← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 71

Sashe 8

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwantar da Hankali ki kira Fadilan sai ta baki Ahmad din kiji muryansa ko..?. Kunya ta kamani na noke fuska ina yar Dariya mun dade muna Hira da Abba yana ta jana da wasa domin ya kwantar min da Hankali,daga karshe ya bama Ammi itama ta rika Lallashina nan da man naji zuciyata tayi sanyi Hankalina ya fara kwanciya kunya da nauyi yasa na kasa kiran Anty Fadila kamar na kira zainab sai na rasa me zan ce mata ganin itama bata nemeni ba. Zama na gyara waya a hannuna ina jiran kiran Anty Fadila har goma ta gota bata kira ba,Duk kuma sai na Damu kamar na kira wata zuciyar sai ta Hanani,goma da minti shidda sai ga Kiranta da Rawan jiki na Daga,cikin sanyin murya na gaisheta ta amsa Lokaci daya tana fadin"Ya jikin ki Fa'in mu..? Kai tsaye nace"Naji sauki Anty Fadila" Ina so na tamnayeta jikin Ahmad kunya ta hanani kamar ta sani sai tace"Ina asibiti,dayake aikin Dare gareni ga Ahmad yau ya kira Umma yafi sau dubu" Murna ta kwace min na kasa mgana har sai da naji Muryan Ahmad yana Fadin"Umma."Umma..ni zan dawo wajen ki" Sai kuka na rud'e na mike har hijabin jikina na neman kadani Cikin rawan murya nace"Ahmad din Umma..Daina kuka kaji ko..? Kamar yana ganina ya fara goge hawayensa yana fadin"Umma ina ta kuka ina kiran sunan ki baki zo ba Umma yaushe zaki dawo..? Ina sharan hawaye nima nace"Kayi hakuri Ahmad din Umma zan zo in dai ka sake kirana ya jikin ka..?ka warke ko..? Da kai ya amsa min cikin muryan Kuka yace"na ji sauki Umma Anty Fadila tamin allura,Anty Zainab da Daada sun kawo min nama Umma" Cikin jin dadi nace"Sun kyauta kaci abinci sosai sannan ka rika shan mgani kaji ko Ahmad di'n Umma..? Da sauri yace"Umma yaushe zaki zo..?mu kadai ne a gida daga Daada sai Anty sai Mama ke baki zo ba" Cikin karfin hali nace"Ka rika shan mgani ka warke da wuri in dai kana so nazo na ganka" Da Sauri yace"To Umma zan warke da wuri" Cikin jin dadi nace"Yauwa Yaro na ina sauran yan'uwan ka..? Ina yaya Amir ina Yaya Anum? Bai yi mgana ba sai naji ana mgana kafin naji muryan Zainab tana Fadin"Maman Amir" Nima sai na maida mata da fadin"Maman Fadil mutanen ikko" Ajiyar rai ta sauke kafin tace"Ba kin ki mu ba Maman Amir..? Ga Ahmad rigima duk ya rikitamu baya yarda da kowa sai Amir ko Anum har Honey baya yarda da shi yanzu shi dai Umma Umma. Don Allah Umma ta Dawo wlh gidan ba Dadi da baki nan" Sai nayi mirmishi Lokaci d'aya ina sharan kwallah kafin nace"Daman gidan bai taba karban bakuncina ba to bakomai ba ne in bana nan Maman Fadil ba ga ki ba?nasan zaki kula da su" Cikin Jimami tace"Nima kinsan ba iyawa zan yi ba. Allah yasa ma nazo da Yarinyar nan dake min Reno. ita ke tayani Dawainiya da yara" Cikin Tausayawa nace"Wlh ga shi kin yi nauyi,Allah dai ya raba lafiya" Ta amsa min da Ameem kafin tace min ga Amir ta mikamai wayar ban san ko Ishaq na dakin ba,Domin banji Ko Tarin sa ba Amir bai yi kuka ba sai dai shima Muryansa a sanyaye ya gaisheni na amsa ina fadin"Amir kana kula da Sauran kannen ka ko..? Kai Tsaye yace"Eh Umma. Ahmad ke kuka kullum Mutsy ma nayi. Umma yaushe zaki zo ki Daukemu mu wajen ki zan koma? Tausayin yaran ya kamani Cikin Dauriya nace"Zan zo watarana Amir..Ya mganar makarantar Boko kun fara zuwa? Cikin sanyin murya yace"Sai Ranar Monday zamu fara zuwa makarantar su Fahad din Anty Fadila Daada ya sakamu" Cikin murna ta nace"Eyee yan gatan Daada islamiya fa..? Kai tsaye yace"Ba'a sakamu ba Umma" Sai na jinjina kai kafin nace"To kace ma Daadan ku ya saka ku kaji ko..?.ya amsamin da toh sannan na sake gyara zama ina fadin"Amir kai ne Babba ka Kula da sauran kannen ka,Ka rika musu Bitar karatun Qur'ani kai da Anum Tunda kin yi nisa ku rika karanta azkar Safe da yammah,ban da abokan banza Amir ban da wasa na rashin gan gado,ka rika taimakon kannenka bangaran karatun Boko da na islamiya,kuma ku zama yaran kirki ban da damun su Daada kada ku ki jin mganar Antyn ku,duk abunda tace ku yi ko ku bari ku ji mganarta,kun samu bambamcin Muhalli ba kamar katsina bace Lagos Amir don Allah ka kula da kanka da kannenka, ku rika sallah akan Lokaci kuna yimin addu'a kuna yi ma kan ku kaji ko.? Cikin Sanyinsa yace"In sha Allahu Umma" Cikin jin dadi na sakamai albarka sai ya bama Anum wayar itako kuka ta sakamin tana cewa itama waje na zata Dawo sai da na Lallasheta da zan zo sannan tayi shuru itama fad'a na rika mata ina Fadin"Anum ke macece kin sani ban da waasa da maza a makaranta ban da kawayen banza Anum,azkar Safe da maraici kun iya karatun Qur'ani ku rika yi in da kika karkare yayan ku ya Tadake,ki kula da kannen ki gabad'ayan su Anum ban da rashin ji ko Rashin kunya ku ji mganar Daada Data Antyn ku in wani abu ya shige miki Dubu ga Antynku ga Mama ga Babanku duk zaki iya tambayan su kin ji ko? Ta amsa min da naji Umma,mganarta tasa jikina yin sanyi da nace ta mika ma Musty wayar kafin ta basa sai tace"Shikenan Umma bazaki dawo nan da zama ba..? Sai na kasa mgana na Dauke Hawayena ina fadin"In Allah ya yi zan dawo Anum" Daga haka bata kara mgana ba ta bama Musty wayar shima duk yan Rigiman ne sai da nace zan zo gobe sannan ya koma yana bani Labarin agidan Anty Fadila an siya musu wannan an siya musu wannan yana gayamin Ahmad bai da lafiya suna ta kuka,Sai da Fadil ya kwace wayar shima duk labarin kuruciyar ne,Mun jima muna mgana da su wayar daga kunnen wannan zuwa wannan sai da naji kamar Muryan Yaya ishaq na Fad'in tafiya za su yi sai naji mgana dai sama sama kafin wayar ta katse na samu natsuwa da nayi mgana da ya'yana sannan na kuma Tabbatar da Ahmad na nan da ransa bai mutu, kamar yadda nake Hashashe ba. Sai alokacin naji yunwa ta taso min na zare Hijabin jikina na fita Falo ba kowa kila Goggo na Dakin mallam Kitchen na shiga ina neman abinci sai ga Goggo ta shige muna Had'a ido tace"Kin gama kukan ne kuma kika Fito neman abinci..? Sai na kasa mgana itama bata kara mgana ba sai da ta Dauki abunda zata Dauka sannan ta fice tana Fadin"Ki duba flalks din nan akwai ruwan zafi ki sha sai ya warware miki ciki yadda kika yini baki ci komai ba" Naji dadin shawaran Goggo tea na Hada mai kauri na sha sai zufa nan da nan naji na fara dawowa Daidai sannan na Dora da doya da miyan da Goggo ta Dafa a cikin kitchen din naci na koshi na kora da ruwa sannan naji ni na dawo cikim Hayyacina. Ranar barci nayi har da makara Washegari tunda Goggo taga na tashi Garas ina walwalata sai ta kalleni tace"Hala kun yi mgana da yaran ne..?. Kai tsaye nace"Eh Umma jiya nayi mgana da su har Ahmad din yaji ma Sauki" Sai Goggo ta gyada,kai kafin tace"Dakyau! Allah ya kara lafiya" Ta Fahimci farinciki a Fuskata. A ranar aka sallame su suka koma gida Anty Fadila na kira ta fad'amin sai na Kira wayar Zainab bayan mun gaisa da Tambayam mai jiki sai ta bani Ahmad da Sauran yaran muka yi mgana suma na Lura sun fara walwala da jin muryata. Da nace bazan nemesu ba sai sun saba da Rashina ammh ban san nayi Fatali da wannan Tunanin ba sai da naga kullum Safiya sai na kira mun yi mgana da su,Ranar da zasu fara zuwa makaranta Zainab ta kira da Safe ta fad'amin harda Ahmad Tunda ya warware tace babansu zai rika kaisu tunda ya siya mota in an tashi Direban gidan Anty Fadila in ya Dauko su Fahad zai rika sauke su agida an basu waya,mun yi mgana nayi ta musu nasihan kada su manta da karanta addu'an fita gida da azkar tare da natsuwa suka tabbatarmin da bazasu manta ba. Naji dadi hankalina ya kwanta Tunda Ahmad ya samu sauki sannan ya Daina Rigima,kuma Yaran hankalinsu ya kwanta tunda suna mgana dani,Jamal ashe sanda Ahmad yayi ciwo yana kano yazo kamallah Takardunsa sai daga baya ya koma sai naji Dadi da Amir ya fadamin yana yi musu Lesson agida kafin ya samu Tafiya bautar kasa ko bakomai shi yana gidan zai kula da wasu abubuwan sai na samu natsuwa Hankalina ya kwanta ammh fa ko ban kira su ba zasu dauki wayar Antynsu ko ta Mama su kirani Amir da Anum tuni sun haddace Lambata. Sati uku Tsakani Abba ya yi min waya cewa gobe suna tafe shi da su Inno yadda bai cemin komai ba nima ban kawo ba sai a daran Anum ta saci Wayar Mama ta kirani tana murna tana Fadamin gobe zasu zo wajena In ji Daada, sai Hankalina ya tashi na rasa ta ina zan kama mganar Cikin Tashin Hankali nace"Ke Saudatu bana son karya" Da Sauri tace"Wlh Tallahi Umma har da ma Mama fa zamu zo Anty kad'ai zamu bari a gida" Sai na yarda da ita domin tasan ai rantsuwa in kayi karya na shafa Fada musu ba kyau,Da Sauri na katse wayar sai na rasa wazan tambaya tuna Goggo yasa na kwashi gudu na Fita bata afalo tana Dakinta ina shiga na isketa tana zaune tana jan Cashaba ina Tsaye a kanta nace"Goggo Abba yace min zasu zo gobe..?akwai abunda zasu zo yi ne" Kallomta tayi da mamaki kafin tace"Eh nima mun yi mgana da shi Inno ne da Baba ati zaso zo dubaki wani abu ne? Kai Tsaye nace"Anum ta kirani da wayar Mama tace gobe Babansu yace zasu zo wajena, har da Mama itama" Goggo tace"To ni ban san wannan ba kira Baban naki kiji" Goggo ta fad'a tana kauda kai ni ko hankalima ne ya tashi bana so ya kwasomin yaran nan ban kuma san yadda zan yi da su ba. Sai na kada
Chapter 8 · 0% Book details