← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 71

Sashe 13

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

min komai ba, Fa'iza ma ban ji tayi mgana shiyasa sai na dauka tsiyar ki ne ya tashi kika dauke kafa." Baba Ati tace"Ko ba domin Darajan Fa'iza ba,ai ya Duba zumunci" Yaya Mariya tayi mirmishi kafin tace"Ke kika san wannan Baba Ati, tunda Fa'iza ta zama banza a wajen su zaki san ba su damu da wannan zumuncin ba" Kai Tsaye Abba yace"Ki fara sanar dani abunda kika sani" Ina kuka ina girgizama Yaya Mariya kai bata Saurareni ba ta fara zayyana ma Abba abubuwan data sani akan zamana agidan Ishaq da yadda ya rabani da su da auran sa da wulakanci da Anty Binta tayi mana. da yadda na kara zama banza bayan auransa da Zainab Saboda ita mai kyau ce kuma yar gata ce,da yadda har mahaifiyarmu ta rasu bamu gana ba,kunci rayuwar da na cigaba da Fuakata kafin samun sana'ata da duk irin cin kashin da Mama da Anty Binta suke min ta fadi iya abunda ta sani kafin ta gama gabadaya su Inno sun fara kuka saboda Tausayina. Ammi tace"innalillahi lalle Fa'iza ta ga Kunci rayuwa" Abba ko Ishaq da Mama yake kallo ji yake kamar ya saka a kulle masa su har sai sun daina Numfashi,shuru falon ya Dauka sai mganganun su Baba Ati cikin Tausayawa ni ko kuka kawai nake yi cikin kunar rai abubuwan da suka faru suna Dawo min Daki Daki. A fusace Abba ya mike yana fadin"Ba anfanin wannan zaman. Ka rubuta ma y'ata takardan saki tunda ba'a Dole. kuma kwatankwancin yadda ka Wulakantamin Fa'iza wlh nima sai na wulakantaka" Kokarin Fito da wayarsa yake yi ganin haka nayi wuf na rike kafafun Abba ina kuka nace"Abba kada kayi mai komai don Allah nice daman baya so to ya sakar maka y'a Abba da gaskiyansa ni Nakashashiya ce ina da Raunin ji,sannan ni ba Fara bace bani da kyau Abba sannan ni bani da ilimin Boko kuma ban iya Turanci ba,sannan ni bani da gata bani da kowa ni ba yar kowa bace sai Diyar Bebiya,Abba da gaske ne ni nayi kutse cikin mafarkin sa ni ban Dace da Mutum irin sa ba,Abba ka Dubeni baka mara kyan Fuska wacce batajin Turanci bata kuma da gata Abba dole yaji kunyar nuna ma Duniya ni a matasayin matarsa in kuma yaji kunyar nuna ya'yansa shima bai yi Laifi ba ,Abba bai so a haife su ba Karfin Rabo ne ya samar da su na fi shi sanin zafinsu shiyasa na zauna Domin na kare su Abba. Abba ka kyalesa yana da gaskiyansa ni Fa'iza bani da wani amfani Abba ni ba macen data dace da namiji kamar Ishaq ba ne,ba ya so na ne Abba Kuma gaskiyan Mama data sha Fad'in bauta ya Dace da Mata irina. Abba na zauna na wahala da ya'yana Tunda ya zabi wata matar sama dani Abba sai mu kwana mu yini ni da yara bamu ci abinci ba Abba,Abba ba tun yau ba Mama da tab'a so ta koreni Anty Binta ta taba zuwa har gidana ta min watsi da kayana akan sai na bar gidan kaninta Abba..! Sai kuka yaci karfina na rika rusa kuka sai jikin kowa ya karayin sanyi Abba ya Duka ya rikeni jin hannayensa yasa na cigaba da Basu labarin irin zaman da nayi da ishaq irin yadda na fuskanci tozarci da wulakanci a wajensa da wajen mama yadda suke zuwa da Zainab ina musu wahala kamar jaka yadda yake tafiyar ya barmu da yunwa ni da ya'yansa,Yadda mahaifin matarsa da shi kanshi suka taru suka wulakantani Saboda bani da gata ni kaina ban san ina mgana ba Idanuwana a Runtse nake maida musu komai ina ganin shi a idona yana wucewa kamar a majigi. Ina basu labarin taimakon Hajiyar su Raliya gareni tare da taimakon Badariya da kudin da Kungiyarsu tabani kafin fara koyan san'ata da yadda muka yi da ishaq da zaman mu da shi bayan haka. Na Damke hannunwan Abba ina Fadin"Bani da abunda zai so Abba. Shiyasa na yi zaman ya'yana Lokacin da na yanke shawaran barinsa sai ya rasa aikinsa sai na janye kudirina Abba har zuwa wannan Lokacin" Kuka yaci karfina ammh ban yi shuru ba na cigaba da gaya musu yadda muka fara Sabuwar Rayuwa da duk abubuwan da suka Faru da Lokacin da ya nemi na bama aurammu wata Dama. D Da sauri Abba yace"Allah yasa baki bashi wannn damar ba Fa'iza..? Ina kuka nace"Na kasa Abba..Na kasa dalilin Ishaq yasa na Tsani aure da maza Gabadaya auren ya fita a raina. Don girma Allah Abba ka saka shi ya Sakeni ina jin kamar zam mutu in na Tuna da auren sa a kaina" Na karishe Fada ina wata jijjiga Saboda kuka Inno na sharan kwallah tace"Tabbas ya wajaba a raba wannan auran Usman zaluncin ya yi yawa" Abba yaji gabadaya bai son ganin Ishaq da mahaifiyarsa dake kuka shi ko Uban gayyar kansa na kasa jiki na rawa. Cikin Daga murya Abba yace"Sai ya saketa..?ai wannan auran ba shi..Duk da ban da zurfi a sanin wasu hukunce hukuncen addini,nasan matsayin ka jingine auran ka a musuluci wata Hudu ne in baka Waiwiyo ba, ta nemi manya su Raba auran ita ko ta haura shekaru mganar ma yayi saki ko kar ya yi ya Rage nasa mgana D'ayace daga ita na gama Bilhil azim ko kusa da Y'ata Ya sake kusantowa sai na saka an Dauremin shi" Ya fad'a cikin bacin rai yana kokarin mikewa da Sauri Mallam yace"AlhaJi don Allah ka koma ka zauna ina da karin bayani kan wannan al'amarin" Girman Mallam yasa Abba ya koma ya zauna ina jikinsa ina kuka Yaya Mariya ma sai sharan kwallah. Kowa ka gani jikin ya yi sanyi Ishaq ko bakinsa ya yi nauyi ya kasa ma mgana. Mallam ya gyara zama yana fadin"Matsalace ta Ila'i wannan mganar ma'ana rantsuwa a shari'a,kamar kace kayi ramtsuwa ka iyakan cewa bazaka kara kusantar matarka ba har na tsawon Lokacin da ka Dib'a ma kanka. A shari'ance Wata Hudu ya bama mace dama ta zauna in bai Sauya ra'ayi ya Dawo ba ta saka manya Cikin mganar, ko ta kai kara Alkali ya raba auran,ita kuma Fa'iza ta Shafe wasu shekaru tana jingine bi masala ta addini auran su bai saku ba, sai in har shi da kansa mijin ya Saketa ko kuma ya bayyana mana matsayin jinginarsa gareta na saki ne ko ba na saki ba ne. Ammh Shari'a ta bata damar ta Nemi Saki in har bazata iya zama da shi ba" A fusace Abba ya ce"Ai ko yanzu zai sakarmin y'a don mai garin su.." Kai Tsaye ya maida kallonsa kan ishaq kafin yace"Zaka sakar min y'a ko sai na gwada ma ka nima d'an tasha ne? Abba ya fad'a yana Zare mai ido Lokaci daya kamar D'an tashan daya ambata.
Chapter 13 · 0% Book details