← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 71

Sashe 66

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya sauyamin gida ba,Dakyar ya lallasheni na dawo da alkwarin zai sauyamin gida na ni kadai ammh kuma mgana ta shiriran ce,Shekaran jiya matarsa tazo gidan tana ta zagina tana ce min Juya in sha Allahu dukiyar da na shigo ci bazan sameta ba har tana zagin Ubana dake Kabari ni kuma raina ya baci na Rama shine ta jani da Dambe har mukayi fad'a,Du keni in Daketa muka yi Lokacin Hajiyar bata nan daganan sai akace taje gidana gaishe da Hajiya bata nan najata da fad'a har nayi Sanadiyar barar mata da ciki daman ina bakin ciki. Yusuf baya nan ammh Hajiya ta kirasa a waya tace ko ya sakeni ko yaga bacin ranta. Shi ya kirani yana kuka yake fad'amin ni kuma da naji haka nace gwara a rabun kowa ya huta tunda yaki saki na sai na zabi na tafi inda bazai ma sani ba ballatana ya nemi shiyasa na yanke shawaran zuwa wajen ki Anty Fa'iza na tabbata ko kowa bai Fahimceni ba ke zaki Fahinceni" Kafin ta gama bani labari naji raina yayi wani duhu jikina duk ya yi sanyi Badariya mai kaunata ce ban so kaddaranta tazo a haka ba, ammh kuma bawa bai isa ya tsara ma kansa Rayuwa ba,muna namu ne Allah kuma na nashi nashin ne kuma na gaskiya. Kuka take yi kamar ranta zai fita ina Lallashinta da ban hakuri kfin nace"To yanzu shi Yusuf din yana ina..? Badariya tace"baya nan,Rabo na da shi tun jiya a fligth mode na saka wayata,mun rabu dai yace yayansu yace ya dawo sai a zauna kada ya sakeni sai indan ya dawo ni kuma daman na shirya tafiyata Shiyasa ban Tsaya ba" Tun daga yanayin mganarta nasan da gaske ta gajin,sai ban matsa mata ba na kyaleta sai dai nayi ta bata baki da ban hakuri kafin na barta naje nayi wanka na shirya ko da na fita falo su kafaya sun tashi suka gaisheni na amsa sun shirya zasu shiga makaranta sai nace su dibi abun karyawa su karya kafin su fita ni kuma na Dibar mana ni da Badariya na kaima har Daki. Abincin ma dakyar ta sauko taci,Tasha dai tea,sai Soyayyan Buredi shi kuma kadan taci sai amai haka ta shiga Tiolet tana kwarara shi ni dai ban ce mata komai ba ne ammh naga Ciki Sabo a tare da Badariya. Su kafaya kafin su fita har Daki suka shigo suka Duba Badariya sannan suka min sallama suka tafi makaranta Dukkansu sun iya mota,suna da kuma Motocin su yau wannan ta tuka gobe wanchan ta tuka. Suka barmu da Badariya tana bani labarin zaman hakurin datake yi a gidan Yusuf ba kwanciyar Hankali,ni kuma ina kara Tausanta da kalmar nan ta Hakuri ita na rike kuma naci Riban Hakurina. Sai yammah Dr din yazo ya kawo sakamakon bayan ya yi mata bayanin tana da shigar ciki na wata Biyu da wasu kwanaki ta kiyaye aikin wahala sannan ta rika cin abinci ta samu Hutu Badariya ta kasa mganar har bayan Tafiyanta ni ce nace mata"To ina zaki kai wannan rabon Badariya..? Baki san abunda Allah ya kaddara Tsakanin ku ba tace ke da Haihuwa sai dai kiga anayi tun ba'aje ko'ina ba sai Allah ya nuna mata bata isa ba. Kinga sunan juya da suke kiran ki sai ya kare daga yau" Bata ce min komai ba sai dai tana ta sharan kwallah Saboda matsalan Badariya yasa sai dare muka yi waya da Engr da ya tambayeni ya ake ciki na Fad'amasa yadda ta fadamin da kuma cikin da aka gano a jikinta. Engr ya fara fad'a yana fadin"Shima dai kamar wani sakarai haba .Ba'a haka sai ya sulhunta lamarin ita matarsa ai karkashinsa take in bata son a zauna lafiya ya yi mganinta mana ita kuma mahaifiyarsa matsayinta Dabam ya kamata in dai yana son matarsa ya san yadda zai iya gyara kowani bangare ammh a bar yarinya na Fuskantar wannan matsalan bai Taso ba Faa'izaa ki riketa a wajen ki Sati mai zuwa zan dawo da kaina zan kira mijinta mu yi mgana, in yana sonta ya gyara gidansa in kuma bazai iya ba to kowa ya kama hanyarsa" Har mamakin Engr na rika yi haka yake da fad'a sai dai nasan shi baya Daukan re ni jarumi ne kuma jajirtattace ne,Da na fad'ama Badariya abunda yace sai taji dadi jin yace zai Shiga mganar zuwan Badariyq yasa su kafaya suka koma gida nima da Badariya ta kara jin sauki munje da ita ta gaida su Maa muka yini achan sai Dare Direba ya maidamu gida. Badariya sai fadi take yi"Gaakiyan dangin mijin ki masu karamci ne Anty Faa'iza" Sai dai nayi mirmishi Saboda abunda na sani ne aka sake fad'amin. Kafin satin da Engr zai dawo Badariya ta murmure tunda ina takura mata taci abinci duk da tana amai ga laulayi da Zazzabi take kwana,wayarta tana Kashe shiyasa bamu ji labarin irin neman da Yusuf ya yi mata har Lagos ba,Da kuma irin yadda Hankula suka tashi tunda duk an nemi kowa bata wajen su ni kuma kila ana tunanin ina amarci kila Badariya baza ta zo wajena ba. Sai ana gobe Engr zai dawo zainab ta kirani a bakinta nake jin hankulansu duk a tashe suke Badariya ta bar gidan mijinta ba'a san inda take ba. Tana bani Labarin yadda Hankalin Mama da su Yaya ishaq ya tashi da shi kan shi Yusuf din sai naji kamar na gayamata gaskiya sai kuma na fasa akallah dai na jira dawowan Engr sai na tada Hankalina na nuna Damuwata da Alhini na. Bayan mun gama wayar na fad'ama Badariya sai ta tabe baki tace"Mama da yan'uwana kawai na damu ammh ba domin Yusuf ba" Ban biye mata ba,ganin yadda tayi fushi illah na rika ce mata"Ke dai fad'i gaskiya kin yi kewarsa sosai ma ko baki yi don komai ba kya yi saboda abunda ke cikin ki" Gajiya tayi ta kyaleni tunda taga na Rike mganar na ki saki,Washegari da Shirye Shiryen Dawowar Engr muka tashi,Badariya ta kama mun muka yi masa abincin kala kala na saukansa jirgin yammah ya biyo sai bayan mangariba ya iso gidan. Lokacin n cakare cikin Riga da sikat na Atamfa mai ruwan ganye cikin kayan akwatin daya dinkamin ne Tunda anan Abujan Maa ta bada aka dimkamin bayan na fad'a mata Measurement dina. Kayan sun karbeni Saboda Daidai jikina ne Badariya tamin Saukakkiyar kwalliya hade da Daurin maryam babbangida sai nayi kyau dani kamar a Sureni a gudu.. Ai ko Engr cak ya sureni haka ya Dagani Sama bai ji nauyi na ba,ya rika zagayen falo dani ni kunya duk kunya ya kamani ganin Badariya na wajen ashe tun Rumgumar Farko ta komaa ciki ta bamu waje. Dakyar na iya lallabasa ya yi wanka ammh sai da ya yi kara'in nasa dai ta bakinsa dai ba yayan ya yi ba kanin ne duk ya batamin kwalliya yasa sai da na gyara Daurin d'ankwalin Tunda har kan sai da ya sha Jagwagwala. Sai bayan ya yi wanka ya yi sallar mangariba da aka kira Isha'i sai ya jamu jam'i ni da shi bayan mun Idar ne muka fita falo na gabatar mai da abinci sai yace na kira Badariya su gaisa na leka na sameta itama ta Idar da sallar Dariya naga tana yi min sanin Dariyan da ma'ananta yasa ban tanka mata ba ammh ina ce mata Engr na mgana afalo ta mike tana Fadin"An gama yar shillan dake..? Sai na juya baya ban kara yarda mun hada ido ba na fice ina mirmishi. In na zauna ina kod'a Engr sai aka ga kamar ina zugasa ne ammh mganar gaskiya Engr shi ya kaini duniyar ma'auratan da bansan ma akwaita ba. Shi ya jiyar dani irin Dadin da mata suke ji a tare da mazajen su. Shi ya kara fahimtar dani aure da zamantakewa ashe ni a baya wahala kawai nayi,ban taba Dauka haka Aure ke cike da Ni'ima ba sai da na Samu Engr. Duk da kowani aure yana da nashi kalubalen,zo mu zauna a kace zo mu sab'a,ammh ni ta bangare na cika da Hamdala na kuma kara da Alhamdulillah. Tunanin da ya cika raina kenan ina zaune gefensa yana cin abinci sama sama yake mgana saboda bai cika son mgana in yana cin abinci ba. sallamar Badariya da shigowarta falon yasa ya Dakata ya dago yana amsawa Nesa dani ta zauna tana gaisheshi ya amsa cikin fara'a kafin yace"Matata zubo muku abincin mana tunda na lura yau wareni akayi tunda naga an zubamin nawa ni kad'ai" Mirmushi nayi kafin nace"Ni bana jin yunwa ne shiyasa sai dai in Badariya" Da sauri tace"Anty Fa'iza ki gayamasa mun ci da muka gama girkawa tun a bakin Tukunya" Hararanta nayi shi kuma sai ya kada kai yana fadin"Fa'izaa na yafe miki ba ma sai kin nemi gafarata ba" Dagani har Badariya muka yi Dariya matsamim ya yi sai da muka saka abincin muka ci kad'an tunda gaskiyanta ne tun a kitchen muka koshi sai dai an dauki Lokaci cikin ya Zazzage. Saboda gajiyan dake jikinsa yasa yace sai da safe zasu tattauna da Badariya da wuri muka shige ciki,saboda yana ta fad'amin ya yi kewata in zai koma kafata kafarsa bazai iya ba. Ai ko naga kewa haka ya rika min rawan jiki da Sambatu ni kaina na karbesa dakyau tunda nima nayi kewarsa sosai Rayuwa juyi juyi sai ga shi ni Fa'iza ke son al'amarin a baya Wlh tallahi al'amarin bai taba dad'ani da kasa ba. Da Asubaa yana kwance ni na tsokane sa muka buga kafi siga dad'i,Da safe ma kafin mu tashi yace zai kara na bata fuska ina Fadin"Baka gajiya ne..? Duk sai ka tsotseni ko..? Yana dariya ya kamoni yana Fadin"Bamu gajiya zaki ce. kema ai ba gajiyan kike yi ba in fa kika ji ni nayi kamar zan sauka sai ki yi saurin rikeni kina Uhm uhm" Ya karishe fad'a yana kwaikwayon yadda nake yi ga kunya ga Dariya Engr halinsa sai shi bakina ya Mutu murus na kasa mgana ya sumbaceni kafin ya Dagoni yana Fadin"Bafa tsotseki zan yi ba. Yarinya ina da Fertilerzer mai kyau kinga yadda kika koma..?Tife din gaske kenan ke da zaki bani dama nayi ta damawa ina cigaba da kara'i
Chapter 66 · 0% Book details