Sashe 12
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mirmishin da ke saman Fuska sai dai a alokacin in za'a tona Zuciyata kamar zata fashe saboda bakinciki da kunci. Abba ya kasa mgana Saboda Takaici Goggo tace"Wannan mganar sharia"a ce ta ila'i dole muna bukatar malaman da zasu yi mana fashin baki kan wannan al'amarin" Da Sauri Mallam ya jefomasa tambaya da cewa"Har na tsawon wata nawa ka di'bar ma wannan jinginar? Ba zato kawai sukaji Muryata a Kausashe ina Fadin"Har na Tsawon Shekaru bakwai. Shekaru bakwai da Doriya Mallam" Gabad'aya sai suka had'a bakin wajen Fadin"Shekaru bakwai fa kika ce Fa'iza..? Ina kuka na jinjina kai kafin nace"Iya shekarun da nagaji ne na nemi mafita ammh Jinginarsa gareni ta har Abada Ne. Saboda baya kaunar kara Had'a zuru'a dani bana haifa masa ya'ya Daidai da Burinsa,tunda bazai iya sakina Saboda kalaman Baba akansa ba,sai ya Zabi ya jingine ni tunda zai auro wacce tayi daidai da Ra'ayin sa kuma wacce zata Haifa masa ya'ya farare kyawawa daidai da ra'ayin sa Shekaru sama da bakwai na kwashe Cikin kunci da bakinciki bayan wad'anda na kwashe a baya Abba ka gayamin nayi Laifi domin na nemi da ya Sauwakemin..?ba aikin da ya fara na nemi ya karishe ba..? Na fad'a ina kallon Abba Hawaye kamar ana tunkudo su haka suke zubomin Abba yaji jijiyoyin kansa na tashi,Saboda bacin rai ya kalli Ishaq yafi sau uku shi kuma kansa na kasa su Inno jikinsu duk yayi sanyi Ammi ko har tana tayani kuka. Abba ya kalleni ina kuka Tsausayina ya kamashi,ya rikoni gefen kafadarsa yana Lallashina jina acikin jikinsa yasa na barke da kukan da shekaru sama da goma ina neman Kafad'an da zan kwanta nayi wannan kukan ban samu ba sai yau sai kawai suka ji muryanta na saki kukana da Dukkan Karfin zuciyata sai Ran Abba ya kara baci ya Dago Cikin Fushi yana kallon Mama cikin Tsawa yace"Da Sanin ki D'anki ya jingine auran yata shine baki yi komai a kai ba..? Jikin Mama na rawa zatayi mgana da Sauri nayi Wuf na tashi daga kafad'an Abba cikin kuka nace"Bata sani ba Abba. Dagani sai shi ne muka sani.." Abba ya dakamin Tsawa nima kafin yace"Meyasa baki fad'ama kowa ba..? Tunda Lokacin bana nan meyasa baki zo kin Fad'ama Goggon ku ba..? Kuka na kara sawa ina Fadin"Ya zan yi Abba..?yace nayi masa adalci da ya shekara takwas yana min na aurena a yadda nake ya zauna dani. to nima ya Roki da nayi masa adalci na barsa yayi Rayuwarsa da amaryansa Abba ina son na zauna da ya'yana Wlh Sabo da su ne. Sannan alokacin bana so na Dorama kowa nauyina Abba Shiyasa ban taba Fad'ama kowa ba" Na karishe Fad'a ina kuka gaban Hijabina ya jike da kuka. Abba sai sakin Huci yake yi yana kallon Ishaq da ya gama Tsurewa Mallam ya yi gyaram murya kafin yayi mgana Goggo ta rigasa da Fadin"Tabbas nasan Fa'iza bata ji dadin zama da Ishaq ba .bata da mutumci a idon sa da shi da Mahaifiyarsa da yayarsa, ni shaida ce ba irin cin kashin da basa mata Har ni kaina da ya'yana bamu Tsira ba Saboda ina kaunar Fa'iza" Abba kamar zai dagi Goggo yace"Kuma kuka kasa Raba auran dake cike da Zalunci Goggon su.? Sai Goggo ta saka kuka tana Fadin"Ya zamu yi Alhaji..?ina tausaya ma Fa'iza ina Tausaya yaran nan nata Sannan ita bata mgana ko yan'uwanta su yi tambayan duniyan nan bata Fad'a musu komai, sai dai tayi shuru bakincikin na cinta,sai dai muga tana ta rama da kamjamewa" Ta karishe fad'a cikin kuka,Abba ransa ya kara baci ya mike a fusace cikin Fusata yace"To ana aure Dole ne..?meyasa aka bashi auranta tunda baya sonta..? Mallam ne yayi mgana cikin lallashi yana fadin"Alhaji koma ka zauna ayi mganar nan a tsanake" Sai da inno ta kara mgana sannan ya zauna yana Huci,Kukan Fa'iza na soya masa rai Mama ma kukan datake yi ya sa kowa ya maida Hankalin kanta. Cikin kuka tace"Alhaji ku yi hakuri wlh ban san da wannan mganar ba,Ishaq bai gayamin ba sannan ita kanta Fa'iza bata gayamin ba. abu daya na sani a baya na musguna ma Fa'iza ina kuma neman afuwarta data yafemin" Ta fad'a tana share kwallah da Haban zaninta Abba kyafci yayi kawai ransa na Cigaba da kuna sai kiran wayarsa ake yi yana Kashewa baya son mgana ma alokacin Saboda yadda ransa ke kuna Ishaq ko motsi ya kasa Saboda Fargaba da yadda yaji muryan Abba cikin zafi da kaushi. Mallam ya gyara zama yana Fadin"Duk ba wannan ba ne Alhaji. A kokacrin Alhaji kabiru shine namiji babba ga su Fatima da Aisha shi kuma ya rike Fa'iza a hannunsa har ga Allah bai had'a auran nan da wata manufa ba. ya hada shi ne Saboda yana Tunanin Ishaq zai iya Rike Fa'iza da maraicinta har bayan Ransa bai taba sanin zai yi haka ba,In da ya sani Alhaji kabiru yana kabarinsa Allah yaji kansa bazai aura mata shi ba sannan inda yana Raye wlh shi da kansa zai raba auran nan indai ya ga Fa'iza na cutuwa" Falon sai ya yi shuru kowa na Sauke Numfashi Inno ta gyara zama tace"Duk mun ji,Daman yaran yanzu ai ka haife su ne,baka Haifi Halin su ba mu yanzu matsayin wannan auran zamu fara nema domin a shari'a ina jin Tuni auran nan ba shi" Baba Ati tace"Gaskiya shekaru bakwai ba kwana bakwai ba ne. Inno wannan Cutarwan ya yi yawa gaskiya" Abba ya yi saurin taransu da Fadin"Ban damu da wannan ba ko da aure ko ba aure sai ya sakar min y'ata tunda ba'a aure dole" Ya fad'a a kausashe Ishaq ya Dago Fuskarsa ta jike da zufa saboda Fargaba,cikin rawam murya yace"Don Allah Abba..! Hannu ya daga masa kafin yace"Ai baka sonta ko.?to ka saketa bazan yi maka Dole ka zauna da wacce baka so" Yafad'a cikin bacin rai sai kuma kowa ya kasa mgana Ammi nata jin Dadi a ranta ni Abba ya kallah ina sharan kwallah Cikin Fada yace"Ni ba sakarai ba ne ban kuma Haifi sakaran d'iya ba.Meyasa,kika zauna Tsawon wannan Lokacin da wanda baya sonki..?wanda ya zabi wata matar sama dake..? Yafad'a yana kallona Zuciyarsa har Dagawa take yi ran yan maza ya baci Tsawa ya dakamin yana Fadin"Tunda kinsan baya son ki meyasa kika yi masa afarman zama dashi..? Ina kuka jikina na rawa nace"Abba ya'yana.." Abba kamar zai Dageni ya tasomin yana Fadin"Ya'yan banza..Nace ya'yan banza kan ya'ya ne zaki zauna ya na wulakantaki Shi da yan"uwansa..?ki bar ya'yaan su mutu mana ai ba ke kika Haifesu ke kad'ai ba shima Uban su ne. Kada ki kara zama Saboda wasu ya'ya ana wulakantaki Jariri ma yazo duniya bai ga uwarsa ba. kuma ya Rayu ballatana yaran da suka girma" Yadda yake mgana yasa Inno saurin cewa"Usmanu kayi mata a Hankali" Sai a lokacin ya Saussauta mganarsa yana Fadin"Ki bude baki ki Fad'amin Tundaga farko har karshe in kika boyemin wani abu sai naci Mutumcin ki Fa'iza" Kaina naji ya sara na kasa mgana Tsawa ya sake dakamin Cikin Hargagi yace"Ki fad'amin Hujja nake nema yadda zan ci uban duk wanda ya ci zarafin y'ata wlh" Jin haka yasa da Sauri nace"Abba ba niyyata in tona masa asiri ba don Allah ka bar mganar nan" Marina ne kad'ai Abba bai yi ba,Ammh sai da na samu Tsaraban kallo kafin yace"Shi ai bai Rufa miki naki asirin ba shine ke kike neman ki Rufa masa.?Tona masa kowa yasan Abunda ke Boye" Kuka na kara Fashewa da shi har ga Allah na riga na yafe masa bana son Dawo da abun da ya wuce shima kallona yake yi alamun roko cikin lokaci daya duk ya zabge sai Zufa yake yi har Shadda jikinsa sai da ta jike da Zufa. Mama ce tayi mgana cikin Dashewar murya tana Fadin"Gwara ki Fad'a Fa'iza ki fad'a musu komai duk da nima nasan da Laifina tunda ina gani yana wasu abubuwan ban taba Hanasa ba,sai ma kokarin Dora shi kan Hanyar banza da laifina nima" Kukan da take yi baisa kowa yaji Tausayinta ba. Kamar daga sama sukaji ance"Ai bazata taba mgana ba Abba. Da zata yi mgana da ta fad'a muku ishaq ya yi ikirarin zai Daukomin yan Sanda in ya kara ganina a gidansa" Gabad'aya muka jiya bakin kofa in da muke jin mganar Yaya mariya ne ke Tsaye tana Hawaye Gabana ya fad'i shikenan Yaya mariya zata fad'i wannan sirrin da na zata ta manta da shi. Da sauri Abba yace"Taho nan Mariya ki fad'amin abunda kika sani kan zaman Fa'iza da yaron nan" Da Dauri ta kariso ta zauna agabansa kafin tace"Abba ban taba fadin ma kowa abunda ya faru ba sai yau. Saboda Fa'iza Saboda ita ammh yau bazan iya shuru ba! Ta kalleni kafin tace"Kiyi hakuri Fa'iza..'" Kafin tamaida kanta wajen Abba bayan ta gama kare ma mutanen Falon kallo ta wani sakarma Ishaq wani kallo kafin tace"Abba ban san mganar da kuke yi ba na shigo na dade Tsaye ina jin wasu mganganu. Wlh Abba Fa'iza ta sha wahalan rayuwar kaskanci da wulakanci a gidan wannan mutumin,Fa'iza bata da daraja ko Kima a wajensa da wajen uwarsa gata nan da Yayarsa Abba ni fa uwa d'aya uba Daya muke da Fa'iza ishaq ya bata Sakon ta gayamin kada na kara zuwa Gidansa da bata gayamin ba ranar da ya iskeni Abba koran kare ya yi min Fa'iza na kuka tana rokonsa ammh ya rantse in ban fita ba sai ya Had'ani da yan Sanda Abba" Gabadaya suka saka Salati Abba yace"Good..' Yaya mariya na Hawaye ta kalli Goggo tana Fadin"ai kin tuna Lokacin goggo. Lokacin da kuka barni wajen Fa'iza sanda tayi ciwon nan kikace nayi mata kwana Biyu to kwana D'aya nayi yayi min tozarcin da har na Mutu bazan manta ba dalilin da yasa har yau ban kara taka inda Fa'iza take ba. sannan ban kuma taba gayama kowa ba,sai yau shima din naga in nayi shuru Fa'iza zata iya koma ma Wannan rayuwar data bari" Da Sauri Abba yace"Bazata koma ba. Bazata taba komawa ba indai ina Raye mari" Yafad'a idanuwansa jajir Goggo na Sharan kwallah tace"Nasan dai daga Lokacin indai zamu gidan Fa'iza sai ki zille na Dauki Saunan wani abu sai dai yadda baki ce