← Book details Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 48

Sashe 21

Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acikin satin Ummi tazo kano, Umma tana ganin ta ta karbeta a mutunce
Abba yakira Malam awaya, ba'a dauki lokaci ba Malam yaqaraso
Nawal tana dakin mama mariya itada Najma, tunda taji baquwar rannan tazo takasa fita saboda gani take kowa haushin ta yakeji, bayan batada laifin komai
Malam yadubi Ummi bayan sunyi gaishe gaishe yace"baiwar Allah kinzo garemu da Babban al'amari, gashi kuma mu munyi bincike mungano cewa yaron wajan ki har neman mata ma yanayi,
ga kuma shigar dabata daceba, kinsan kuma ba kowanne ubane zai iya daukar yarsa yabawa irin wannan yaron ba "
Ummi ta jinjina kai tace" Baba nasan d'ana, shi yasa Tun farko ban boye muku ba nafada muku cewa bayaji, nasan cewa yana saka kayaiyakin dabasu daceba, amma neman mata kaam bayayi, Inda yanayi Tun farko bazan boye muku ba, akwai qanwata uwa daya uba daya, itace tabani shawara namasa aure zai daina irin wannan shigar da temakon matarsa, nikuma nayaba da hankalin 'yarku, uwa uba tanada hakuri, shikuma d'ana yanada tausayi, nasan cewa da temakon ta zansamu Allah ya shiryamin shi, yana fita wasu qasashen yana ayyuka yanzu hakama bayanan,kuma banaso yasan da maganar auren, nafiso kafin yadawo ayi musu auren,
to kaga baba bazai iyu duk Inda yaro zaije nadinga binsa ina ganin me yakeba, amma itaa matarsa dole duk Inda zaije tana tare dashi, kuma idan taga yayi ba daidai ba zata tsawatar masa
, bayan neman aure harda neman alfarma nazo akan kuban 'yarnan taku Dan Allah, saboda inasonta har cikin raina Kamar d'ana, sunan yaron nawa Muhammad Kabeer ammma ina kiransa da Baffah, saboda sunan babana yaci "
Malam yayi ajiyar zuciya yacemin" to munji baya nanki, kuma insha Allah duk abinda muka yanke zamu sake tuntubarki "
Tace" to nagode baba, bayan kunyi nazarin, idan kun amince inaso adaura musu auren ad'an qanqanin lokaci ,banaso ayi wasu bidi'a saboda albarkar auren kawai muke buqata, idan kuma baku amince ba daan Allah karku boyemin kawai ku sanar Dani, ina nan ina jiran wayar taku "
Daga nan sukai sallama da ita tatafi, Malam yadubi Abba yace" akira masa Nawal," Umma taje da kanta ta kirata
Malam yadubeta yace"Nawal, kwanaki anzauna dake akan zaki kawomin Wanda kikeso, kin samo wani?

"
Jijjiga kanta tayi, gaabanta na faduwa
Malam yasake cewa" to yanzu Nuhun za'a baki?

"
Hawaye ne suka zubo mata,zancen zuci tafara, karfa naje ahad'ani da mutumin da ban saniba daga qarshe nazo ina DANA SANI, bayan kuma BURINAH a rayuwa shine mk, to shikuma mk ya gujeni bare inyi tunani tsakanin shida Nuhu WAZAN ZABA?
inama ace zan zamo SHALELAN MK wata rana?

Haqiqa danaji dadi arayuwata
Ahankali ta girgiza kai alamar a a
Yace" to shikkenan tashi kije sai abaki wannan bawan Allah da matar nan tazo da maganar sa "
Kuka tasa musu tace" Malam wallahi bana sonsa, banfa sanshi ba,
Dan haka karku bani shi "
Malam yace" Nawal auren wannan yaron Kamar jihadi ne zakiyi, ni kaina abin alfahrina ne ace jikata ta shiryar da wani, tashi kije Allah yamiki albarka"
Daki tashige take kuka tuquru, yanzu shikkenan Babu mk, wacce irin qaddara ce wannan?

Ita tana haukanta ashe bama mk din zata aura ba, wanine daban, tayaya zata soshi?

Inaa bazai iyuba, bazata iya sonshi ba
Acikin satin Abba da Malam suka fadawa Ummi cewa sun amince, kai tsaye tatafi yola tasamu danginsu maza ta turasu akayi komai aka gama Kamar yanda al'ada ta nuna, aka saka ranar biki kwana kusa, haka gida suka fara shirye shirye aka sanarwa da dangi na kusa bikin Nawal ya matso, anty maryam batayi qasa a gwiwa ba tataho, Umma ko kallan Nawal batayi, anty maryam ce take mata komai, amma cikin ranta tausayi ne fal na 'yar tata
Najma tayi rarrashi harta gaji, abubuwan tsumin da anty maryam take bata batasha, zuwa take tazubar dashi, Data gano haka sai take tsayawa akanta sai taga tasha komai
Abubuwan datake sha yasa jikinta yayi kyau,ko'ina yaciko yayi bulbul musanman Kirjinta, Kamar zai tsolewa mutum ido
Jiki kaam yayi kyau har ya gaji amma zuciyarta Babu dadi
Cikin satin mutanan yola sukazo da sadakinsu ahannu, aka daura auren Muhammad Kabeer, tareda matarsa Nawal Muhammad lawan akan sadaki nera dubu hamsin Kamar yanda Ummi takeso
Sannan suka sake bawa iyayen amarya hakuri kan rashin zuwan Ango, baya qasar idan yadawo zaizo tareda amaryarsa tanuna masa yan'uwanta, amma yanzu yarinya kawai suke buqata, basa buqatar akaita da Komai
Duk yan unguwa kowa saijin labarin auren Nawal yayi, saboda bakowa ne yajiba
Aranar kuma suka dauki amarya, a lokacin da zasu tafi ta qanqame ummah, ita kanta umman kuka take sosai, Najma kuwa daki tashige ta dinga rasgar kuka
Malam ne da kansa yayi mata nasiha Mai shiga jiki akan biyaiyar aure, kuma yanemi tayi masa alqawarin zatayiwa mijinta biyaiya, atake ta dauki alqawari
Yan'uwan umma da Abba mutum biyar ne sukabi amarya, sai anty maryam da Salisu, Sultan yace zaije daga baya
Sunkai amarya lafiya, sun samu tarba Mai kyau, tunda su kaga gidan suka tabbatar ba qaramin gida Nawal tajeba
Kai tsaye Ummi tace akai mata Nawal cikin Dakinta su zauna tare kafin mijinta yadawo, duk lokacin da yadawo qasar saisu shirya d'akinsu dakansu irin yanda sukeso
Washe gari tasa aka musu komai suka dawo gida ta jirgi
Sauran yan'uwanta da sukazo daga yola suma duk sun koma, tunda ba wani event da za'ayi
*** ***** ***
Da yamma Nawal na dakin Ummi tana sallah, bayan ta idar tayi addu'ointa tashafa, tafada duniyar tunani, Allah sarki ummah, kome Najma takeyi yanzu?

Hawaye suka zubo mata, tashare
Turo dakin Ummi tayi tashigo Tace"Nawal tashi mukoma falo mana, banaso kina yawan tunani fa, kid'aukeni Kamar ummanki kinji?

Ahankali tace "to Ummi"
Futowa sukai falon, Nawal de tanata ganin tsarin gidan wannan uwar tv din kadai ma ta isa kagane cewa ba qananun mutane bane
Zazzabi yanaso ya rufeta saboda bata saba da esi ba, gara gara de fanka
Ummi na lura da ita tace "meyake damunki?"
Ahankali tace "zazzabi nakeji kad'an"
"subhanallah, bari narage wannan esin saikici abinci kisha magani ki kwanta, Baffah baya nan dasai yamiki allura ya iya sosai"
Amma bari na kirashi nafada masa yana da patient
Wayarta tadau ta kirashi bugu daya yadauka"Baffa yaushe zaka dawone?

Kanada maraar lafiya "
Gabansa ne yafadi yayi zatan itace batada lafiya" Innalillahi Ummi meyasameki?

"
Tace" kaga nide kawai kataho inason ganinka "
Daga haka takashe wayar
Nawal dake gefe Cikin ranta tace "tofa nikuma nashiga uku, banzo bama ana ban labarin baffa inaga nazo kuma
Abinci taci tasha magani, ta kwanta, har dare de bata wani sake da Ummi ba, har washe gari, taji zazzabin nata yasauka
Harma ta gyarawa Ummi 'Dakinta, wdrb d'in da Ummi tace tabude akwai kaya aciki tasaka, shita bude tasaka wata doguwar riga ready made, rigar tamata kyau, sannan tafitar mata da shape
dinta, shafaffan cikinta ya kwanta, hips dinta yasake futowa aciki, amma batayi batayi kwalliya ba, sannan tafara goge mata dakin
Ummi na falo kawai sai ganinsa tayi yashigo hankali tashe
Cikin murna tace "oyoyo Baffah nah, sannu da zuwa,"
Zama yayi akan kujera jagwab yadafe kansa
yace "yanzu Ummi fisabilillah , kinsan qalau kike shine kika tasoni?"
Cikin Murmushi tace"to yanzu bagashi naganka ba, dama akwai maganar danakeso muyi dakai "
Kafin yayi magana ta d'aga murya tafara kiranta "Nawal!

Nawal!

'yata Nawal
Cikin ransa yake fadin Ummi da kwashe kwashe take wallahi,kowa ta kwaso harta bata iznin shiga cikin dakinta?

"ya kalleta yace" Ummi kinyi Sabuwar mai aiki ne?

"
Kallansa tayi tace" A a, ba Mai aiki bace, Matarka ce Baffah, aure namaka ai "
Cikin sauri yazabura yamiqe tsaye yace" wai wanne Baffan kike nufi ne?

"
Mutara zuwa gobe
(kullum de maganar guda daya itace hakuri, mudinga hakuri da junanmu yan'uwa, sai kaga Allah ya azurtaka ta Inda baka taba zatoba, idan kukai dogon tunani zaku gane cewa Shifa Anwar Kamar alkhaairi ga Rayuwar Nawal, yayi mata cin mutunci tayi hakuri ta dauki qaddara daga qarshe ga abinda hakurin yajamata, Sanadin ta yan'uwan ta zasu shiga makaranta, still sunyi karo gashi de shine da laifin amma itace ta bashi hakuri, Sanadin hakurin gashi Allah yahadata da mahaifiyar mk cikin Ruwan sanyi, itafa duniyar nan idan kayi hakuri ka dauketa asannu wallahi zakaga daidai arayuwarka, abinda nakeso mutane su gane har nake wannan haqilon typing din wallahi shine fa'ida da amfanin hakuri)
Masu cewa nayi 2pages kuyi hakuri, duk Wanda kukaga anyi muku posting dinsa to aranar na zauna na rubuta, bazai iyu nayi sau biyu ba, mu lallaba ahakan de
Sharhi sharhi pls
Sorry Nuhu kaban tausayi wlhy
Yaya zaman mk, Baby, da Ummi zai kasance? kubiyoni
Amnah El
[2/2, 1:47 AM] Amnahelyaqoob:
NI DAKE
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
23&24
Cikin ransa yafara cewa "wallahi sak irinna Baby, to kode sunada wata alaqa ne?"
Wata zuciyar tace masa Babu wata alaqa, yawancin fararen fata haka bakinsu yake, Ahankali yatashi, still bai daina Kallanta ba harya fice daga dakin
(nikam nace da sannu
Yana zuwa falo Ummi tace" dafatan kayi mata addu'ah?

"
" eh nayi mata saida safe "bai jira amsartaba yafice daga falon, sai mita yake, ga jaririya mezai hana yayi mata addu'ah
Ummi ma kawai bayansa tabi da kallo badan ta yarda da maganar tasaba
*** ***** ***
Washe gari kiran sallar farko acikin kunnanta akayi, tana juyi tareda addu'ar tashi daga bacci kawai saita ganta akan gado, tajuya gefenta taga Ummi tana bacci
Tambayar Data fara zuwa ranta itace waye yakawo ta?

Itade tasan cewa a kujera bacci yadauketa, bade wannan Baffan ne yadaukota ba?cikin sauri tafara dudduba jikinta, Allah yasa de bashi bane
Saukowa tayi tashige toilet tadauro alwala tafara gabatar da sallah, bayan ta idar tafara karatun qur'ani har aka shiga sallar asuba, saida ta idar sannan ta tashi Ummi itama tayi, harsaida gari yayi haske sannan ta gaida Ummi, fita zatayi waje, Ummi tace tadawo ta kwanta tahuta, komawa sukai suka kwanta, amma bakwai da rabi tafarka, ta tashi Ahankali tashige kitchen, tana zuwa taga wata yarinya tana aiki, tace mata "sannu da aiki, kema anan gidan kike?"
Kallanta tayi cikin ladabi tace"ina kwana?

"
Nawal tace" lafiya, Yaya sunanki?
Chapter 21 · 0% Book details