganta, ina fatan a lokacin Data dawo shima Anwar yadawo, zanzo naganta kaga a lokacin saina ritsa shege
"good hakan yayi, Allah yasa lokacin dazaka zodin shima yadawo"
"usy koda baidawo ba Zan jinkirta zuwan nawa har sai lokacin daya dawo, nide abinda nakeso dakai shine daka ganshi kamin waya"
"to shikkenan Sultan saika jini,"
Daga haka sukai sallama
*** ***** ***
Washe gari tunda asuba Abba dayai sallah a dakin nasu yafara karatun qur'ani Ahankali, karatun dayake ne yatashi Nawal daga baccin datake
Ahankali ta yunqura ta tashi, Dasauri Abba yaqaraso ya riqeta "Nawal kina buqatar wani abu ne?"
"Abba fitsari nakeji, kuma da yunwa ma
Yace"to bari akira likita", yana fita yadawo da wata mace, itace takamata har zuwa toilet tayi fitsari tareda wanke baki, suka futo "
Gadon tamaidata ta kwantar, itade mamaki yagama kasheta cikin sauri tace" Abba bata barni nayi alwala bafa "
Adede lokacin likitan dasukazo dashi yashigo dakin tareda bata amsa" ai saide kiyi hakuri har acire miki wannan abun na idonki sannan ki rama sallolin dake kanki, keda ba'aso ko abu ne kidauka aqasa saboda idonki "
Abba yayi Murmushi yace" to kinji "
Sannan suka gaisa, itama ta gaishe su tayi shiru, Abba yace" kidinga addu'ah fa, anjima zasuzo su cire miki wannan abun na idonki, idan anyi nasarar aikin idonki zai bude"
Murmushi tasaki tace "to Abba zanyi" cikin zuciyarta kuwa murna ce fal, idonta zai bude zataci gaba da ganin su ummanta
Wata zuciyar tace mata toshi kumafa?mutumin daya ceci Rayuwar ki daga fadawa makanta ta din-din-din?

Murmushi tasake saki ita kadai, to kodan tasake jin muryar sa ai dole ma ta nemeshi, bare kuma yayi mata wannan kirkin ai dole ma ta nemeshi a duk Inda yake (tofa
Shide Ab
ba yaga tana ta faman Murmushi, amma bai kawo komai aransa ba, yadanganta hakan da murna akan maganar dayayi mata
Sai wajan sha daya saura sannan likitoci suka shigo dakin nasu kusan su uku
Ba ita da akaiwa aikiba hatta su kansu likitocin idan kadubi fuskar su zaka tabbatar suna cikin shakku, kowa fatansa asamu nasara akan aikin nata
Gabanta kawai luguden faduwa yake, yanzu idan aka kunce mata tace bata gani shikkenan fa tariga tazama makauniyar karfi da yaji
Wanda zai cire mata ne cikin sigar rarrashi yace "ki kwantar da hankalin ki kinji?sannan yafara warware mata bandejin Ahankali
Mutanan dakin duk sunyi shiru
kowa jiki yayi sanyi, musanman Abba, Wanda mutanan Nigeria suke jiran kiran wayarsa
Cikin nutsuwa yake warware mata bandejin harya cireshi gaba daya,idanunta alumshe, yace "Open your Eyes"
Ahankali tafara bude idonta harta bude shi gaba daya, cikin sauri ta maida idonta tarufe ganin wani irin haske daya ziyarci idonta
Gaba dayansu hankalinsu yana kanta, kowa jira yake yaji abinda zatace
Likitan yace, "bude mana "
Sake budewa tayi ta kalleshi, sannan ta kalli Abba, tasake kallan likitan dasukazo tare amatsayin Wanda yayi musu jagora
Abba de atsorace yake,
Likitan yace "kina ganina?"
Ahankali ta daga masa kanta, sai hawayen farinciki tace "ina gani, amma dishi-dishi nake gani"
Gaba dayansu likitocin suka fara murna ganin anyi nasarar aikin, yadubi su Abba yace, "aiki yayi kyau, dama dole ranar da'akai mata aikin bazata gani karkar ba, dole sai Ahankali idonta zai washe taci gaba da gani sosai, zuwa gobe za'a iya sallamarku"
Abba yadaga hannu sama yace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah nagode ma"
Fita likitocin sukai daaga dakin kowa na farinciki
Suna fita likitan dasukazo tare yadubeta "to yanzu de kuka yaqare ko?

Tunda kinga abbanki, shikkenan kuma idanu sun bude"
Hawayen idonta tashare tace "Abba ashe Zan sake ganinka?

Abba Dan Allah kiramin umma tah"
Shima kansa dadin yakeji yace "to bari akira su, yana kira baiyi magaanaba yabata wayar, cikin sanyin jiki umma tadaga tace" Alhaji yaya ake ciki?

Idanun nata sun bude?

Hawayen farin ciki suka sake zubo mata tace "umma nice, Umma idona yabude, ina ganin komai, Ga Abba ma ina ganinsa da idona"
Ai cikin murna umma tafuto daga falonta tanufi dakin mama mariya tace "maman mus'ab idon Baby yabude" sai hawaye, nan danan umma tafara shashshekar kuka, duk abinda sukeyi Nawal tana jiyosu, itama anata bangaren hawaye take, Abba kuwa yazuba mata ido yana Kallanta wani irin farinciki yaana ratsashi
Shi kansa likitan dasukazo tare jiyake Kamar yayi kuka saboda tsabar farin ciki
Mama mariya tace "Aiyiriri
jama'ar Gida Baby de tawarke"
Aifa lokaci daya suka kaure da ihun murna, har hakan ya janyo hankalin maqota, aka fara tambayar ba'asi
Najma Data futo daga wanka daga ita sai daurin Zani
takarbe wayar tace "shegiya Baby ido kuma yabude, fadamin ya kikaga jirgi?"
Dukda tana kuka hakan bai hanata darawa ba tace "Najma taya zanga jirgi nida nataho a makance?"
Tace "ke wallahi namanta,
idan zaku dawo ki karbi wayar Abba kidauko mana photon cikin jirgin mugani"
"to Najma Zan dauko, ina wayata?"
Najma tace "tana nan naboye miki ita adaki,"
"to kisa min ita achrge, kuma kikira Nas kifada mata Dan Allah"
"to Zan fada mata, Ga yaya Sultan ma da yaya Salisu sun shigo"
Suma karbar wayar sukai kowa yana taya ta murna, daga nan sukai sallama da yaya Sultan akan idan sun dawo zaisa lokaci yadawo yaganta
Saida aka bawa kowa wayar yayi magana da ita sannan takashe wayar tana share hawaye, nanfa yan'uwanta kowa ita yake tayawa murna, gaskiya tayi sa'ar yan'uwa, kowa soyaiya yake nuna mata
Ta bawa Abba wayar shikuma yakira Malam yanayi masa bayanin komai, aka ba tashi suka gaisa yanata tsokanarta
Saida tagama waya da Malam tashare guntun hawayen idonta, cikin ranta tace "ita kuwa dame zata sakawa wannan mutumin?

Bai santaba, babu wata alaqa tsakanin su amma har ya iya bata wannan gudunmawar, "MK" sunan yafado mata cikin qwaqwalwar ta, waye mk?

Yaya zatai tasake ganinsa Taji muryar sa?wacce irin godia zata masa?

Dame zata saka masa?

Tunani tasake yi sannan taci gaba da zance cikin zuciyarta tabbas babu abinda zatayi masa ta nuna godiyarta agareshi face tayi masa tayin auren ta
(aradu kin taro december Nawal
to inba mk sai baqa ba
Ganin tana ta tunani tayi shiru yasa Abba yafara janta da fira harta sake tanada daria, daga qarshe ma ta tashi tana ganin tsarin dakin nasu, sannan tawuce toilet domin yin alwala
*** ***** ***
Kamar yanda doctor's suka fada hakace ta kasance, washe gari aka sallamesu dasafe
Saida suka gama had'a komai nasu sannan suka nemi ticket sukayo gida, Nawal kam tasha kallo, domin kuwa abinda bata ganiba atahowarsu yanzu ta ganshi
Sai bayan azahar suka sauka akano, gida kowa yanata murna, Salisu yaje yasiyo kaji guda uku akayi musu hadaddan abinci
Taxi suka tara ta kawosu Gida, yayinda shima Doc.

Yawuce Gida, Tun kafin su futo daga cikin motar yan gidan suka mamaye jikin motar, tana futowa dukansu suka fara rungumeta saida suka kaita qasa
Daga nan suka shiga Gida aka fara baje kolin fira, maqota sunata shigowa suna taya umma murna, Najma kuwa taqi tafiya nan da can hannunta yana cikin na Nawal, saida sukaci abinci sannan tafara bawa su nura da saif da Najma labarin abubuwan Data gani
Har dare suka kai sunata fira abin sha'awa
Da daddare suna kwance da umma adaki, Umma ta dubeta"Nikam baby abbanku yayi miki magana ne akan abinda yafaru?
Chapter 11 · 0% Book details