← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 71

Sashe 45

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsakanin Mama ko Anty Binta an rasa mai iya mgana ballatana su fahimci yadda aka samu wannan Sauyin haka bangaran su Goggo ma suna ta jimamin garin yaya aka samu Sauyi ba tare da kowa ya sani ba..?Sai dai ba amsa tunda mazan duk ba su dawo ba,ni kuma ina gidan su Yaya isa Nana Fatima ta kira Ammi tana fad'a mata Halin da ake ciki da sauyin da aka samu. Ammi ta rangada guda ta yi rawa tayi juyi ina zaune ina kallonta Sai da ta katse wayar Fatima sannan ta kalleni tana fadin"Aure ya Dauru murna muke ta yi. Kin Zama Amaryan Engr igiya uku har Abada" Kamar an zaremin wani mutuwar jiki haka naji,sannan na ji gabbaina da suka yi sanyi sun tashi daga suman da suka yi,Naji dai yanayina ya sauya kadan ammh kuma bana bakincikin sai ma wani boyayen ajiyan zuciya da na saki batare da na sani ba,Ina da yakinin zan samu farinciki ko ba duka ba ammh zan samu ko da kad'an Daga cikin farincikin da Sauran mata suke samu a gidan auran su. Sai da mukayi sallar Azahar Ammi ta sani gaba muka koma gidan Goggo ba wasu jama'a sosai sai na gida,Muna shigowa Yaya Mariya ta saka gud'a tana fadin"Shi daman alkawarin Allah baya tashi" Daman ita bata wani so Yaya ishaq ba,tun da farko da bata yi da shi yasa har yanzu sama sama sama ne,ni dai daki na wuce,Su Mama na falo duk jiki ba Dadi,Badariya ce kadai ta biyo su Nana Fatima zuwa dakin wajena ita kuma Ammi ta tafi wajen Goggo Abba ya kirata suna bukatar abinci da abun sha. Duk da Jikin Badariya ya yi sanyi bayan Nana Fatima ta rumgumo ni tana fadin"Ina tayaki murna yar'uwata. Allah ya sanya alheri" Na amsa mata da Ameen kasa kasa Sai Badariya itama ta kariso tana Fadin"Ina murna Anty Fa'iza Allah yasa gwara da akayi" Na amsa mata ina kallonta tana so mu yi mgana ammh sai taga idanuwan mutane shiyasa ta juya ta fice Su Raliya ne da su Yaya Asiya tare dani suna ta tattauna yadda lamarin ya sauya ni dai ina jin su ban ce komai ba zan yi mgana ammh ba yanzu ba. Abinci su Abba Nana khadija da Hafsatu suka kai musu,Sai wajen uku na rana muka samu kebewa da Badariya shima din tazo fad'amin su Mama na shirin zasu koma katsina ne.. Cikin mamaki nace"Yau kuma..?Na sha sai gobe..? Cikin damuwa tace"Mama tace kunyarku take ji bazata iya zama ba. taji abunda yaya ishaq ya aikata Jamal ya kirani a waya duk ya fad'amin yace Yaya ishaq nata kuka yana bama Abba hakuri, shi kuma yace bakomai tunda dai kin auri wani shi ba da shi za ayi masa rufa rufa akai masa Datti ba.." Kai na sadda kasa ban yi mgana ba sai ta Dafani tana fadin"Don Allah ki yi hakuri Anty Fa'iza" Ina kokarin maida hawayen da suka kawomin nace"Bakomai rayuwa ce Badariya" Nama kasa mgana sai kawai na saka kuka,sai ta rumgumeni tana Lallashina itama tana cikin damuwa ammh kuma bazata iya gayamin ba ganin yanayin da nake ciki. Tare da ita mukaje wajen su Mama,Anty Binta dai ta kasa mgana Mama ce ke ta bani Hakuri nace bakomai Anty mahma tace"Shi ma dai Ishaq kamar wani yaro..? Ai ba haka ake nuna kishi ba" Yake kawai nayi ban yi mgana ba Halisa nake kallo duk ta rame ta lalace kamar ba Halisa ba Daga gani dai tana ji ajikinta a raina nace Allah ya kyauta. Anty Binta ke tambayan ina shi Ishaq din.?Badariya tace"Jamal yace ya wuce kano ta chan zai siyi ticket na komawa Lagos. tunda yasan tsiyar da yayi" Mama tace"To ina shi Amir.? Sai da akayi mgana na Tuna da Amir cikin Damuwa nace"Ko dashi ya tafi ne..? Badariya na shirin mgana sai ga Jamal da Amir sun shigo tare,yana ganina ya Rugo ya rumgumeni yana kiran"Umma." Mu kadai ne afalon su Goggo suna ciki,Ammi ta gama warware musu komai kowa yaji sai yace gwara da ya rasa Fa'iza bai chanchanta ba. Mama har ciki ta shiga tana basu hakuri tana sharan kwallah Goggo tace bakomai kansa yayi mawa ga shi ya rasa Fa'iza ita kuma Allah yasa gidan arzikinta ne. Ganin yanayin sa yasa nasan Amir na cikin damuwa sai najashi Daki bayan mun gaisa da Jamal shima hakurin yake bani nayi yake,nace bakomai a raina ko nace shi ke da Hakuri kuma yanzu ammh har abada bazan taba yafe masa da kazafin da ya kullamin ba sai mun yi Hisabi a gaban Ubangiji ranar gobe kiyama. Tambayan Amir na yi da yaci abinci sai ya dagamin kai kafin yace"Naci ai ina tare da su Abba ne a sabon gida" Sai nayi shuru na kasa mgana saboda nasan yaji mganganuna da na Babansa kuma wasu kalmomin masu nauyi ne a Tunanin yaro karami kamar Amir. Ba zato kawai naji ya riko hannuna kafin yace"Umma ki yi hakuri" Sai hawaye sharr da sauri na rikosa ina fadin"Kai Amir menene yasa kake kuka..? Sai na rumgumesa ina Lallashinsa cikin shesshekan kuka yace"Umma ki yi hakuri kin ji ko.? Sai naji kaunar d'ana ta kara ratsani na Dago fuskarsa ina share masa hawaye,ina fadin"To shikenan na hakura kai ma ka daina kuka" Mirmishi nayi masa shims ya maidamin kafin yace"Umma gwara da kika auri Baba baki auri Daada ba. Tunda yace miki ke datti ce" Cike da mamaki nake kallonsa kafin na samu bakin mgana yace"Baba yace yana son ki Umma. Muna yace yana son mu" Sai ga hawaye sharr sun zubomin rike hannayensa nayi ina fadin"Nima ina son ku ya'yana ka kula da kannen ka Amir kuma kada ka kuskura ka fada musu abunda ya faru kaji ko..? Sai ya gyad'amin kai alamun bazai fada ba,kansa na dafa ina fadin"Yauwa Sannan ka lallashesu in zasu yi kuka saboda ban dawo ba kaji ko..? Nan ma kai ya gyadamin nima sai na jinjina kaina kafin nace"Allah ya yi muku albarka gabadaya" Ya amsa da Ameen,mun dade muna Hira da shi yawancin labarin rayuwar su a lagos ne ina jin sa ina mirmishi gefe daya ina sharan kwallah Haka Allah ya kaddara bazan zauna da ya'yana har abada ba. domin nasan Ishaq bazai bani ko daya Daga ciki ba. Sai bayan La'asar su Mama suka wuce katsina an rabu zukata ba Dadi,kamar kada mu rabu da Amir da yaga ma Ina Damuwa sai yace"Umma ki daina damuwa fa zan lallashi su Anum kuma ma ai Baba yace zai rika kawo ki,kina ganin mu muma yace zamu rika zuwa muna ganin ki" Sai na rumgumesa ina kuka Kaunar Engr da ta boye acikin raina ta sake Fitowa a cikin zuciyata,ance mai d'a wawa daman ya Fad'amin shi baya son ya'yansa su kirasa wani Daddy yafi son Baba na gargajiya. Nasan Engr na da kirki ammh sai da Amir ya kalleni yace"Umma ki daina Damuwa shi Baba na da kirki bazai rika sakaki kuka kamar Daada ba" Har suka tafi da na tuna da mganarsa sai naji hawaye sun kawo min Allah Sarki ya'ya Rahma ne Allah ya bama wadanda ba su da ya'ya masu albarka mu kuma da muke da su Allah ya tsare mana su sannan ya kara shiryawa,katsina zasu kwana Gobe su tafi kano Jamal Dole zai siya musu Tiket zuwa lagos tunda Uban gayyar ya watsar da su ya yi gaba. Tunda dai na tabbatar da cewa Engr na aura sai duk wani Fargaba na ya kare na saki jikina da yammah Nana Fatima na cewa na sake wanka ba Gaddama na Sake yin wanka na sauya kaya zuwa atamfa Doguwar riga. Da naga bata ce zatamin kwalliya ba kai Tsaye nace"Fatin mu kwalliyar fa..? Cikin shagwaba na fada ai sai ta rike baki tana fadin"Eyee lalle na yarda ana son Engr ammh ai dazu har kina mana Boren baki so" Ina Dariya nace"Dazu kika ce. yanzu ai komai ya sauya". Duka ta D'akamin tana fadin"Zaki sani ne bazan yi kwalliyar ba". Dariya na fara ina bata Hakuri sai ta rumgumeni tana fadin"Naji dadin ganin ki cikin farinciki Fa'in mu Allah ya saka ki yi farinciki fiye da yadda kike Tsammani, Allah yasa Engr ya juyar dake Dadin da sai kin manta sunan ki" Tsungulinta nayi ina fadin"Ba'a gasa bakin nan naki ba" Na fad'a ina dariya ni da ita ina tuna Dazu da Yaya Mariya tace gwara da Ishaq ya furta haka akansa wasu hallayansa tasa Inno ta mata dakuwa tana fadin bakin ki kamar bai ji gashi ba Mariya, muna ta dariya shine na tuna na fad'ama Nana Fatima" Sai da mukayi sallar mangariba sannan Nana Fatima ta min kwalliya mai sauki sai tunani nake yi ko Engr yayi Fushi ne bai nemeni ba. Abunda ban sani ba suna tare da su Abba har Dr.Lawal sai washegari zai koma Abuja,bazai iya barin su ba,kuma wayata ban kunna ba amnh yafi kowa son ganina da jin muryata. Abincin har sai da aka bama almajirai tunda ba wasu jama'a ni ko su Sa'adatu hana su dawowa yau nayi alokacin bansan lamarin zai sauya ba Ammi ko bakinta har kunne ammh da Safe ko Fara'a batayi. Taruwa suka yi Nana Fatima da Raliya suna min tsiya Badariya na taremin daman tana nan bata koma ba,Yusuf din zai turo Direba yazo ya Dauketa jibi. Muna cikin hakane Abba ya kira wayar Nana Fatima akace a bani ina karba yace"Fa'i ki kunna wayarki Engr na son mgana da ke" Cikin sanyin jiki na amsa mai da toh wayar na cikin karamar jakata ta hannu na fiddota na kunna,naga tarin sakonnin Engr ban bude ba sai na goge su nasan ma magiyane tun a baya yanzu kuma mun taka wani mataki basai mun koma baya ba. Ina kunna wayar kamar yana jira sai ga kiransa gabana ya fadi ga su Badariya sai na lallaba na fice ashe suna Lura dani sai suka kwashi shewa na fice ina girgiza kai kawai. Tsakar gida na fita sai naji akwai sanyi sai na shige dakin Karikitan goggo da nawa ni kaina,na samu saman Freezer na haye har kiran ya katse sai ya kara kira ina Dagawa bai jira nayi mgana ba yace"Alhamdulillah Faa'iza ta zama ta Tosin har Abada" Mirmishi nayi ban yi
Chapter 45 · 0% Book details