Sashe 12
Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"
" A a ummah, baimin magana ba, tunde fad'an da Malam yamin a asbiti, amma shide baicemin komaiba "
Umma tasaki ajiyar zuciya" to Allah yarufa Asiri "
Fira sukaci gaba dayi sama samah daga nan bacci ya daukesu Ga kanta Gana mahaifiyarta
Washe gari Abba ya shirya tsaf, kasancewar ba ummah ce adakinsa ba mama mariya ce, Dan haka yaleqo dakin nata, anan yagansu suna bacci Kamar zata maida Nawal cikinta
Murmushi yayi yafara kiran sunanta harta farka "cikin yanayin bacci tace Alhaji zaka fita ne?"
Yace "eh zanje asbiti likitan da mukai tafiyar nan dashi yace yanaso naje, sannan kuma nima dama inaso naje wajansa na tambayeshi number wannan bawan Allah daya temaka mana, inaso na kirashi nasake yimasa godia, inso samu nema saimu shirya nida Malam Muje har Gida muyiwa iyayen sa godia, saboda naduba jikin katin daya bamu babu number wayarsa ajiki
Tun lokacin dayayi maganar zuwa asbiti tafarka daga baccin datake, amma sai tayi shiru tana saurarensu
tanajin maganar number waya tayi hamdala ciki ranta
Umma tace" to Alhaji saika dawo "
Abba yana fita kofar Gida yahadu da Nasrin tazo gidan itama, kasancewar yasan ta kuma yasan tsakanin ta da yaransa yasa ya tsaya suka gaisa sosai, harda tambayarta mutanan gida, sannan ta shige gidan, shikuma yayi asbiti
Yana zuwa asbiti likitan yace "Alhaji dama akan maganar sauran kudin ku ne, inaso kubani account number natura muku abinku"
Abba yace "to likita mungode, amma karaba mana, kaima ka dauki sauran"
"A a Alhaji, idan ban temaka mukuba ai bazan karbe muku ba, dama million goma yaturo, munyi amfani da million biyar da rabi, saura hudu da rabi "
"to likita Dan Allah ka dauki wani abu aciki, nima idan ka dauka din zanji dadi ai"
Yace "to shknn Alhaji, zan dauki Rabin, saina turo muku million hudun , nagode sosai, Allah yabar zumunci"
"amin likita, amma Dan Allah ina zamu samu number wannan yaron ?
Inaso na kirashi naqara gode masa,"
"gaskiya Alhaji nide banida number sa, asali ma ni bansan shiba ranar nafara ganinsa, kasan number manyan mutane Kamarsu, wahalar samu take, mutum saiya rasa wajan wama zaije yanema, amma kajirani, zanje wajan director nasan bazai rasaba"
Abba yace "to alhmdlh, nagode sosai saika dawo"
Likita nafita bai dadeba yadawo da number arubuce a takarda, yabawa Abba tareda karbar account number din nasa, daga nan sukai sallama Abba yayo gida
Abba yana zuwa gida mama mariya takawo masa abin kari, yace taje takira masa Nawal
Mama mariya na futowa ta duba daki bata ganta ba, tajuya zata koma dakin abban taganta tashigo da hijabi a jikinta, tace "kekuma daga ina kike?"
"mama Nasrin naraka soro, babu Inda naje"
"to kije abbanku yana nemanki"
Dakin abban tanufa, a lokacin takardar tana hannunsa yana kokarin saka number aciki
Tashigo ta zauna agefensa, idonta kar akan takardar hannunsa
Tace "Abba gani"
Takardar ya ajiye agabansa sannan ya fuskanceta yace "babu Inda yake miki ciwo deko?"
Kanta aqasa tace "babu ko'ina Abba, lafiya kalau nake," magana take masa, amma gaba daya hankalin ta yana kan takardar dataga anrubuta number ajiki
Kasancewar layin nasu na manya ne number special ce nan da nan ta haddaceta akanta
Abba yace "shikkenan zaki iya tafiya"
Kallansa tayi tace"abba harka karbo number mutumin ne?
Naji umma tace zaka je kasamo number sa
Yace "eh nasamo, gatama har nasaka acikin wayata, yaqarasa zancen yanayi mata nuni da takardar dake gabansa
Nan da nan fuskar ta tanuna farin cikin datake ciki, tace to Abba atashi lafiya, tamiqe tafice daga dakin
Bayanta yabi da kallo cikeda mamaki, cikin ransa yace ita kuma menene take tawani Fara'ah?
Tana zuwa daki ta dauki wayarta tayi saving number aciki da sunan 'my Choice' (tab
Dole ma tasa kati awayarta ta kirashi da daddare, sai Murmushi take ita kadai Kamar sabon kamu
Najma ce tashigo dakin ta zauna agefenta tace"ke Baby kin dawoma amma kin wani liqe adaki Kamar Anwar din zai shigo Gida yakamaki?
Haba yakamata ki futo tsakar Gida asha fira "
Ajiyar zuciya tayi ta dubi Najma, tace" ina nan ina tunanin za'bina "
Najma ta juya idanunta tace" zabinki?
Waye kuma zabinki?
Kode kin fara son Nuhu bansaniba?
"
Lokaci daya tabata ranta tace" waye kuma Nuhu?
Kinga ni MK nake nufi "
Kallanta tayi dakyau tace" Baby kinada hankali kuwa?kyautar million goma fa ba dubu goma bace, cikin yan siyasa ma bakowa ne zai dauki zunzurutun kudi har million goma yabaka ba, to banqiba gwamnoni haka, kinsan kuwa tunda yayi wannan kyautar ba qaramin mutum bane, shine zakice kina tunanin sa, nasan qarshan maganar dai shine kice kina sonsa, kinsan matansa nawa?
Kinsan halinsa?
Mutumin kirki ne kona tsiya?
Sufa irin wannan manyan mutanan ba kasafai suke zama da mace guda d'ayaba "
Itama Kallanta tayi tace" Najma, kinata maganar wani kudi million million, ni waye yace miki Dan kudinsa nake sansa?
Kawai nima haka naji ina sansa, sannan ni koda yanada wata matar hakan ba zai dameni ba tunda shi nakeso dole naso abinda yakeso, koda matansa uku ni Zan roqeshi ya aureni amatsayin ta hudu
Najma tace "to wallahi bari kiji, Dan baki ganshi bane ranar daya biya miki kudin aikin idonki a asbiti, mutane ne suke take masa baya Kamar wani Dan siyasa, yasin wannan mutumin duk da banganshi ba ko a 'yar aikinsa ba zai daukeki ba Baby
Nusaiba Muhammad
saqonki ya iso gareni, sau dayawa zakaga ana karanta littafi amma ba' asan ma'anar sunayen taurarin littafin ba, abinda sunan NAWAL yake nufi shine (kyauta) NAJMA kuma (tauraruwa) NAJMATY ( tauraruwata)
Naci karo da Comment din wani bawan Allah dayake tambayata wai Wacece Baby din da MK yakesan yasake gani?
Idan kana bibiyata daaga farko naayi bayani cewa yarinyar sunanta Nawal, kasancewar adakinsu babu mace sai maza shiyasa yayunta suke kiranta da Baby, Beauty kuma qawarta ce take fada mata hakan,shikam mk ai bai santa da Nawal ba, da Baby yaji ankirata, kaga kuwa aishi Baby zaice, Allah yasa Wanda basu ganeba sun fahimta yanzu
Banajin dadin yanda wasu basasan yin Comments bayan kuma sun krnta, inasan sharhi sosai
(yaya makomar alwashin da Nawal ta dauka akan mk?)
(shin waye mk?)
Mutara zuwa gobe insha Allah
Amnah El Yaqoub
[1/28, 11:26 AM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE...
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
*Gaskiya Babu abinda zance tsakanina da 'yan group din Khaleesat Haidar sai godia akan yanda suke zuba sharhi, ban taba tunanin book din zai samu karbuwa hakaba shiyasa na sadaukar da wannan shafi agareku*
13&14
To yanzu waya fadamiki su masu aikin basuda qima?
Ai idan nasamu ya dauke ni aiki shikkenan zance yaqare yagama sona, Kamar baki karanta labarin shalelan baba ba?
"
Najma tace" kada kiyi kuskuren hada Rayuwar novel da Rayuwar ki Baby, marubuta suna saka abubuwan da bazai taba faruwaba agaske acikin novel,misali :ya rungumota, yakama hannun ta, yayi kissing dinta wannan duk tatsuniyace, kawai maggi ne suke qarawa miyar littafin su Dan yayi dadi, amma agaske cikin al'ummar hausawa yarinya Mai tarbiya ai bazata taba yarda hakan tafaru a gareta ba
Sannan itama shalelan da tayi aikin aka sota aiba haka kawai yaso taba, da temakon yar'uwarsa, ke kuwafa?
Wakika sani nasa dazai soki harya temaka miki kisamu shi mk yasoki?
Kamar fa kiwayi gari ne kice ke Mai kamfanin mtn kikeso, Dan Allah Baby awacce duniyar zaki sameshi?
Saiki hadu dashi ahanya ma yawuce kiwuce bakisan shine ba, nide shawara ta agareki kicire wannan al'amarin daga cikin zuciyarki, wahala kawai zakisha "
Budar bakin Nawal sai tace" ai dama ita soyaiyar gaskiya sai ansha wahala ake samunta,
kawai Najma kifadi alkhaairi ko ki shiru "
Miqewa tayi tace" nayi shiru, kisha tunani lafiya Baby "daga haka tafice daga d'akin
*** ***** ***
Har zuwa yamma tana d'aki tana tunanin mafita, ta saqa wannan ta kunce wancen nazari tayi akan kalaman Najma, kuma fa aduk cikin maganganunta babu na yarwa
gaskiya ce abaiyane, yanzu idan nemansa zata fara ta wacce hanya zata bi?
Hanyar farko de itace number sa kuma tasamu, hanya ta biyu kuwa itace nemansa, ta ganshi yaganta, Dan haka dole zata nemi shawarar Nas, tasan cewa bazata bata shawarar banza ba
Umma ce ta leqo cikin dakin tace "kije Nuhu yazo inji Saif,"tareda juyawa
Wani haushi ne yakamata, ace za'azo wajan ka amma akasa sanar dakai?
Ai aqalla ko awaya ne akiraka aji kana Gida ko bakanan, kanada lokaci ko bakada shi?
Amma kawai shi kullum babu tunani babu komai saide ya wanke qafa yazo
yanzu Inda girki take haka zata katse kenan taje wajansa
Tsaki tasaki tadauki dogon hijabinta tasaka tafice daga dakin
Umma tana zaune afalo ta kalleta "ahaka zaki fita idanunki fari qal ko kwalli babu?"
Murya ciki-ciki tace "umma bansan zaizo ba, bai fadamin ba shiyasa ban shirya ba, kuma likita ma ya hanani saka kwalli (
kai)
" ke kika sani, idan bakya sansa meyahana kifada masa gaskiya Tun tuni, Tun magana bataje ko'inaba "
Itade batace komaiba tafice, ta iskeshi a kofar gidansu azaune akan wani banci, tasan aikinsu Saif ne wannan, a tsaye ta tsaya masa aka tareda sallama
Ya amsa mata cikin sakin fuska," My heart Rabin raina ya hanya?
"
Tace" lafiya "
" to Alhmdlh ido kuma sun bude Allah yaqara kiyayewa gaba, "
" amin ya Allah, wai Dan Allah Nuhu na tambayeka "
" inajin ki malama Nawal "
Tace" meyasa kake sona ne?
"
Murmushi yayi ya gyara zama" abu na farko shine kinada kyau, zaki dinga haifamin yara masu kyau kamarki, amma nafiso suyi kamarki kawai, jikin kuma saisu iyo nawa, kinga Ga kyau Ga tsawo kuma Ga qiba
, kuma masha Allah kinga nidin dama gentleman ne, saikiga ana layi a kofar gidana"
Cikin takaici tace" Nuhu saikace samudawa?
Kasan tsawonka kuwa?
Tsawo ne dakai Kamar daran mutuwa, ahakan za'ayi layi a kofar gidanka?