Sashe 33
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni ko ban san wainar da ake toyawa ba,Tsakani har ga Allah nima cikin wani yanayi na kwana abun mamaki da Haushi mafarki na yi ta yi masu cike da Engr a cikin su,sannan ko yaya na yi zurfi a tunani sai na hango kamilalliyar Fuskarsa na min mirmishi gabad'aya sai na tashi a jagule na rasa gane kaina Na tambayi kaina Fa'iza daga ganin mutum baki san komai a kansa ba sai Tunanin sa..? Abunda ban taba yi ba ko zamanin Ishaq wlh tallahi bana zama nayi Tunanin sa to basai da kwanciyar Hankali da so da kauna kake tuna mutum ba..?ba auran soyayyah nayi ba shiyasa ban san kallon so ko mirmishin soyayyah ba,ni bani da sani ta wannan bangaran a bangaran auran ma akwai ta bangaran da ni Fa'zan ban san komai ba. Na idar da sallar asuba ban d'aga daga kan Darduman ba ina ta azkar dina daman kuma jiya da daddare sai uku na kwanta nayi istikara,sai kuma na ga akasin haka maimakon naji na samu natsuwar Komawa gidan Ishaq a'a sai mafarkan Engr nake yi acikin barcina. Kuma in bude baki in fad'ama wani wannan iftila'in daya sameni abun kunya ne to abun kunya mana Daga ganin Sarkin fawa ni Fa'iza sai miya taki zaki...? Da hannu bibbiyu nayi Taguni ga Uban Hijabi ga carbi ina ja har bata lissafi nake yi saboda Tsabar Tunani ana ta ma kiran wayata ban ji ba sai daga baya ina Dauka Zainab ce sai dai ba muryanta ba ne na Anum ne na Tsorata ganin bakwai saura. Cikin tashin hankalin daya bayyana har amuryata nace"Ke Anum lafiya kuwa..?ina Antyn naku..? Sai naji ta saka Tsalle da Ihu tana Fadi"Eyee Umma wai da gaske zaki Dawo gidan Daada gabadaya ki zauna tare damu da Daada da Anty..? Sai da gabana ya fadi Zainab ta gama dani daga ce mata zan yi Tunani har ta Yadani na kuma san gabadaya yaran ta fad'a musu har da uban gayyan. Kafin na bata amsa naji hayaniyan sauran yaran suna ihu suna kiran sunana dakyar na iya tambayanta su Ahmad ne tace min"Eh Umma kowa nata Murna zaki dawo har da Yaya Amir baki ga Daada ba,yace yau zamu fita shopping gabadayan mu zamu gyara miki daki Umma don Allah ki Dawo.." Miyau na naji ya kafe nama kasa hadiyewa,saboda rudani ni yaushe nace zan dawo..? Ina jin hayaniyar yara kamar zan kashe wayata ammh Anun taki bari fadi take"Umma don Allah ki dawo kawayen mu fa kowa gidan su Umman su daadan su na waje d'aya sai mu ne Umman mu bata nan,Sannan Umma Daada yace shi ya yi miki laifi mu tayasa bashi hakuri don Allah ki yafe masa.." Tafada cikin wani yanayin da yasa sai da Hawaye suka kawo cikin Idanuwana,Anum da iya zencen Amir ne daman mara Hayaniya. Damuna tayi da fadin"Kin ji Umma ki yafe ma Daada don Allah ki dawo" Sai na samu kaina da fadin"Na yafe masa tuntuni Anum" Sai ta saka Ihun murna tana fadin"To Umma zaki dawo din.? Da gaske ne..? Kasa ba ta amsa nayi ina fadin"Yau ba makaranta ne..? Da sauri tace"Umma muna shiri ne..Ni ki fad'amin zaki dawo..? Da kai na daga mata kamar wacce aka zare ma lakka naji jikina ya yi min nauyi kafin nace"Ehh.." Kamar ashe a amsa kuwwa a ka sakani ina jin ihun yaran gabadaya Da mganar Anum tana fadin"Umma Umma yaushe..?gobe..? Don Allah ki dawo gobe.? Kaina na Dafe da naji yana Saramin kafin na samu damar mgana naji sallamar Ammi da shigowarta yadda naga tana hanzari ne yasa na katse wayar na mike da sauri kafin ma nayi mgana tajani gefen gado muka zauna tana Fadin"Fa'i albishirin ki..? Cikin kallonta nace"Goro Fari kal Ammi" Tana Dariya tace"Sauya Hijabi kije falon Baban ku ki dawo sai na baki albishir din" Cikin mamaki na kalleta zan yi mgana ta dora yatsa a bakina tana fadin"Ba yanzu ba sai kin dawo" Da kanta ta mike ta zabo min wani hijabi sea green cikin kayana Sabo ne ban ko taba sakashi ba. Ta bani na cire na jikina na saka bayan ta sakani na sauya kayan barcin jikina na saka wata bakar Abaya,ta kuma saka na goga Turaren Humra cikin mamaki nace"Ammi bana son kamshin turare,kuma fita zan yi fa" Ammi tamin dakuwa tana Fadin"Kuma kike had'awa kina Saida mana amnh ke kice baki so..?ai ko baki isa ba yarinya ba turare yanzu kika fara son shi da saka shi" Dariya nayi ban yi mgana ba,haka ta sakani gaba muka fita ina tafiya ta shiga gabana tana nuna min wai irin Salon Tafiyar da zan yi in na Shiga Falon Abba baki na bude kafin nace"Ammi waye ya zo wajena..? Ko baki Abba ya yi.? Fadin haka yasa sai da gabana ya amsa ko dai ko dai Engr ne..? Na juya nayi ma Ammi mgana naga Tuni ma ashe ta koma Shashenta ta barni nan tsaye sai na fara waige ina jin wani yam acikin jikina. Kamar najuya zuwa shahshen Inno daman ban shiga mun gaisa ba da Safe,Sai kuma na kasa bazan iya komawa ba tunda Ammi ce da kanta ammah jikina ya bani wani abu. To ko dai ishaq ne..?in shi ne kuma da Anun ta fad'amin.." Ni dai kafafuwana suke ja na zuwa Falon Abba ga yanayin mganata ga Sanyin murya shiyasa da nayi sallama ban sani ba ko yaji,ni kuma sai naji kamar gyaran murya shiyasa na shiga falon kaina na kasa. Kafafunsa na fara gani zuwa kansa yana tsaye ya juyamin baya yana waya ammh kuma abun mamaki wani yare yake yi kamar yarbanci yarbanci na kasa dai ganewa saboda ina Rude ne. Dagowa nayi in kallesa dakyau karaf ko kamar juyin waina naga ya juyo muka hada ido hud'u da shi jiri ne yaso ya kwasheni na kame kaina da jikina ammh a wannan karon ma jikina da gabana sai da suka amsa wannan kamilaliyar Fuskar da wannan mirmishin da yaki b'acemin yau ma da su ya jefeni kafin ya yi mgana ashe wayar na makale a kunnensa bai kashe ba naji yana Fadin"Is ok Papa i will call u later" Daga haka ya katse kiran kacokan kuma ya maida Hankalinsa kaina ni ko ban saba ganin irin wannan kallon ba, kaina na kasa ina rawan jiki Lokaci daya ina faman cikwikwiye hijabina ta gaba. Ina ga fahintar haka ya yi yasa ya yi mirmishin sa dake dimautani kafin ya matsa yana nuna min saman d'aya daga cikin kujerun falon Abba yana fadin"Barka da shigowa sarauniyar mata Hv a sit.." Sai kuma daya fada haka yayi yayi sauri gyarawa da fad'in"Ki zauna bismillah" Yafad'a duka a tare ai da sauri na samu gefen kujera na zauna ina kara Dukar da kaina sai kawai naji yace"Kada mu fara haka dake Fa'izaa kan kujera zaki hau a matsayin ki na Sarauniyar mata,ni kuma na zauna a kasa a gabanki tunda nine zan mika kokon barata." Da sauri na dago muka hada ido sai na Dirirince zan yi mgana ya yi saurin cewa"Kada ki fara da min gaddama Faa'izaa ni mutun mai son ya yi mgana Daya ajisa. kuma a Sauraresa" Yafada kai Tsaye cikin taushin murya mamakin kalamansa yasa na dago ina kallonsa kwarjinsa yasa na kasa mai gaddama sanda ya sake nuna min kujera yana fadin"Ga inda ya dace dake nan" A kunyace na mike na zauna kamar zan yi kashi,saboda yanayin zaman nawa sai ya yi dariya kafin na ankara sai ganinsa nayi a gabana ya zauna har da tankwashe kafa baki na bude ina kallonsa da Sauri yace"To Rufe bakin mana kada ya makale a haka na shiga uku" Mganarsa ta bani Dariya har sai da na kannen fuskata cikin Hijabi Saboda kunya shima yar Dariyan ya yi kafin kuma yadan ci Serious yace"Da farko dai ni sunana Abdulbasit Abdulghaffar Alowatosin.." Da sauri na d'ago ina kallonsa in naji dakyau sunan yarbawa naji ya fad'a shi kan shi yasan yanayin kallon nawa kenan yasa yayi dariya kafin yace"Yes ni bayarbe ne mahaifina Haifaffan garin Beneu ne,mahaifiya ce Bahaushiya haifaffiyar garin kano ni ruwa Biyu ne Hausa_Yoruba" Yafada kai tsaye bai kuma bani Damar mgana ba ya cigaba da fadin"Ni Engr ne ina aiki da matatan mai na Edo state,ni ba yaro ba ne ba Wasa ko bata Lokaci ko Doguwar mgana yasa nace ayi miki mgana ba. jiya ne da kika zo gaisheni na ganki to mganar gaskiya tun daga jiya zuwa yau baki bari zuciyata ta Huta ba Faa'izaa.." Ya fad'a yana kallona nima abun mamaki shi nake kallo ina auna daman akwai yarbawa masu kyau haka..?Na san maza masu kyau da gayu tunda na zauna da Ishaq ammh sai naga kamar wannan na gabana ya hada wasu abubuwa masu tarin yawan da Ishaq bai da su. Sai dai tunanani ya tsinke ne da nganarsa na karshe gabana ya fad'i kada dai shima jiya tunani ne ya kamasa kamar yadda ya kamani..? Sai dai ganin yadda na bada Hankalina a kansa ne ina jin yadda yake kiran sunana na shiga duka sassan jikina FAA'IZAA..! Gyara zama ya yi yana fadin"Kai tsaye ba tare da kwana kwana ko zagaye zagayen samarin zamani ba, na ganki kuma naji ina son ki Faa'iza kuma so irin na aure" Ido na waro a firgice kafin nace"Ni..? Sai ya gyadamin kai kafin yace"Yes..Ko ban kai ki soni ba ne..?nayi miki tsufa ko..?Shekarata arba"in da Biyar kiyi hakuri ban fara Furfura ba, a kai ne kuma bata wuce guda Biyar ba in baki so sai na aske su Faa'iza.." Dariya ce take neman kamani sai na kanne na juyar da kaina ganin yadda ya marairaicemin a gabana cikin yanayin muryata nace"A'a ko d'aya ai kai ba tsoho ba ne" Ajiyar rai yayi har ina jin saukanta kafin yace"To mene laifina ne..?ko so na ne kawai ba'ayi..? Kai na girgiza kafin nace"Ba haka ba ne" Da Sauri ya katse ni da fadin"To ya ya ne Faa"izaa..? Yadda ya kiran sunana sai da tsikar jikina ya tashi kai na girgizamai kafin nayi mgana yayi saurin fadin"Bana son mgana da kai. Ina son ko da wani Lokaci na rika jin muryan ki mai Dadi" Sai na saki hanci kawai ina jin abunda ban taba ji ba,ni daman ashe