Sashe 67
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
na" Ai ko na basa dama kamar yadda ya bukata. sai ya koma bayan mun natsa fad'i yake yi"Kamar ma ban yi ba. Wlh komai ya sauya ya kara sugar" Kansa na dungure ina Fadin"Kuma sai akace komai kaji sai ka fad'a..? Bakinsa ya kama yana fadin"To in kama bakina kenan..? Harda wani ladabin Dole Mirmishi nayi kawai ban yi mgana shi kuma sai ya kamani ya Rumgumeni yana Fadin"Allah ya yi miki albarka. Allah yasa ki haifo kannen su Ahmad dozin Biyu haka" Mukamikinsa na Tokare ya yi gefe yana wash,Sosa wajen ya fara yana Fadin"Yaushe kika zama Muguwa Faa'izaa..? Ya ja sunan kamar wani abu,Hararansa nayi sai ya gane laifinsa da Sauri yace"To na rage Dozin Daya" Tiolet na shige na barsa ina ji yana Fadin"To naji rabin Dozin ga su Amir goma kenan ina laifi Father of 10" Sai dai na bige da mirmishi ina wanka Soyayya da kaunar Engr sun taru sun cikamin kirji sun hanani sukuni yadda yake kaunar ya'yana wlh ko Ishaq albarka shiyasa nake yi masa kara in muna mganar su sai dai nace ya'yan ka. Yaran nan suna da lambarsa barin ma Anum uwar karambani sai dai yace min sun kira shi da wayar Mama Amir ma suna mgana da shi,Zumunci dai ne kila bazai Dore ba tsakanin Engr Da Ishaq kowa na ganin zumunci da wani matsala ne shi Engr haka nan baya so ya shigo masa shima Ishaq din har gobe yana kaunar Fa'iza shiyasa baya son Doguwar mu'alama da wanda ya hanasa mallakar Fa'iza a karo na biyu. sai dai yaran bai isa ya raba su da mahaifiyasu ba yasan Fa'iza ta shanye abubuwa dadama Saboda yaran nan suna mata kauna ta sosai kuma shima Engr yasan yana kaunar su Darajan yana Son Fa'iza yana jin kishin yadda yaran ke kiran Engr Baba sai dai ba shi da yadda zai yi yasan ni ko ya fad'a ko kada ya fada Engr mutum ne nagartattacen kuma Kishinsa duk akan Fa'iza ta auri wanda ya fisa ne yana ganin ta cigaba fiye da in da ta dawo ma auransa. Da safe bayan mun gama karyawa Engr ya zauna da Badariya suka Tattauna ta fad'amai komai kuma ya gamsu a wajenta ya karbi lambar Yusuf ya kirasa suka gaisa ya fad'amasa sunansa Engr Abdulbasit Mijin Fa'iza yar'uwan Matarsa Badariya daman don ya shaida masa ne matarsa na wajen su da sauran bayanai yusuf ya rude Engr yace zai bashi address yazo nan Abuja yana son ganinsa. Abun mamaki da Sassafe sai ga shi jiyan ma bai samu jirgi ba ne da Shigar dare zai yi irin yadda Hankalinsa ya tashi yana son Badariya kuma bazai iya Rabuwa da ita ba. Engr bai bari yaga Badariya ba sai da suka tattauna na tsawon awa Biyu sannan ya kira wayata yace na Turo Badariya,mu dai tare muka bar su biyu su fahimci juna bayan Engr yace mata ta saki ranta in sha Allahu wannan matsalan angama da ita. Bai yi wani bayani ba sai chan ba jimawa Badariya tazo tace min yusuf yace tare zasu koma naji Dadi na yi ta mata Fatan alheri ina kara jadaddamata ta yi hakuri ta kuma kara Hakuri. Badariya tayi mirmishi kafin tace"Nagode Anty Fa'iza ke da Mijin ki kin yi min dukkan gatan da Dangina zasu yi min Allah ya saka da alheri. Yusuf yace an daidaita bayan tafiyata Yayansu ya shiga mganar Hajiyarsu ta amince ya sauyamin gida sannan an yi min iyaka da matarsa kuma ya fadamin megidan ki ya yi masa Fad'a sosai ya kara nuna masa tunda yana sona to yasan Darajata" Nasan halin Engr daman bazai yi wasa ba muka rumgume juna,muka fita tare har Falo Yusuf nata godiyan Hidima itama Badariya nayi Direban gidan su Papa ya kira shi yazo ya kaisu Filin jirgi Yusuf bakin nan kamar Gonar auduga tsakanin miji da mata sai Allah har ta fad'a masa tana da ciki. Nima ranar tukwaici na musamman na bama Engr saboda jin dadin yadda ya maida matsalan Badariya kamar tawa muna kwance kaina na saman kirjinsa bayan ya gama shagalinsa yace"Ki daina min godiya duk mai kaunarki nima ina kaunarsa kin fad'amin yadda Badariya ta kaunace ki saboda Allah nima sai naji ina Kaunarta Saboda wanda ta kaunace ki domin sa" Kuma fa ba wani labari na bashi ba nadai fad'amasa Badariya mai kaunatace shima yace tunda tana kaunarki nima ina kaunarta,Washegari gidan su Papa muka yini ni da shi muna ta Hidimanta ma Hajiya Kudurta da Burinta ya gama cika Tunda Oluwatosin ya yi aure kuma daga gani yana cikin kwanciyar Hankali ita da Maa suna ta godiyar Abinci har Papa sai da ya yi min mganar ina ta Dawaniya da su bana gajiya..? Kaina na kasa ina mirmishi nace ba wani Dawaniya aciki suna ta min godiya da zamu tafi Maa ta bani Mayafai da Turarukan wuta sai ban ce mata ina hadawa ba na bari sai naje kaduna na hado mai kyau da kanshi na kawo mata. Da muka dawo gida nayi ma Engr mganar turaruka sai yace na bari akwai tsarin da yake so ya yi min yadda Sana'ata zata tafi tare da zamani daman na fad'amasa ina so maje kaduna ko nayi sako,asiyo min kayan hadin na hada a gida saboda Maa,kuma tunda naji yace haka sai ban kara mgana ba, nasan tunda yace yana da Tsari to ina tabbatar ma kaina Tsarinsa a kaina mai kyau ne. Ban sani ba ko Badariya ta kira chan Lagos ta fad'ama su Mama komai,?ni dai sai kiranta nagani tana ta min godiya har Anty Binta ma ta Kirani sai gashi da bakinta take fad'amin Halin da Halisa ke ciki da mashayin mijinta kuma an yi an yi yaki sakinta. Tana kuka tana fad'amin ko zan fad'ama Engr in zai iya wani abu nace mata zan fada masa in sha Allahu. Ni kuma ganin taimako ne sai nake gayamasa,nima sai alokacin yake fadamin Yaya Ishaq ya kirasa yana ta Godiyan abunda muka yi ma Badariya kamar mun yi mata wani Hidima,mganar Halisa kuma yace sai ya shiga kano zai ga mijin Halisan da kansa ko jari ne bai da shi a bashi ammh sai in har zai daina shan kwaya da saida su. Nan take ma yace akwai abokinsa dake aiki da Kotun musulunci a kano Lauya ne zai sa ya gayyacesa ya yi masa nasiha da barazana ko za'a dace. Ta hannun Anty Binta aka samu lambar wayarsa aka turama Lauyan shi kuma yace in sha Allahu zasu zauna da shi. Kwana Biyu tsakanin Lokacin muna shirin tafiya Edo washegari tunda yace tare zamu koma ya Kira Engr ya fad'amasa ya nemesa sun zauna ya Fahimci rashin sana'a ne da kuma rashin gata yasa ya fad'a wannan harkan sai kuma Tarayya da abokan banza,ammh ya yi masa alkawarin in yau ya samu wanda zai tsaya masa zai bar wannan sana'ar daman sha ba kullim yake afata ba,zai koma makaranta sannan zai zama nagari Engr na jin haka yace tafiyarmu sai Jibi washegarin jirgi yabi zuwa kano sai Dare ya dawo yace min kamar ya yi ma mijin Halisa kuka ga namiji har namiji ammh zuciya ta mutu,yace ya bashi Miliyan daya zai fara kasuwanci sannan zai koma makaranta Tunda yana da Diploma kuma ya yi masa alkwarin zai zama nagari in dai zai Tsaya masa shi kuma yace zai Tsaya masa har abada, ya bashi lambarsa yace in yana bukatan wani abu,Har kuma gidan yaje yaga Halisa yana Fad'amin ko abinci basu da shi ga gidan Haya an yi yawa. sai ya ce masa ya samu wani gidan da zasu kama su kad'ai zai biya kudin to sun rabu akan sai an samu zai kirasa. Idanuwana suka ciko da hawaye Allah Sarki rayuwa na rumgumesa ina masa Godiya sai ya rikeni sosai yana Fadin"ko kashi ne indai dan'uwanki ne abun Darajawa na ne Faa'izaa" Ban ji wani bakinciki domin ya taimaki Halisa ba yar'uwata ce har Abada ban isa in raba wannan jinin ba,ballatana abuda ya faru a baya ya Dade da wucewa ni din ne kuma na rabu da Ishaq na auri wani wanda yasan Darajata da mutumci,ban taba rikonsa araina ba ina yin komai Saboda Zumunci ne. Sai ga Anty Binta na kuka tana min godiya ita da Mama tsakani na ko da Halisa kamar uwarta haka ta Dauke ni. kira akai akai Anty Fa'iza kaza Anty Fa'iza tun balle da suka samu gida karami Flat,Engr ya biya musu kudin haya na shekara Biyu,sun koma sannan Rayuwa ta fara zama daidai bata iya yin komai sai da shawarana.