← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 71

Sashe 68

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Sai da muka koma Edo sannan na Tura mata 50k nace itama ta fara sana'an cikin gida sai ta nuna min tunda ta iya su Cake,donut bari ta gwada sai nace hakan yayi ta kuma tallata cewa tana aikin su Sai a biyata,bansan irin addu'an da muka sha Daga ita har mijin nata ba,
Ni da Engr ne madubin su yanzu a baya Hajiya Dala suke ganin zata iya musu komai sai ga shi yanzu an ce tsakanin su ba Mutumci Hajiyar Dala da kanta ta Kirani Duniya mai ya yi tunda yanzu ina auren mai kudi nima kuma ina da abun hannuna na wuce reni.
Da bakinta take fad'amin fadan su da Anty Binta daga karshe tace"Chan sanda Halisar ta hadu da shi nama sani ya yi musu barin kudi lokacin ana samun dillar kwayoyi na kai masa,kuma koda suke ganin dan'uwan megida na ne. yace fa Zaman makota ne na iyayensa da kakkanin yaro ammh basu hada komai da shi ba. ammh daga karshe Binta da Saudatu na ganin laifina ai ni kiri kiri na fad'a musu cewa hakkin ki ne ke bibiyan su suke ta ganin haka daga Halisan har Badariyan'"
Mamaki bai barni nayi mgana ba ina Tunanin ita duniya daman haka ta gada tunda har yau Hajiyar Dala ke kirana tana sukan Mama da ya'yanta komai daman ka gina shi da amana,ba ma ita ba kaf ya'yanta suna kirana da masu auren da yanmatan alhalin a baya ba wanda ma yasan da zamana ba..

Autan ta ma Futuha,ta kirani tazo Abuja bikin kawarta ko ina nan nace mata ina Edo ammh sai na had'a ta da su Kafaya ta kwana Biyu a gidan su Paapa kuma suka karammata da zata koma Ta jirgi paapa ya siya mata Tiket bayan abun arzikin data koma da shi sai ga shi ta koma tana labarin iyayen mijin Anty fa'iza suna da kirki kadan kadan sai na zama abun so a family kowa yana nema na, har da wanda ban taba zato ba in na zauna ina Tuna matakin Rayuwata tun daga farko har zuwa yanzu hannuwana kadai nake Dagawa sama na godema Allah Tunda Duka Ni'imarsa da ta mamaye rayuwata sanadinsa ne yau ga shi Fa'izar da ake gudunta sai ga shi na zama abun son kowa da kowa Allah kenan.
Muna Edo kafin mu koma Abuja,Zainab ta kirani tace yara sun samu Hutu ammh bata ji Yaya Ishaq na mganar zuwan su wajena ba,ina jin haka sai naji na kosa suzo sai na gayama Engr shi kuma ya Kira Ishaq ya kara rokonsa sai ya cika masa ido yace zasu zo yana jiran jamal ne tunda bazai sako su su kadai ba.
Jin haka yasa Engr ya karbi Lambar Jamal din suka yi mgana shi kuma ya Siyama duka yaran ticket yace su biyo Jirgi in zasu taho mu hadu a Abuja.
Duk yadda naso na boye murnata na kasa sai da na bayyana Engr nata min Tsiyan nace na bar masa ashe zence ne namu na mata kunya naji ganin har Zalamata ta fito Sarari.
In da ta ni za'a bi har Islam azo min da ita Zainab tace bata yayeta ba in bari sai in ta isa yaye zata kawomin na yayeta da kaina,ammh duka yaran su Shidda zasu mana Hutu suma Zainab tace suna ta murna zasu wajen Umma.
A satin muka dawo Abuja mukaje muka yi shooping saboda Engr yace bayaso su nemi wani abu su rasa,kamar Yadda Babansu yace Jamal ya taho da su ni da Engr mukaje Filin jirgi muka Daukosu haka yara nan suka kamkameni suna Ihun kiran sunana Umma Umma har da Anum babban banza Amir dai yana gefe shi Babba bai cika harkan yara ba.
Sai ga Jamal a gidana bai kuma san haka saukin kan Engr yake ba, sai da suka zauna suna ta hira ni kuma ni da yaran muna cikin gida,Amir daki guda na sauke shida Musty ,Dayan dakin kuma su Ahmad,Anum kuma nace ta zauna adakina.
Duk inda na saka kafa nan suke sakawa komai suka gani sai sun yi mgana Labarai ko haka nake shan su gidan sai ya karade da hayaniyar yara daman nayi abinci kafin su iso ai sai kowa yace ga abunda zai ci wannan yace Shayi wannan indomie ammh ban damu ba haka na shiga kitchen ina yi musu ra'ayinsu zuciyata Fes kamar an yi min albishir da gidan Aljannah.
Chapter 68 · 0% Book details