← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 48

Sashe 14

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shine nace saide na tambayeka tunda kunyi tafiya zuwa germany kaida abokinsa, ko zakasan wani abu daya danganceshi?"
"eto gaskiya abinda nasani shine naji abokin nasa yana fadawa qaninsa cewa shi mk din Dan Adamawa state ne, cikin garin yola, amma yana zaune a Abuja, saide mafi yawan harkokinsa yana gudanar dasu ne a qasar Dubai, amma baya cikakken sati biyu baizo Nigeria ba, maganar waya kuwa naaji yana cewa sai ranakun aiki yake amsa waya
, idan ba week day neba baya amsa waya saide in shine ya nemeka "
Yace" to shknn mungode, sai anjima "
Yana kashe wayar yadubesu yace" to kunji,"
Murmushin yaqe Nawal tayi" tace toshknn likita mungode, insha Allah zamu fadawa abban, ngd "
Yace" toki gaishe shi nagode sosai "
Fitowa sukai daga office din jikinsu a sanyaye, ta dubi Nas tace" Nasrin mutumin nan yafi qarfina, sai hawaye sharrr "
" haba Nawal, ya zaki karaya Tun yanzu?

"
" Nas kinajifa abinda akace akansa, yana wata qasa, idan yazo Nigeria ma sai Abuja, nida ko hanyar Abuja ban taba biba"
"ki kwantar da hankalin ki nace, akwai bikin wata yar'uwarmu da za'ayi a Abuja, zamuje bikin, kawai ina ganin ki shirya mutafi tare, insha Allah zamu hadu da shi"
Hawayen idonta tashare, "Nas kina ganin babu damuwa kuma agida za'a barni?"
"mezai hana, zanzo gobe da kaina nayiwa umma da Abba lissafin karya kawai saimu wuce
"to shikkenan Nas saikinzo"
Haka suka futo daga asbitin tana qara kwantar mata da hankali
*** ***** ***
Tana zuwa kofar gidansu taga yashi dasu siminti dayawa an jibge, Data shiga gidanma duk suna nan atsakar gida tayi sallama tareda cewa"umma nadawo, ta kalli mama mariya tace mama nadawo "
Atare sukace to sannu
Hijaabin jikinta tacire taja kujera ta zauna tana cewa wash Allah, Saif daya futo daga daki yaja ribom din kanta, kasancewar babu kitso sai gashin nata yazubo agadon bayanta yace" yaya Baby yalasha "
" Saif banaso, inba idaan aljannu na suka tashi ba zakaji dadiba "
Yace" yasin su tashi, muda muke da Malam "
ta kalleshi tace "ina Najma?"
"tana daki tana Zumba"
Cikin sauri ta tashi tace"a a nima natafi "ta shige dakin mama mariya
Wata tsohuwar computer Salisu ce agabanta ta qure wakar zumba tana gani tana rawa
Itama kuwa ta shige sukaci gaba
(zumba wata rawace da masu qiba sukeyi domin motsa jiki, idan kana yawaita yi qibarka zata ragu, idan bakada qiba kuma tana qara futowa da mutum shape dinsa musanman mata)
Har wajan azahar suna abu daya, sannan sukaje sukai wanka saboda gumi dasuka hada
*** ***** ***
Washe gari kuwa Nasrin tazo gidan, da Abba tafara haduwa a kofar Gida shi da masu aiki suna kwaba siminti, ta gaishe shi ya amsa mata, tace Abba dama wajan ka nazo kaida umma "
Cikin mamaki yace" to inajin ki me yafaru, Allah yasa de lafiya, "
" Abba dama biki zamuje Abuja nidasu mamata, shine mama tace nazo na tambayeku tanaso mutafi tareda Nawal "
Nasrin Allah ya hore miki)
Abba yayi jim yana tunani sannan yadubeta" to kwana nawa zakuyi?

"
" kwana biyar "
Yace" to shknn Babu damuwa, idan tafiyar ta tashi saiki zo kutafi "
Cikin murna tace" to Abba mungode, daga nan ta shige gidan, tana bawa Nawal labari tahau murna tana kuma fata Allah yahadata dashi
Saida Nasrin tawuni sannan tatafi Gida
Cikin satin kuwa tafiya ta kankama
, Umma tace nide Baby ki nutsu karkije ki dinga yimusu sakarci agida, sannan kuma kidinga saka kayan mutunci banda zama da qananun kayan nan"
"to umma insha Allah, Abba yazo har dakin yabata dubu sha biyar, ta karba tana godia shikuma yafice umma ma tabi bayansa, Najma ce tashigo dakin tace" Baby mutanan Abuja,
yau kuma sai Abuja "
Tace" wallahi kuwa, Abuja Kamar munje "
Najma ta kwashe da daria," to yaushe ita Nas din zatazo?

"
" tacemin tana hanya, zatazo mutafi, amma sai munje gidansu, da yamma kuma zamu dauki hanya "
Najma tace" to mude tunda munbaki shawara kinqi dauka bamace komai ba "
" Najma kekike nufi?

"
" A a Babu abinda nake nufi Baby, kuda zakuje kusha biki, amma inaso kisani Tun muna yara tare muka taso dake, banda umma Babu Wanda yasan halin ki sama Dani, haka kema kinsanni kinsan abinda Zan iya da Wanda bazan iyaba, saboda haka Babu abinda zaki boyemin nakasa sani, "
" aikuwa wannan karon tunaninki bai baki daidai ba "
Cikin daria tace" to Baby, adawo lafiya, Wanda baiji bari ba yaji hoho
, idan kin hadu dashi kice yayarki tana gaishe shi "
Daga haka tafice daga dakin, ita kuwa ko a jikinta kayan ta ma taci gaba da shirya wa cikin jakar da zata tafi da ita
Da yamma suka dauki hanyar Abuja itada Nasrin dakuma wani qanin Nasrin din, sunata firarsu amota
Har Allah yasauqesu lafiya
Gidan yan'uwan su Nasrin din suka sauka Inda ake hidimar bikin, matar tanada faram faram Babu ruwanta, daga nanfa aka fada harkar biki, koda batada niyyar kwalliya Nasrin ce take sakata dole taayi, aikuwa sosai suke zuba kyau abinsu duk Inda suka wuce sai ankallesu musanman Nawal
Kwanansu biyu a Abuja Babu wani labari, nanfa tadaga hankalin ta, ta shiga damuwa, Nas tace "kiyi hakuri beauty insha Allah zamu ganshi kafin mubar garin nan"
Tace "toshknn Nas Allah yasa"
Washe gari za'ai dinner haka sukaci kwalliya, matar Data yiwa amarya itace tayi musu daidai misali
Aikuwa sunyi masifar yin kyau
Suna zuwa wajan dinner aka farayi cikin kwanciyar hankali
tadubi Nasrin tace "Nas nagaji da zaman nan wallahi, bari nadan fita nadawo,"
Tace mata" to beauty "
Tana fita wajan kuwa ga motoci nan birjik, ta jingina ajikin wata Mota
gawasu maza nan agefenta kusan su hudu suna firar su
Wani bawan Allah ne yaqaraso wajan ta yace mata " hi"
Kallansa tayi kawai batace komai ba
Yasake cemata "Baby girl mekike jira ne anan wajan ke kadai?

Be kamata mata kyawawa irinku sudinga zama su kadai ba"
Tace masa "ko?"
Yace "sosai ma kuwa, ga motata can, mezai hana kishiga Muje ko shisha ne musha mudawo kafin agama dinner"
Zaro ido tayi
, cikin ranta tace"nashiga uku shisha?

Gabanta yafara faduwa, gatada tsoro
Amma afili sai tace "A a nagode"
Yace"fine, to nide nagani inaso "
" kayi hakuri bawan Allah ansamin rana, wani watanne ma bikina "
Cikin rashin damuwa yace" to shikkenan, Babu damuwa, bye "
Bayansa tabi da kallo, oh akwai tantirai aduniya, Allah kaqara tsare mana imaninmu"
Wasu motoci ne guda uku baqaqe sukazo wucewa ta wajan, ba wani gudu suke sosai ba, mazan nan na gefenta ne taji wani daga cikin su yace " kace akwai harka, MK Yashigo gari kenan"
Gabanta ne yafara faduwa, tabi motocin da kallo bakinta yafara rawa wajan furta m.m...mk
Wani daga cikin su yasake cewa "ai mk yayi a rayuwa, kana ganifa duk samarin nan na unguwar su daya bayan daya ya nema musu aikin yi"
Wani kuma yace "nifa naji ance wallahi ba qaramin Dan shaye shaye bane"
Na hudun kuma yace "dalla Malam ware, kawai hassadar mutane ce, inde anga kanada shi yanzu za'a fara cemaka manemin mata, Dan giya, Dan ta'adda"
Kanta ne ya kulle, tarasa abinyi, kawai saita doru abayan motocin tana binsu cikin sauri, wayar ta tad'auka takira Nas tace "Nas futo futo, futo Nas ga mk can, futo futo Dasauri Dan Allah"
Ai afujajan Nas ta futo
tana waigawa damanta sai hango Nawal tayi tanabin wasu motoci Dasauri, itama kawai saita fara binta da Dan gudu harta tarota
Adede lokacin saiga wani me adedeta, Nasrin ce ta tsaida shi, yana tsayawa kuwa Babu neman excuse suka fada ciki, Nawal tace "Muje Muje Dasauri kabi bayan wadancen motocin pls "
Hajiya kuyi hakuri, doka tahana adedeta haya agarin nan, nima yanzu satar hanya nayi nafuto, amma idan aka kamani kulleni za'ayi"
Nasrin tace "Dan darajar Allah karuf
a mana Asiri, Muje Dan Allah, Babu abinda zai faru "
Cikin faduwar gaba yaja adedeta suka fara tafiya, Nawal kira take "kaqara sauri mu tarosu pls Malam"
Hajiya saide kuyi hakuri ina hawa Babban titi kamani za'ayi, saide mubi ta qasa
Nasrin tace "koma ta inane Muje, mude fatanmu mutaro motocin kawai"
Aikuwa saiya qara gudu sosai , kasancewar hanyar akwai gargada ana sabunta titin ne, me adedeta yaci karo da wani rami sai kiyaaaaa adedeta tafadi
Agefen da Nawal take zaune Agefenta adedetan yafadi, Nasrin tafad'o kanta
Aikuwa sai suka dauki ihu da kururuwa Nasrin tace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, jama'ah akawo dauki
Ita kuwa Nawal sai ihu take tana" cewa wayyo nashiga uku hannu na, na mutu na lalace
Mutanan dasuke gefen titi ne suka taho aguje aka kawo musu dauki, aka samu aka dago adedetan, Nasrin tafuto, ita kuwa Nawal sai ihu take saida aka zarota
Sannan shima me adedetan aka bashi temako
Gaba dayansu sunyi tsumu tsumu agefe Nasrin na kuka Nawal na kuka
Babu Mai rarrashin wani
Maganar Najma ce tafado mata, gaskiya ne Wanda baiji bari ba yaji hoho
Wani yace "yakamata kuje asbiti, me adedeta yace" a a Babu komai shi baiji ciwo ba, ya kallesu yace "saide yanmatan "
Suma suka fara girgiza kai, Nawal tace bamuji ciwo ba, hannu nane de yadan bugu idan naje Gida Zan dindima da Ruwan dumi
Wani yace "inane gidanku amaidaku gida?

Nasrin tace" can hakane gabas "
Wani yace" ikon Allah, yarinya a tambayeku gidanku kice gabas, a a yamma ba gabas "
Wanda yace zai kaisu gidan ne yace" zaku gane hanyar?
Chapter 14 · 0% Book details