← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 71

Sashe 71

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Dagani har Engr muna da Gajiya a tare damu,Jiya ma Musty ya koma makaranta tare muka dawo Abuja dashi su Ahmad kuma suna katsina zasu koma tare da Babansu.
Dagani sai Tauhidat agidan Engr na ta barcin gajiya sanda muka yi wanka ni da Taihudat mukaje gaisuwan safe.
Gefensa na zauna ina mai kuramasa ido ina kallonsa cike da mirmishi.
Addu'a da fatan alheri nake ta kwarara masa har sai da idanuwana suka ciko da kwallah.
Tauhidat na kallah dake gaurancinta tana yafito kafar Baban nata kallonta nake yi ita kadai ta Dauko kalan Fatata da kamata,Tamadina da Paa kuma kaf din su ahalin su Engr ta Dibo Tamadina Maa tace kamar kafayatu tana karama.
Kaina na kara kallo ina sanye da wani leshi mai Tsada ne,kimanin kudi dubi Dari da goma,na siye shi Saboda kalan mai ruwan zuma ne Engr na son kalan,a kayi min dinkin Buba yayi cif ajikina,Yau ba zan fita Shago ba, akwai yaran dake kulamin da shi ko bana nan in  wani abu ake so zasu kirani a waya.

Na kara kallon kaina naga yadda na koma cikin shekara shidda zuwa bakwai yadda Allah ya haskaka rayuwa ta.
Ni Fa'iza ban taba zaton watarana matakin rayuwa zai kaini ga haka ba ammh nasan naci Ribar Hakuri ne da addu'a.
Mijina kuma bani da bakin mgana sai masa fatan ya gama da duniya lafiya kuma yasa na zama matarsa a gidan aljannah bani da abunda zan iya rama masa alherinsa gareni.
Ashe Tauhidat tayi barci a hannuna ban sani ba sai da naji ta sunkuya sannan na kwantar da ita ta chan gefen na dawo na Zauna kusa da kafafun Engr na fara masa Tausa ina Fadin"Sannu Baban Anum aurar da y'a ba wasa ba.."
Nazata barcinsa ya yi nisa sai gani nayi ya Bude idanuwansa tar a kaina Ido na waro kafin in yi mgana ya yi caraf da hannayena bai yi wata wata ya fad'o dani jikinsa bayan ya jawoni.
Saman kirjinsa na fad'a ya kamani ya Rumgume kamkan na wani Lokaci muna jin bugun zuciyar juna
Kafin ya sausauta rikon da ya yi min yana Fadin"Ban gaji ba domin yanzu zan dora da shagalina ki bari in nagama sai ki min tausan gabadaya"
Na dago kaina zan yi mgana ya hade bakin mu Waje daya ya dade kafin ya Sararamin yana Haki yace"Tsakani ga Allah nayi hakuri yaron nan Mus'ab haka ya kirani yana godiya kuma nasan shima yaji dadin da nake ji ne indai Anum tayi gadon ki. ammh ni sai dai ayi ta min kwalele bata sab'uwa fa ina son kanwar Tauhidat ko kaninta.."
Dariya na saka ina fadin"Surukin zamani..'
Engr ya karishe da fadin"Kuma ya had'u da surukan zamani ba.."
Kai na girgiza nasan waye Engr har aransa shi Surukin zamanin ne ina fatan kada watarana ya bani kunya gaban mijin Anum.
Biye masa nayi muka sha shagalin mu Tauhidat na gefe tana ta sharan barci muka juya muka kalleta ni da shi kafin mu yi mirmishi.
Cikin sigan rad'a yace"Allah yasa na jefa kwallo a raga."
Yafad'a yana shafa cikina sai na Danne hannunsa kan cikina yana Fadin"Ameen Habibina Allah ya barni dakai har a Ajannah"
Saboda burina kawai na kara samun ciki ni da Engr mun yanke shawaran in mace na Haifa.
Goggon Karofi zan yi ma takwara.
In kuma Namiji ne Abba ne.
Ya amsa min yana sumbarta wuyana kafin yace"Allah ya yi miki albarka kin bani komai Faa'izaa. ya'ya mata,Kanwa,yaya,abokiya kece komai nawa kodayaushe fatana mu Dauwamana tare har Mutuwar mu kin zama ni na zama ke,Allah ya bamu Tsawon rai mu aurar da Amir da Musty da Ahmad sannan mu kai Tamadina da Tauhidat gidajen mazajen su"
Ina dariya nace"Ameen Lokacin ka zama Kaka Kenan..?
Wata muguwar Dariya ya yi kafin yace"Granny zamani ba. Ban yarda na Tsufa ba fa,ke kuma ai lokacin kin zama su Goggo Faa'izaa. Haka zaki ji ya'yan su Anum suna Goggo..Googgo..'"
Har yana kwatantawa na mintsine shi da hannu ina fadin"Kai kuma fa ya sunan ka..?
Yana dariya ya karya murya kafin yace"Granny.
Granny mana is in Stayel haka.."
A yadda ya fad'i sunan ne yasa muka fara Dariya dagani har shi.
Dariya mai cike da farinciki da nishadi.
nishad'in da nake fatan ya Dauwama har abada a rayuwarmu.

*ALHAMDULILLAH*!
*ALHAMDULILLAH*!
*ALHAMDULILLAH*!

*Nan na kawo karshen Labarin KANA NAKA. Kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min,in da kuma nayi daidai Allah ya ba ni lada*
*Godiya ta Musamman ga Masoyana da suka yi Tururuwa wajen siyan wannan labarin Tabbas kauna ce,nagani kuma na yaba Allah ya saka da alheri VIP001 Tare da FA'IZA'S HOUSE,jinjina ta musamman gareku tare da kyatattun Sharhin ku, Allah ya had'amu a gidan Aljannah Firdausi Ameen*
*Kafin na sake dawowa da wani sabon Labarin in muna raye,zan tallata muku sabon Littafin mu mai suna BAKAR TA'ADA.*
*Na marubuciya Surayya Dahiru gwaram,marubuciyar Halin yau da Sabo da kaza,ba domin tana kawata zan tallata muku labarinta ba,a'a sai domin yabon gwani ya zama dole kada ku bari a baku labari,Na tabbata zaku ji dadin sa kamar Kana naka kila ma fiye da Hakan in sha Allahu*
*Allah ya jikan iyayenmu da magabatanmu,Allah ya jikan Kawu Abdullahi Allah yasa yana Dausayin Aljannah Allah ya jikan Muhammad Tukur mijin kanwata Allah yasa yana Kyakyawan matsayi,Allah ya gafartama Alhaji Abubakar Mijin Ummi Allah yasa chan ta fiye musu nan Gabadaya. Mu kuma Allah yasa mu cika da kyau da imani Ameen ya Rabb*

*INA SON NA MAIDA KANA NAKA ZUWA HARDCOPY.*
*AMMH HAKAN BAZAI SAMU BA SAI DA HAD'IN KAN KU,IN AKWAI MASU BUKATA ZASU IYA MIN MGANA TA WANNAN LAMBAR 09069067488*

*Janafty*
*02/08/2023*
*JAMILAUMAR*

 
Chapter 71 · 0% Book details