Sashe 22
Ni Da Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"
Ranki yadade sunana" Sabira, nice me aikin gidan nan, naje ganin gida ne kwana biyu, bana nan akai bikin yallabai "
Tace" Allah sarki, kawo nataimaka miki da wani aikin "
" A a ranki yadade kibarshi, yallabai bazaiji dadiba idan ya ganki kina aiki "
" kinga Karki damu, kawo muyi tare "
Badan tasoba tabata suka fara gabatar da break fast din tare, har falo suka kai komai, sannan ta koma daki taga Ummi bata nan da alama tana toilet, gadon tafara gyarawa sannan tafara gyara dakin, ta nemo wayarta acikin jaka ta kunnata, tareda ficewa daga dakin takoma falo
Layin umma tafara kira, bugu uku umma ta dauka, "Baby yagidan"
Muryarta ce tafara rawa Kamar zatai kuka tace "umma ina kwana"
"lafiya, menene kuma abin kukan?
Bakya rabo da sakarci"
"umma inasu Najma?"
"Najma gata can adaki a kwance, batajin dadi ba amma yau jikin nata da sauqi, bari nakai mata wayar"
Tashi tayi tashige daki tabawa Najma wayar tareda futowa, sai yanzu hankalin ta yadan kwanta dataji muryar 'yar tata
Najma tace "Baby yagari, ina angon namu?"
"lafiya kalau Najma, Umma tace bakida lafiya ya jikin naaki?"
"wallahi bana danjin dadi, zazzabi ne yarufeni, amma yau da sauqi"
"nima haka shekaran jiya nayi wannan zazzabin wallahi, amma yanzu da sauqi"
"to Allah yasawaqe, ina in law dinki me kirki?"
"Ummi wallahi taana daki tana shirya wa, ni ina falo"
"falo kuma?
Me kike nufi ne Baby?
Keda yakamata kicemin kina kirjin mijinki, amma wai wani falo"
Zaro ido tayi dukda Najma bata ganin ta, sannan tace "ke baya nan yafita"
Najma tace"owk yanzu naji batu, ai naso ace yana nan kibani shi nayi masa gargadi akanki, kada yabari ko quda yatabamin qanwata, amma yanzu tunda bayanan idan yadawo ki gaishe shi "
Murmushi tayi tace" Najma kenan, to zaiji, bawa ummah wayar takaiwa mama mugaisa "
Tashi Najma tayi takaiwa ummah wayar, suka gaisa da mama mariya dasu mus'ab, suna sallama da umma awayar a lokacin Ummi tafuto tace" Nawal dawa ake waya ne?"
Kallanta tayi tace" su ummah ne "
Hannu tabata tace" bani su nima mugaisa, kije kiyi wanka ki shirya muyi break "
Wayar tabata, tashige cikin daki
Sosai suka gaisa dasu ummah tana kuma qara bata tabbacin insha Allah zata kula da Nawal Kamar yanda zata kula da Baffah, daga nan sukai sallama
Tana kashe wayar aka nuno mata adadin kudin da akaja dakuma sauran blance dinta, katsewa tayi ta ajiye wayar agefe
Wajan goma da rabi yashigo falon, da takardu ahannun sa, ya rissina yace "Ummi barka da safiya"
"yawwa Baffah barka, yanaga idonka yayi ja,?
Ko bakai bacci bane daren jiya?"
Ahankali yace "nayi" share shi tayi, tasan cewa baiyi baccin ba, Yaya zata masa, yarinya ma tayi hakuri bare shi?
Tsintar maganar ta yayi tana cewa"Yakamata kaje kayiwa layin Nawal register basai tasa kati ba, su dinga cirewa a account dinka Kamar yanda kayiwa naka sim crd din, sannan kasaka mata Data saboda ganin labarai a yanar gizo"
Cikin rashin walwala ysce"yanzu Ummi wannan yarinyar wanne labarai zata gani?
Me labarai zasu qara mata?
"
" kacemin kawai baza'ayi ba"
Ahankali batare daya kalleta ba yace"za'ayi"
Cikin ransa kuwa tunanin barin qasar yake inba hakaba wannan yarinyar zata dinga hadashi da Ummi
Sake kallanshi tayi tace"ga wayar tata nan kaduba kadauki number, idan kafita yanzu sai kayi mata abinda yakamata, kaga saikaga number tata ma koda zaka dinga kiranta kaji lafiyarta,
itama sai kayi mata saving taka number, sannan ba number ka ta gama gari zaka saka mataba, number ka zaka saka mata wadda koda baka qasar idan ta nemeka zata sameka "
Wayar yadauka yasaka number sa aciki yayi kira, kiran yana shiga cikin wayarsa yakatse, sannan yayi mata saving number tasa da Muhammadu
Amma shi baiyi saving number taba, kai tsaye wajan massage yaje yaturawa wani abokin sa number, yasa yayi mata register tareda turo datar
Futowa tayi falon, tayi kyau cikin doguwar riga Mai fadi Kamar ta 'yan mali tareda mayafin rigar, mayafin sosai yabawa sumar kanta damar futowa, tana zuwa ta tsugunna har qasa tace masa "ina kwana?"
Kamar anmasa dole yace"lafiya" atakaice
Ahankali tatashi ta zauna daga gefen Ummi
Sabira ta gabatar musu da abinci, shikam kawai tea yasha, shima yadade yana juya tea spoon din sannan yagama
Saida yabari suka gama sannan yadubi Ummi "Ummi Zan fita, akwai aikin dazanyi"
Tace"to Baffah adawo lafiya "
Kallanta yasake yi, baiyi magana ba, tasan nufinsa sarai, jira yake taje tarakashi, Dan haka tasa hannu ta dauki takardun gefensa
Yana gani ta dauki takardun yamiqe, yayi zatan zata rakashi ne, kawai sai gani yayi tabawa Nawal takardun tareda cewa" tashi ki rakashi bakin gate"
Yana jin abinda tace yayi gaba, baima tsaya jiran taba, itama kuwa ta doru abayansa
Sai sauri yake fiya-fiya, har yazo harabar gidan, yajuyo yaga Nawal tana wata irin tafiya Kamar bataso, cikin bacin rai yadawo baya, yamiqa mata hannu batare dayayi magana ba
Tayi zuruu tana kallansa tarasa gane meyake nufi
Cikin tsawa yace "kibani takarduna nace"
Cikin sauri ta miqa masa, ya warce yayi gaba
*** ***** ***
"Nuhu abinda nakeso dakai shine kayi hakuri Nuhu, haka Allah yatsara, dama can Allah ya qaddara ba matar ka bace"
Hawaye ne suka zubo masa, yasa hannu ya share "hakane Abba, kukam kun soni, Babu abinda zance daku sai godia, Allah yabata zaman lafiya"
Mama mariya tazo wuce tadawo daga unguwa taga Nuhu a tsugunne gaban Abba yana share hawaye tace"a a Nuhu ashe kaine
Cikin sauri ya gaishe ta yace" yasu Najma?"
Tace" lafiya kalau Nuhu, ai Najma ma batanan tayi tafiya,
yaya qarin hakuri kuma na Baby?
"
Kansa aqasa yace" Hakuri da godia"
Tace"Allah sarki, sai hakuri Nuhu, Baby antafi Birnin tarayya, saide ka musu addu'ar samun zuri'ah tagari "
Abba ne yawatsa mata wani kallo, tasake cewa" to Nuhu kagaida mutanan gida "daga nan tashige cikin gidan, shikuma Abba yaci gaba da bawa Nuhu baki
*** ***** ***
Da yamma suna zaune itada Ummi, Ummi tace"kinga ameerah har yanzu bata zoba, Tun jiya naketa faman kiran wayarta bata shiga "
Cikin sanyin murya tace" Ummi baquwa zamuyi?
"
" A a Nawal ba baquwa bace, zuwatake kawai tanamin karatu, akwai littattafan datake qaramin "
Tace" To Ummi kawo nayi miki mana "
" kin iyane Nawal?
"eh Ummi na'iya"
Littafin tabata tace to gashi 'yata
Nan suka fara karatun tana koya mata littafin ishmawi babin dayake magana akan abubuwan dasuke warware alwala
Har wajan karfe biyar suna karatun su, wata mata tayi sallama tashigo, Ummi tace"a a Hajiya Karima mutanan cairo, ashe kindawo?
"
Qarasowa tayi cikin falon ta zauna akan kujera tareda cewa, Hajiya Halima wallahi nadawo jiya, kawai wai saiji nayi Muhammad yayi aure"
Ummi tace "wallahi Baffah yayi aure hajiya"
Nawal ce ta gaida matar tareda shigewa kitchen domin kawo mata ruwa
Matar ta dubi Ummi tace" Hajiya Halima ina kika samo 'yar kyakykyawar yarinya haka?
"
Murmushi Ummi tayi tace"laa matar Baffah ce"
Tace "kai amma yaron namu yayi sa'ar mace, gaskiya Baffah yasamu mace"
Cikin jin dadi Ummi tace "wallahi"
Nawal tadawo takawo wa matar ruwa da lemo, tace "gashi"tareda juyawa daki
Tace"to nagode amarya"
Bayan tasha Ruwan ta kalli Ummi tace "Ziyara tazo miki ne?"
"A a Hajiya, anan suke, tare nake zaune dasu saboda kinsan halin Dan naki, auren ba sonsa yakeba, shiyasa kawai nabarsu agidana"
"ai hajiya Halima inde kinsan basason junansu, toki tarkatasu sukoma gidansu, suje suyi fad'a awajan shara suyi fad'a awajan wanke wanke, ke sujiwa kansu ciwoma suyi 50 50 zasu so junansu, amma ahaka kam, hajiya bana tunanin zasu samu daidaito"
Ummi tayi jimm tace"kuma fa hakane hajiya, kinyi gaskiya, to kawai abinda yafi shine akwai wani gida anan kusa, kawai gobe Zan tarkatasu sukoma can, tunda nan din ina tareda sabira, yanzu fa ko magana ba sayi, tunda akai auren basu zauna sunyi magana ba, ina hankalce dasu "
Hajiya tace" yawwa kinga abinda nake fada miki ko, amma idan gidansu daya, dole wani abu zai tashi dazaisa suyiwa junansu magana, amma ahaka kam, akwai gyara "
Ummi tace" wannan gaskiya, ai kuwa gobe zasu tafi
Daga nan sukaci gaba da firarsu
*** ***** ***
Zuwa dare kam Nawal tasake da Ummi, dad'i da qari ma idan tatuna Baffah yafita saitaji wani sanyi, haka ta ware sunata fira sosai, har Ummi tana mamakinta
Sai wajan goma da rabi yashigo gida,bema lura da Nawal dake kusa da Ummi ba yafad'a cikin kujera cikin sigar shagwaba yace"Ummi wallahi nagaji dayawa yau "
Dadi Nawal taji,maganar tasa tana mata yanayi Data mk, cikin sauri tayi istighfari, domin tuno da cewa yanxu tanada aure
Ummi takalleshi" Baffah sarkin shagwaba, to ai yanzu bani zakayi wa ba, "ta nuna masa Nawal, kaga wadda zakacigaba dayiwa shagwaba"
Gaba daya yamanta da yarinyar, jin antuno masa da ita yasa nan da nan annurin fuskarsa ya dauke
Ummi tana gani, tasake tabbatar da maganar qawarta, bata sake yimasa magana ba, tadubi Nawal tace "tashi kikawowa mijinki abinci"
Cikin nutsuwa tatashi tayi hanyar kitchen,by mistek yad'ago idonsa, bai tsaya ko'inaba sai a tudun hips dinta, nan take yakawar dakai yasaki tsaki, wannan yarinyar har tasan tasaka irin abinda turawa suke sakawa na cikon hips
Ummi dataji yana tsaki tace"kode yunwar ce Baffah?
"
Batare daya kalletaba yace" A a "
Tasake cewa" Baffah Nawal fa tana zuwa makaranta, shine nace mezai hana itama kamaidata, tunda kaima wajan aiki kake zuwa, kaga ba dadi ta zauna ita kadai agida "
" Ummi ni yanzu banda time, amma zanyi magana sai akaita, a JSS nawa za'a sata?
"Baffah jss kuma?