← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 48

Sashe 2

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gwamnati ahannun mu take, kowa yayi laifi katakashi,"
Tace "amma alhaji..."
" _but_ _what_ hajiya?

Kinga ni yanzu Zan wuce _Kuwait_ , akwai _meeting_ din da zamuyi gobe da yaron uban gidanmu, ya kalli dansa yace _my_ _son_ , jeka shirya mutafi tare, sai kasha iska kafin nagama abinda yakaimu, inkuma wata qasar kakesan wucewa saika wuce tacan
Cikin shagwaba yace " _dad_ gaskiya babu Inda zani, akwai _birthday_ _friend_ dinmu da zamuyi goben
Cikin rashin damuwa yace" toshikkenan _my_ _son_ kaje dakina akwai kudi a _bedside_ _drower_ kadauki abinda yama
Tsalle yayi gami da rungume uban yayi cikin dakin dagudu
Girgiza kai hajiya tayi tace "to alhaji kwana nawa zakuyi"?

Yace "2 to 3 _day's_ insha Allah"
"to Allah yadawo daku lafiya Alhaji"
** *** **
Hudu da kwata suka futo daga _lacture_ dasuka shiga, ta dubi aminiyar tata tace "besty saimun hadu gobe, yunwa nakeji wallahi Ga bamuyi sallah ba,"
Tace "Beauty nima nagaji wallahi, saimun yi waya kawai"
Daganan sukai sallama kowa yashiga adedeta yawuce Gida
Saida suka dau hanyar Gida, abinda yafaru dasafe yafado mata arai
Tsoro ne yakamata, cikin ranta tace "Allah ka rufamin Asiri kasa wad'ancan sakarkarun basa nan"
Tana cikin wannan zulumin aka sauketa abakin titin, ta bashi kudinsa sannan tayi cikin layin nasu, wannan tafiyar datake Ahankali denawa tayi, taware qafarta tana zuba uban sauri
, hartazo wajan dasuka tareta da safe, amma tsabar tsoro tama kasa kallan wajan, yayinda gabanta yaketa lugudan faduwa, sai tafiya take fiya-fiya hartazo wajan dayake da yalwar mutane
"laaaa Affan kaga wasu baqaqen motoci masu kyau, daya, biyu, uku, hudu, biyar, shida, bakwai, takwas, tara...

Laaa affan wallahi guda goma ne"
Wanda aka kira da affan ne yakalli motocin nan take ya nuna guda daya yace "nida wannan"
Shima dayan yace "wallahi baka isaba na rigaka, wannan tawace
Ko juyowa batayi ta kalli wadannan yaran dasuke fira abayan taba bare ta kalli motocin dasuke magana akansu, fatan ta daya shine taganta agida ta rama sallar datake kanta
Wani me mashin ne yashawo kwanar aguje, baisan tana gabansa ba,gadan gadan yayi kanta, ita kuma batajiba saboda hankalinta gaba daya yayi Gida
Kasancewar kowa yasanta a unguwar, kuma ansan cewa itace ma'abociyar wannan shigar shiyasa wadannan yaran na bayanta suka dora hannu aka, cikin kaduwa da qara suka hada baki wajan fadin " YAYA BABY bayanki!!!"
"bayanki yaya Baby!!!"
Lokaci daya me _machine_ din yataka wani wawan birki, jikake quuuuu
Adede lokacin daya daga cikin _Escort_ dinsa yabude masa kofa yafuto, yayi bala'in kyau cikin farin yadi, had'eda babbar riga, yanda yaci manyan kaya zaka iya rantsewa wani Babban magidancin ne, fari ne tas, kallo daya zaka masa kashaida cewa shidin cikakken bafulatani ne, zagayaiyen sajen daya bari a fuskar sa, shine zaisa dayawa daga cikin mutane zasuyi masa kallan wani balarabe ne.
duk abinda yake faruwa akan idonsa
Duk yanda taso kaucewa saida mashin din yabigeta kad'an, tai wani irin juyi, niqab dinta yadage har zuwa wajan hancinta
Tace "Wayyo" saigata da'bar aqasa
_Pink_ _lips_ dinta sirara masu kyau yabi da kallo, yanda ta motsa bakinta tace " _wayyo_ " dinnan shine yafi komai daukar hankalin sa, cikin ransa yafurta kalmar " _Cutie_ "
Dama a _Nigerian_ yankin Arewa akwai irin wadannan yaran masu kama da jinsin larabawa?

Duk da baiga _face_ dinta dukaba yasan cewa Allah yayiwa yarinyar baiwar kyau
Ita kuwa tashi tayi tana karkade jikinta, me mashin din yace "Qanwata Dan Allah kiyi hakuri, wallahi ban kula bane, kiyi hakuri dan Allah"
Dagowa tayi daga kad'e jikin nata tace masa "babu komai wallahi, ai banji ciwoba,"
Tana fadar haka taci gaba da tafiya,ance juma'ar dazatai kyau tun daga laraba ake ganeta, ita kam tasan cewa yau bata futo a sa'ah ba
Me mashin yafara buga abinsa zai tafi, shikuma yana tsaye yana kallan ikon Allah, kakade mutum ba dabba ba, amma kabarshi yatafi, ai kamata yayi ka tsugunna har qasa kabata hakuri
,, inta baka damar tafiya shikkenan saika tafi, Dan haka cikin sauri yafara cewa "ka dakata!"
Amma inaaaaa, baijishi ba,binsa yafara yi yasake cewa "nace ka dakata", amma tuni me mashin yayi gaba abinsa, to dama maganar ce gata Ga yanda take, ba'a qwala da karfi yanda za'a jiba, mukuwa mun saba sai an bude mana murya
Daya daga cikin _guard_ dinsa ne yabiyoshi "yallabai kana san magana dashi ne abishi adauko shi ?"
Yace " _no_ " tare dakai dubansa inda yarinyar take, 'bat ya nemeta yarasa babu ita babu alamar ta
Cikin ransa yake cewa "wacce irin yarinya ce wannan me hakuri?

Ankadeki amma ko ajikinki kitashi kici gaba da tafiya, yanzu Data tsaya aida sunje _hospital_ aqalla ko lafiyarta ne aduba
, amma tayi qanqanta da daukar wannan _Prager_ din tayi qarama dayawa
"yallabai ga lungun dazamu shiga can, anan gidan yake"
Juyowa yayi ya kalli Wanda yayi masa maganar sannan ya kalli lungun
"wai kana nufin wannan wajan zamu shiga?"
"sai hakuri yallabai, anan gidan yake,"
Babbar rigarsa yafara tattarewa Kamar Wanda zai tsallaka ruwa
sannan yace " _Ok_ " yayi gaba sukuma suka take masa baya, sai zare ido suke suna kalle-kalle
Kofar gidan dasuka nufa acike take da mutane kowa yana zaune a tabarma anyi shiru
Suna zuwa yacire takalminsa fari qirar italy,sannan yafara bawa mutanan wajan hannu suna gaisawa daya bayan daya
Matsawa yayi wajan wani dattijo suka sake gaisawa cikin girmamawa yace "yaya qarin hakurin mu?"
Mutumin yace "hakuri sai ma'aiki,"
"Allah yaji qanta, Allah yasa tahuta"
Yace "Amin Amin, MUHAMMADU ne yaron wajan Alhaji KABEER ko?

Saida yayi qasa da kansa sannan yace" eh nine baba "
Mutumin yace" ikon Allah, kaduba kaga yanda Muhammadu yagirma yayi hankali, Muhammadu ashe zamuga wannan ranar?

Kawai saiya fashe da kuka yaci gaba da cewa Allah yajiqan Alhaji Kabiru, Allah yakai haske kabarinsa, ubangiji Allah yasa can tafi nan, oh, mutum Mai taimakon takalawa, Mai basu gudunmawa...

Mutanan wajan ne suka fara bashi hakuri, sannan yagoge hawayen idonsa yace "nagode sosai Muhammadu"
Shima Ahankali yace "babu komai ai baba, yiwa kaine, yasa hannu a aljihun Babbar rigarsa yadauko kudi masu yawa ya ajiye agaban mutumin" Ga wannan ayi mata sadaka, Allah yaji qanta, "
Atake duk wajan suka amsa da Ameen
Yayi musu sallama yatafi, muqarrabansa na take masa baya, kana ganinsa kaida kanka zaka tabbatarda cewa shidin wani me fad'a ajin ne a wannan qasar, suna zuwa wajan dasukai Parking motocinsu aka bude masa domin yashiga, kafin yashiga saida yasake kallan wajan da aka kad'eta kozai sake ganinta, amma shiru kakeji
Wani daga cikinsu ne yalura dashi, cikin sauri ya qaraso gamida rissinawa yace "yallabai ko akwai damuwa ne?"
Bece masa komai ba, kawai girgiza kansa yayi alamar babu, sannan yashiga suka rufe, sun fara tafiyama amma sai waiwayen wajan yake
Sunyi nisa sosai Ahanya, driver yajuyo yace" yallabai ina muka nufa?

"
" kashiga wancan layin, akwai Wanda nakesan gani "
Umarninsa _driver_ yabi, suna zuwa wani kofar Gida yace" ya'isa"
Wasu samari ne guda biyu azaune a kofar gidan, gaba daya suka maida hankalin su kacokam akan motocin dasuka tsaya
Ana bude masa yafuto, Dasauri daya daga cikin samarin nan yamiqe tsaye yace "wanake gani Kamar MK"
Shima cikin mamaki yace "yasir kaine ka koma haka?nayi tunanin kun tashi daga gidan nan ashe har yanzu kuna nan? _But_ yasir meyake faruwa hak...

Dasauri yasir yakatse shi" labarin yanada tsawo , mushiga ciki mana, na barka a tsaye "
" _no_ yasir, ina kan hanya ne, _latter_ zamu samu lokaci mu tattauna, dama kawai ka fadomin ne naji ina san ganinka, wanne aiki kakeyi yanzu?
Chapter 2 · 0% Book details