Sashe 9
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kai na koma Daki Goggo ta bini da kallo kafin tace a fili"Ya Allah in da sauran zama Tsakanin yaranan Allah ya Daidaita su. in babu kuma Allah ya warware mana al'amuran" Taki fad'amin abunda zai kawo su Abba saboda jin nima bai Fadamin ba,Abunda bata sani ba ina komawa Daki na kasa Hakuri sai na Kira Yaya Ishaq har sau uku bai Dauka ba,Dare ne nasan yana gida sai na Kira Zainab tana Dauka ta fara fad'in"Maman Amir" Muryata a shake nace"Yana kusa..?basa wayar" Tasan wanda nake nufi tunda ai a gabanta nake kira yaki Dagawa so yake yayi amfani da yarana ya sake Cutar dani tana bashi ko mganarsa ban jira ba na fara fadi'n"Kada kace zaka yi amfani da yarana domin ka sake Kuntatama rayuwata Ishaq.." Kada mu yi haka dakai. Ka bar su, su zauna in da ya zame musu Dole. Naji Labarin kana shirin kwaso su ka kawomin su nasan manufarka wlh karka fara na riga nayi rantsuwan Wallahi Tallahi NAGAMA aure dakai. ya rage naka ka kyalesu ko kazo da su, ka kara Rikita su yadda kaima din zasu Gagareka" Ina gama fad'in haka na yanke kiran ina Huci duk da Abba bai Fito Fili ya fad'amin ba ammh na Fahimci zama Abba ya Shiryamana kamar yadda yaso yayi tun farko na tuna mganar mu da Nana Fatima jiya har ce min tayi in Abba yazo yana tambayata kada naji nauyin gayamasa komai Abba zai kwatar min yancina to sai yanzu na Fahimci mganar ta gefen gado na zauna gabana na Faduwa ni bazan taba iya mgana ba. sai in har Ishaq ya warware mafarin komai da bakinsa. Washegari ma yadda Goggo ta tashi da Shirye shirye na tabbatar da Zargina sannan da Safe mun yi mgana da Hafsah tace Har da Ammi da Yaya Abdul'Ahad a babbar Jeep din Abba zasu taho,Kuma naji Goggo na waya da Yaya mariya ita zatayi girkin bakin,Tunda Tafi kusa akan Anty Nasara ina Daki sai na Lafe wanka kawai nayi na koma na kwanta Ina Tunanin yadda komai zai gudana yau sai dai na samu mutuwar jiki da Faduwar gaba Ishaq da Mama suka Fara isowa tunda su tafiyar Jirgi ce,Ina Daki naji muryoyinsu suna gaisawa da su Goggo,naki Fitowa nima kuma ban ji an yi mganata ba Duk da Raunin jina nima na Koyi na kasa raunanun kunnuwana ina Jiyo mgana daga Falon Goggo. Su Abba sai wajen sha Biyu suka iso,zuwan su yasa na fito bazan ji zuwan Abba da su Inno naki Fitowa ba,sanda na fito su Abba na kofar gida sai su Inno na duka na gaishesu Inno tace"Yar nan haka kika sha jinya..?jiki sai kashi..? Baba Ati tace"Daman ai duk sauran sun fita kumari sannan ga rashin Lafiya kuma" Sai mamakin Ramata suke yi wajen Mama na isa tana Falo na gaisheta sai naga bata son kallona kanta na kasa ni dai ban bi ta kanta ba. araina nace yaji barazana kenan bai Daukomin yaran ba wajen Ammi naje muka gaisa ita kan sai da ta taba wuyana Tana Fadin"Na shige su ni Aziza..Fa"i kin ji kasusuwa..?bari Baban Nana yazo tafiya dake zan yi na cike miki wannan kasusuwa da ba su da kyan gani" Inno tace"ke ana shirin Daidaita komai tabi megidanta kina wata mgana" Sai Ammi tayi shuru batayi mgana ba,Abba basu shigo gidan ba sai bayan azahar yaje duba ginin gida sai da kuma suka Tsaya suka yi sallar azahar sannan suka shigo nan ma cikin gida su Ammi sun yi salla sun ci abinci Inno da Baba Ati da Goggo sun kule sai Tattaunawa suke ni ko muna tare da Ammi tana ta ja na da Hirarta na barkwanci,su dai sun ci abimci ammh Su Abba ko da suka shigo akace ga abinci yace sai an gama zaman muna Daki ni da Ammi ya kirata yace tazo dani. Ina jin haka sai na Rude ganin haka yasa Ammi ta mike ta Dafa kafad'ana tana Fadin"Kada kii damu Fa'i ba wanda zai miki Dole. sai dai kada ki yi shuru ki Cutar da kanki ki yi mgana domin nema miki yancinki aure Ibadan Allah ne ba Cutarwa ko bautan Mutum ba ne, kin ji ko? Sai na gyada mata Kai Lokaci d'aya ina maimaita sunan Allah a raina yadda zan samu natsuwa Hijabi na saka ta riko Hannuna har Falon Goggo kaina na kasa har gaban Abba. Ina zama na dago kaina karaf ana Yaya Ishaq ya rame yayi baki yana Sanye da shadda navy blue daga bangaran Hagun Abba ni kuma ina Bangaran Dama mun saka shi a Tsakiya, sai na dauke idona ina zagayen mutanen falon da kallo. Dukkamu muna saman Cafet ne Inno da Baba Ati ne suke kan kujera,Naga Mallam mijin goggo sai Ammi sai Mama sai ni sai Abba, sai Uban gayyar Ina jin Yaya Abdul'Ahad yana waje shi da su Yaya isa. Kaina na maida kasa ina kokarin Daidaita kaina. domin sai naji kamar bazan iya mgana a yanayin da na samu kaina a gaban Abba ba.