← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 48

Sashe 25

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"
Takardar ya wulla masa yace" nikam idon 'yan chaina nace ka zanamin ne?"
Shima yace" to ai yallabai, kwatancan nakane narasa gane kansa
ba madedetaba, ba qarami ba, ba Babba ba
Nawal dake gefe tana jinsu ta kwashe da daria
, sai qyalqyala daria take
Juyowa yayi yana Kallanta, aransa yace"ashe tana daria,
dariyar tamata kyau "
Saiya juya ya kalli Mai zanen yace" kasan qananun yara basu cika hankali ba, muci gaba da abinda yakawoka "
Mai zanen ya maida hankalinsa wajan zanen amma duk yanda yazana sai yace baiyi ba, sunyi haka yakai sau hudu, daga qarshe kawai dafe kansa yayi da hannunsa
yace" jeka na sallameka "
*** ***** ***
Da yamma tana kwance afalo tana karatun qur'ani a zuciyarta
sai ganinsa tayi yasauko daga d'akinsa, daga shi sai three quater, da rigar marar hannu, gefen hannunsa ta kallah taga anzane shi da wani zane irinna yan wrestling, kallo d'aya tayi masa takauda kai cikin ranta tace gayu mutanan Allah
Saida yazo dede kanta ya tsaya, yafara qwalawa sabon maigadi kira, cikin isa yafara cewa "Nuhu"
Amma maigadi baijiba, yasake cewa "Nuhu kai"
Da gudu yaqaraso har cikin falon, mata shi ne amma da alama yanada iyali
Kayan hannunsa ya watsa masa "dauki wannan Nuhu, maza maza kaje ka wankesu yanzu"
Cikin ladabi yace "to yallabai angama"
Yadebi kayan zai fita yasake cewa "kai Nuhu"
Nuhu yajuyo yace "na'am"
Yace"idan kagama wankin ka wankemin motocina gaba dayansu"
Yace "to yallabai"
Zai juya yatafi yasake cewa "idan kag
ama ma kaga compound din gidannan yayi datti kasa tiyo ka wankeshi gaba dayansa kajiko Nuhu"
Bawan Allah yace "to yallabai angama," yafice da sauri
Shikuwa cikin gadara yace "yawwa Nuhu, maza" sannan ya wurga mata harara yayi cikin dakinsa
Tashi tayi zaune tabishi da kallo, Wato da ita yake, shiyasa yaketa nanata sunan Nuhu, saboda jiya yaji tace dama Nuhu ta aura
Afili tace lalle ma mutumin nan, aikuwa Zan rama
*** ***** ***
Haka zaman su ya kasance har tsawo kwana uku, kuma kullum zata gyara masa gida ta goge, sannan bata denayin girki dashi ba, kullum sai tayi amma ba yaci
Haka ya tattara yawuce Dubai batare daya fada mata ba
Tafiyarsa tayiwa Nawal dadi, saboda tana shiga irin wadda takeso, Babu aiki kullum, ita kadai ce agidan saide ta gyara falo da Dakinta kawai
Har yayi sati biyu, Tun tanajin tsoro harta denaji
Ummi ta kirashi awaya, tace"Baffah shiru ake jinka katafi, yaushe zaka dawo ne?kasanfa yanzu kanada iyali, idan kasan zaaka dade haka aida saiku tafi tare, Pls yaushe zaka dawo?

"
" Ummi itace tace ai Babu damuwa natafi, tafison kusa dake "
" to koma de mekake kakamo hanya kataho gida,"
" to Ummi insha Allah "
Ummi tana kashe wayar saita kira Nawal domin ta tabbatar da maganar Baffah, tana kira bayan sun gaisa tace" yaya Baffah ina fatan yana lafiya?

"
Zuciyar Nawal daya tace" lafiya kalau wallahi Ummi, dazu ma yafice
Ummi ta jinjina kai tace toki gaishe shi
, daga nan sukai sallama
Shiru tayi tana tunani, haqiqa Baffah yayi sa'ar mata, amma ita kam sai du'a'i
Bayan kwana biyu Sultan ya kirata yace yashigo Abuja zaizo gidan nata, cikin murna ta tashi tafara yimasa girki Mai dadi
Lokacin dayace yazo unguwar da temakon Nuhu maigadi
yaqaraso
Cikin murna ta rungumeshi, shima cikeda murna yabata kayanda yasiyo mata, qananun kaya dakuma fruit
afalo ya zauna ta gabatar masa da abinci, yaci sosai, sannan tahada shi da Nuhu yarakashi gidan Ummi suka gaisa dashi sannan suka dawo gida
Sun dade suna fira, ya kalleta sosaai yace"Baby ki kwantar da hankalin ki, naga duk kin dan rame, kinga idan ummah ta tambayeni yana ganki ba zataji dad'i ba idan nace kin rame "
Damuwa ta bayyana a fuskarta tace" to yaya insha Allah "
Sai wajan yammah yace zai tafi, tara koshi yar bakin gate, futowa sukai daga gidan suna tafe suna fira, ya dakata ya kalleta" to Baby nah, kijuya kikoma gida, "
Idonta ne yayi raurau zatai kuka
Yace" au sai kinyi na gadon de
Da taga yana mata daria kawai saita fashe masa da kuka, tace" Allah yaya ni banajin dadin gidan nan"
"bayanta yabubbuga yace" kiyi hakuri kinji, wataran zaki saba, "yasa hannu ya share mata hawayen idonta
Karaf a idon mk da'aka daukoshi amota daga Airport, cikin sauri yaacewa direba" dakata "
Direba ya tsaya, saida yagama ganin komai, har zuwa lokacin da Sultan yajuya yatafi, sannan itama tashige gidan
Lalle yau yarinyar nan zata tattara tabar masa gida, ashe maza take kawowa idan yafita, wannan shine Nuhu, shine nuhun datake cewa sai yazo kenan
Kallan direba yayi, "mu qarasa direba"
Suna zuwa cikin gida yadauki jakar sa yashige ciki, direct Dakinta yawuce ya murda handle din amma yaji arufe
Alokacin ita kuma bata jishi ba tana toilet
Dakin sa yawuce, yafara hargitsa sumar kansa, ko masallaci bai iya fitaba, saide yayi sallar adaki
Zuciyarsa ce ta bashi shawara akan ya qyale yarinyar saboda gudun raini
Nan take yadau shawarar data bashi
Har dare yayi ya kwanta, Nawal batasan yazoba, saboda kawai falo tazo ta agyara, sannan tayi wanke wanke takoma daki
Tun karfe goma yakashe wutar dakin ya kwanta bacci, amma baccin ya gagara daukarsa
Kawai sune suke fado masa a idon zuciyarsa
Tsaki yasaki, to menene ma Zan damu Dan takawo saurayinta gida, nida ba sonta nakeba
Wata zuciyar tace dashi to meyasa kake kishinta?

Girgiza kansa yafara yi, wannan ba kishi bane
haqqin aure na nake karewa
Har shadaya tayi bai runtsa ba, yatashi yafara zagaya dakin yana tunanin mafita
Yakoma ya kwanta, daga qarshe de mk har qarfe daya na dare idonsa biyu yakasa bacci
Dirowa yayi daga kan gadon yana cewa "kai wallahi bazai iyuba, dole naje ta fadamin uban waye yace takawomin saurayi gida
Da gashi sai jallabiya, yasauko qasa, yana zuwa yatura kofar dakin yayi sa'ah abude take
Ganinta yayi tana bacci hankalin ta kwance, doguwar Rigace a jikinta ta bacci Mai Dan kauri, ta dauki fillo ta rungume, yanda ta rungume fillo din yasa nashanunta sake baiyana awaje
Kasa dauke idonsa yayi akanta
Yaqurawa Kirjinta ido yana kallo
Amma daya tuno yanda yaganta ta tsaya da wani, sai ransa yabaci
Fillo din datai matashi dashi, yafara bubbugawa "ke"
Bata tashi ba, yasake bugawa da karfi "ke, ki tashi nace"
Juyi tayi ta kalleshi da idanunta cikeda bacci, yanda ta kalleshin kadai yasa jini da jijiyar jikinsa de na aiki nawucin gadi
Ta yunqura ta tashi zaune tace "lafiya?"
"biyoni"
Ta shi tayi tasaka hijabi tabiyoshi abaya
Taga yanufi harabar gidan itama ta doru abayansa
Wajan motarsa sukaje, yabude Mota yace "shiga"
Ta shiga ta zauna tana cewa ikon Allah, karfe daya da na dare ko Ummi
ce Babu lafiya?

Shima shigowa yayi yaja motar aguje sukabar gidan, ya dade rabonsa da driving, haka yake sharara gudu akan titi
Tajuyo tadubeshi tace "ina zamuje ne?"
Fuskarsa atamke Babu alamun Fara'ah yace "kezan tambaya, kifadamin inane gidan sa yake?"
(tofa
kishi yakama maza)
Sharhi please
Mrs Usman ce
[2/3, 11:35 PM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Banyi tunanin NI DAKE yanada masoya hakaba,yau wannan labari yasa nasamu alkhaairi ta yanda zansai data inci gaba da posting abina
, wannan shafin nasadaukar dashi ne ga cmrd Abdul Bauchi, Allah yabar zumunci
27&28
"gidansa yana kano"
Wani irin wawan birki yataka, kanta yasake buguwa da jikin kujerar datake zaune saboda batasa belt ba
Cikin masifa yace"ina fada kina fada "yafuto daga cikin motar, ya zagaya yabude mata gefen datake zaune yace" Futo"
Tajuyo ta kalleshi tace "ina Zan sauko?"
"kifuto kije gidansa, gara kikoma can dazama akan kidinga kiransa yana shigomin cikin gida"
Ta kalleshi, tasake kallansa dakyau "acikin wannan tsohon daren Zan futo daga cikin motar nan?

Inje ina?

Ina bacci katasoni kafuto Dani wannan wajan, Dan haka saide kamaidani"
Qugunsa ya riqe yace "Owwk, yanzu kuwa Zan futo dake, tunda ke wuyanki yayi qwari, bakida mutunci bakida tarbiya mijin ki yana fada kina fada, to yau kuwa NI DAKE dan halak kafasa" yana kaiwa naan yasa hannunsa yafusgota daga cikin motar, cikin sassarfa tafuto daga cikin motar tasaki qara saboda ta saddaqar ma tafadi aqasa
dasauri yasake fuzgota jikinsa ganin zata fadi, sai gata tafada saman Kirjinsa
Kuka tasaki Mai ciwo,tasake qanqameshi, sosai take rinza assala akan qirjinsa, hawayenta yana sauka ajikinsa, shikuwa yaqame yakasa aikata mata komai
Rigar dake jikintace ta bashi damar jin albarkatun qirjinta anasa, wani irin yanayi yajishi aciki, saboda duk matan dayake runguma bayajin hakan
Saukar hannunsa Nawal taji agadon bayanta, alamun sake rungumeta yayi
Kuka taci gaba dayi cikin kukan tace masa "yaya nanefa, dsme fathr and mothr"
Lokaci daya kunyar kansa ta kamashi, toda mema yakai shi aikata hakan?

Shiru yayi yakasa magana saboda aida kunya yace jinake Nuhu ne
Akaro na farko, sai gashi yafara bubbuga bayanta alamun rarrashi
Amma yakasa cemata komai, kuma yakasa rabata da jikinsa
Asalima daga bubbuga baya saiya sake matseta ajikinsa, ga motoci agefen titi d'aid'aiku suna wucewa
Jin yayi baya Kamar zasu fad'i yasa tayi saurin kallansa, shima Kallanta yayi ayayinda qafafunsa suka kasa daukarsu
Ahankali tafara zare jikinta daga nasa, shima bai hanata ba,motar tashige tareda rufowa,shima cikin rashin kuzari yashiga yaja motar suka fara tafiya
Babu wanda yace da dan'uwansa komai har suka qarasa gida
Nuhu yana zaune idonsa biyu, Dan yasan idan ya kwanta ma zasu dawo
Bude musu yayi suka shigo, yana tsayawa tabude motar tafice, cikin ranta tana cewa Allah yayayewa Baffah masifa, cikin dare tsabar bala'i
Shikuwa bayanta yabi da kallo yana tuna yanayin da yajishi ciki dazu, zaiso kasancewa cikin wannan yanayin akoda yaushe, but idan kuma yaci gaba da hada jikinsa da yarinyar ai Kamar yaci amanar Baby ne
Da wannan tunanin shima yayi ciki, sai a lokacin yasamu damar bacci
(yanmata Allah yahadaku da masu sonku na gaskiya masu kishinku)
*** ***** ***
Washe gari saida ta makara wajan aikin gida
Sai wajan karfe tara ta gama komai sai mopping datakeyi, taga ganinsa yafuto daga d'akinsa, cikin sauri tace masa "ina kwana"
Saida yaja wasu second sannan yace"lafiya, "
Yakalli Agogon hannunsa yasake cewa" karfe nawa yanzu?
Chapter 25 · 0% Book details