Sashe 54
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read
din Engr fara zamu tafi dagani sai shi sai Direba. An kai ni wajen Hajiya kudirat ta sakamana albarka sannan ta bani kyautan warwaro da ashoben su da murjanai,sai duka kannen Papa da yayyensa suma na samu kyatuttukan na kudi da kaya tare da addu'a daga garesu. Gabadaya kuma suka rakomu har bakin mota,Abaya na saka maroon mai zanen baki sai Nana Fatima tamin nadin mayafin baki nayi kyau sosai duk da ina kin sakawa sai gashi na saka takalmin kafata ma baki ne,mai Tudu duka kayan jikina ba na kudi kad'an cikin ma wanda muka siyo ne da Ammi ne. Ina ji ina gani Ammi ta sakani a mota suna d'agamin hannu Engr ma ya shigo Direba ya rufe shi ya tsayama Lallashin Anum ammh tana ta kukan sai ta bimu a raina nace Anum ta girma bazata daina shagwaba ba. Mun dauki hanyar Edo cike da kewa na tuna Maa yadda ta rika sakamana albarka da fatan zaman lafiya itama tace duk abunda nake so na kirata ita uwa take gareni. Hawaye haka suke bulbulomin Duk Dauriyan Engr haka ya rumgumoni yana Lallashina kamar karamar yarinya fad'i yake"Shii..am sorry matata..Ko mu koma ne kawai mayi shagalin mu achan..? Wata uwar harara na Dago ina hawaye na makamai sai ya yi Dariya yana Fadin"To ba ke bace kina ta kuka ina kike so na saka raina don Allah..? Hawayen ya fara sharemin yana Fadin"Kin yi bamkwana da kuka har Abada sai dai na farinciki. Ki bari kawai mu sha kara'in mu ba gani ba..?ko ni ne baki son gani kike kuka saboda mun baro su..? Sai na kasa mgana na sunne kaina a saman kirjisa ina mirmishi kamar yadda na yace bayason kuka dole na shanye hawayena ina ji ya saka hannayensa duka biyu ya rumgumoni. Kaina na saman kirjinsa yana lallashina kamar wata karamar yarinya ni ko na lafe ina samun natsuwa Lokaci d'aya da natsuwar zuciya. Sai kuma na fara tunani had'e da kuma Fargaban wata irin kuma rayuwa zan fara gudanawar tare da Engr..? Shin wani irin bambamci zan samu a zaman aure na da shi..? Fatan farinciki nake yi ma kaina ko ya ya ne. Fargabata har da yadda nayi aure abunda ban taba tunanin yinsa nan kusa ba.