← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 71

Sashe 42

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka na kamkame takardan ina kuka wannan wani irin shiga tsaka mai wuya ne..?bana duba ban kuma san wani irin zama zan yi da Engr ba, ammh ina masa kyakyawan zaton zan samun farimciki ko da ba duka ba a tare da shi Fiye da yadda na samu a tare da Ishaq sai dai ya'yana su nake tunawa bana so a wannan karon ma na kara karya musu zuciya, shiyasa na yanke shawaran komawa in dai su zasu yi farinciki na amince ko da nawa Farincikin zai samu tawaya. Kwata kwata bana jin Farinciki ko annushuwa kan maida aurena da Ishaq,sai ma wani kunci da nake jin yana mamaye ruhina ina ji ajikina kamar zan koma gidan Jiya ne,wanda fa yace baya sonka to har abada baya sonka sai dai kila Daga baya ya Fahimci kana da wani Muhimmanci a Rayuwarsa ne shiyasa ya Damu ya kai. Ammh nasan waye Ishaq ni ba Zabinsa ba ne bazan kuma taba samun Farinciki daga garesa ba.. Gobe ne za'a maida auran mu ammh mgana ta Fatar baki bata had'amu ba,koma ya tambayeni wani shiri nayi..?hakane soyayyar..?na fi Tunanin shima Saboda ya'yan mu ne sannan kuma da Tasirin zama tare da shi ba Domin muna da Fahimtar juna a tsakanin mu ba. Na yarda da wani tunanin masana Soyayya,ita soyayya tana ginuwa ne tare da Fahintar juna,ban dad'e da Haduwa da Engr ba ammh ya fahinceni nima na Fahincesa fiye da yadda Ishaq ya Fahinceni shekaru kusan goma sha da auren mu nima yadda na Fahimci Engr wlh ban Fahimci waye ishaq ba. Saboda bai bani Damar haka ba abu daya kawai ya bani wanda zan Daki kirji na nuna shi shine ya maidani uwa ya bani Ya'ya bayan su a zama da shi ban san komai ba, sai Tozarci da wulakanci sai kuncin zuciya da ciremin dukkan sha'awan aure acikin raina. A Daran ranar nayi kuka sosai kukan da bansan iyaka ba,Ina kuma kamkame da agogo da yar takarda a Hannuna ina ji ana kwankwasa kofar naki Budewa,inaga ganin halin da nake ciki yasa suka kyaleni. har Biyu na Dare idanuwana Biyu,gajiya nayi da kukan na tashi na Dauro alwala na shiga Sallah bayan na Idar na Daga Hannuwana sama ina fadin"Ya Allah ga baiwarka nan Fa'iza kaga zuciya ka ga zabina sai dai na baka zabi. Sai ka zabamin Ishaq a karo na biyu..Ya Allah ina rokon ka da ka tabbatarmin da alheri ka bani natsuwar zuciya da kwarin gwiwa shi kuma Engr yadda ya kaunace don Allah,ka basa wacce zata kaunace sa shima domin ka,ka cire masa damuwan rashi na,ka yi masa kyakyawan Sakamako irin sakamakon da kake yi ma bayin ka Salihai masu Hakuri" Ina addu'a ina kuka Sauran Daran da karatun Qur'ani na raya su kuma na Bude muryata har ma karatun ya tada wasu da asuba sauran kuma Dakunan su na Bisu na buga musu sannan na koma na tada sallar Raka'atul Fijir. Ina sallamewa na Dora da Sallar asuba bayan na idar ina azkar barci ya rika Fizgata nan saman Darduma na bingire da barci ban ta shi ba sai tara na Safe kuma Daurin auran karfe Daya ne ina ta shi ba kowa a dakin, sai ni a firgice na tashi da ganin rana har ta fito,hayaniya na rika ji a tsakar gida ina lekawa naga suna ta ayyuka kamar ma sun gama abincin share share suke yi. Nana Fatima ce ta shigo falon Goggo tana ganina tace"Amarsu kin tashi..? Ina tura baki nace"Shine baku tasheni ba..? Tana Dariya tace"Mu tashe ki mu yi laifi..? Ban ce mata komai ba na juya na koma Daki har ga Allah naji zuciyata ta samu natsuwa kuma na samu saukin Al'amura naji na samu natsuwa Dari bisa Dari,wanka nayi tunanin na fara yi na shirya kafin mutane su fara taruwa duk da ni ban yi gayya ba ammh nasan Goggo tayi gayya kuma wasu mutanen arxukan ko ba gayya sai sun shigo. Bani da wani zabi sai na Ubangiji kuma Tunda ya zabanin Ishaq to bazan yi Butulci ba na karba Hannu Bibbiyu. Ina wanka Abba ya shigo gidan saboda ta bayin ne tsakar gida ina jin mganarsa,har yana tambayana shiyasa da na fito na shirya a gurguje cikin,less riga da zani ko kallabi ban saka ba na zumbuda hijabi na fita Falo muka gaisa da Abba da Mallam Sai Amir da ya taho wajena yana Fadin"Umma ina kwana" Ina shafa kansa na amsa masa chan ya kwana wajen babansa. Zama na yi a kasa Mallam ya bamu waje tunda kamar Abba na son mgana dani ne. Cikin dattakonsa ya kalleni yana Fadin"Ya kuka yi da shi Ishaq din kan mganar tafiyarki..? Kaina na kasa Amir na gefena nace"Ni bamu yi wata mgana ba Abba" jinjina kai Abba ya yi kafin yace"Shikenan in an Daura auren sai ku yi mgana in zai wuce dake ne sai na baki kudin kayan Dakin ki yar'uwanki ta rakaki ki siya abunda kike so. ina Tunanin kila tare zaku koma" Gabana na fadi ammh na cije sai kiran sunan Allah nake yi acikin raina,Abba ya yi ta min nasihan da suka kara sanyayamin jiki,haka Inno da Baba ati suna ta bani Hakuri da Nasihan zamantakewar aure. har Abba zai fita ya tuna ya Dawo da baya yana fadin"Kin ga na manta ki kira Engr ki yi masa godiya 300thousand ya turomin yace a baki,ko kuma ma kije chan gidan ku gaisa ki yi masa Godiya,Engr mutum ne mai kirki har ga Allah a zuciyarsa komai ya wuce, yace ke ba Rabonsa ba ne" Kai na kasa na Daga ma Abba kai,ina son tashi ammh na kasa bani da kwarin gwiwan Fuskantarsa yasa nayi zama na Badariya da Nana Fatima ne suka jani Daki suka tasani gaba da tsiyan sai nayi kwalliya Gajiya nayi na kyalesu suna min kwalliyar a waje kuma Yaya Asiya ke fadin ko kayan gyara ban sha ba, Ammi naji batace komai ba saboda Ishaq ne yasa bata bani komai na shafa ba, ammh da Engr ne da an ga Ruwan gyara kuwa. Yaya mariya ne tace tana da wasu sai a bani na sha Goggo kuma tace kwanaki ai ta bani na tsumi na sha da tace na mganin sanyi ne achan Daki kuma sai da sukamin kwalliya suka min Dauri sai ga shi na fito ras dani Allah yasa daman kaina ya Tsefe yake Kunshi ne ban yi ba. Badariya sai fadi take"Kina gyara wasu amaran ammh ko yar Dilkar nan bazaki kwama kan ki ba..? Nana Fatima tace"Ba kuma turarren kamshi ta kuma iya had'a ma wasu ammh ita ko na goga ma jiki bata da shi" Duk ina jin su ban ce musu kala ba ina da Turaruka suna cikin kayana ne ban fito da su ba, Tunda ba amfani zan yi da shi ba kuma ma ina da Zallar madaran Turaren ban dai hada ba ne. Tunawa nayi da mganar Abba yasa nace musu zan fita Amir ya fice tun dazu kila yana wajen babansa. Sai kuma na rasa yadda zan yi na fita sai na ari wayar Hafsah na kira Abba na tambayeshi suna tare da Engr ne..? Abba yace basa tare sun fita da mallam Shi Engr na gida naje nayi masa godiya. Kunyar zuwa ni kadai yasa naja Nana Khadija nace ta rakani,na saka Dogon Sabon Hijabina mai ruwan madara da takalmi,goggo kawai na fadama inda zani ta kalleni cikin wani yanayi kafin tace"Yakamata kam sai kin dawo" Suna ta faman tambayana ina zani nayi musu banza domin haushin su nake ji suma. Muna fita waje muka hadu da Yaya isa da su Yaya Salisu muka gaisa suna ta zolayata mun wuce kenan sai ga Yaya Ishaq da Amir,har ga Allah ni ban gan su ba ance hankali ke gani ni kuma ina chan tunanin haduwata da Engr suna ta mana mgana ban ji ba hatta Nana khadija bata gan su ba tunda suna ta gefen hanya ne. Shi kuma yana ganin mu mun nufi gidan Abba sai yayi tunanin ko shi nake nema sai suka biyo bayan mu. Tunda tun safe suna tare da Engr suna ta Hira mutum ne mai ilimi ba ruwansa ga sakewa da mutane. tun a jiya Abba ya yi masa bayanin shine Ishaq din da ya kirasa kan mganarsa da EFCC har yasa mahaifinsa ya shiga ciki,Engr na ta mamakin daman shine mijin Fa'iza kenan..? Ko a fuska bai nuna masa komai ba suka cigaba da tattauna mganar aiki Sai Ishaq ya Fahimci Engr mutum ne da yake da ilimin rayuwa da wayewa ga shi bai da girman kai duk ko da matakin Rayuwar da ya samu ya yi mamakin da yaji sunansa ashe bayarbe ne..?ko a kama ko a mgana ba shi da kama da yarbawa Allah mai hikima kenan.. Dayake gidan shashe biyu ne shashin da aka bude na Abba sai nayi Tunanin yana ciki muna kokarin shiga Nana Khadija tace min wai fitsari take ji nace mu shiga tayi tace a'a bari ta koma gida tayi ba'a son raina ba ta koma tana fita suka hade da Ishaq a Hanya shine yake ce mata ya gansu yana ta mgana basu ji ba.. Nana khadija tace"Laa bamu lura dakai ba dayake muna ta sauri Anty Fa'iza tace na raka zata je wajen Engr" Gaban Ishaq ya fadi bai gane zata je wajen Engr ba..? Bai gama tunaninsa ba Nana Khadija yace"Tana chan ni zan koma gida ne na Dauki wani abu" Fitsarin ne ya matseta sai ta wuce da Sauri bayan tace Amir yazo ya rakata sai ya noke wajen Babansa. Ishaq kasa gaba ya yi ballatana baya haka kurum yaji shakku a ransa. Sai da Amir yaja hannunsa yana Fadin"Muje Daada Umma na chan na jiran mu" Kamar an jasa haka ya shiga Binsa har gidan. Suna bakin kofar falon sukaji Muryan Engr na fadin"Faa'izaa..Son da nayi miki daga Allah ne. Don kuma na rasaki sai na butulce masa..? Sai kafafun Ishaq suka fara rawa jin kalaman Engr,sai dai kuma bai jin mganar Fa'iza ba, abun mamaki sai Amir shima ya Tsaya cak kamar ubansa. Ji sukayi cikin tattausan murya ya Cigaba da fadin"Ni daman bana so nayi miki Dole wajen aurena. Tunda kika zabi komawa gidan mijin ki i will Support
Chapter 42 · 0% Book details