Sashe 65
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tafiyar Engr Edo ta dauke sa kimanin Sati uku da wasu kwanaki ne sannan ya dawo. lokacin su Hafsatu sun gama min Hutun su. Sati uku suka yi min sannan suka koma saboda an koma makaranta har ga Allah naji dadin Hutun su a wajena tun ballatana ga su Kafayatu da suka saba da su watarana duk gidana ma suke kwana, A taru ayi ta Hira ana dariya Su hafsa na son koyon yarbanci su kuma suna son iya Hausa sosai Diramansu ma abun dariya ne. Engr kudi ya turomin masu yawa tun yana chan muka je nayi musu shooping kamar yadda yace haka ma Papa ya bada kudad'e yace aje kasuwa su dauki duk abunda suke so. Maa ma ba'a barta a baya ba. dukkansu kowacce da akwatinta shake da Sabbin kaya da kayan amfani sai wanda ya gani. Sannan Direba ya kai su har gida sannan ya juyo Abba da Ammi sun kira suna ta fad'an Hidima tayi yawa nace ba ruwana Aikin Engr ne tunda nace haka sai na kashe bakin su. Sanda ya dawo na fad'amai abunda su Abba suka ce dariya kawai ya yi kafin yace"kyaleni da Rigimammen baban nan naki. ya kirani zai fara mganarsa nace ni sisters d'ina nayi ma alheri ko Haramin ne..? Ai daganan bai kara mgana ba nasan mganinsa" Tsungulinsa nayi ina fadin"Uban nawa..?sai da ya yi wata dariya kafin yace"Nima ai Ubana ne. Tunda ya bani ke ammh wani lokacin ki kauda idanuwan ki bayan Uba shi abokin aikina ne" Dariya kawai nayi ban ce masa komai ba tunda nasan gaskiya ya fada tare na gansu kuma ban isa nasan Tsakanin su ba. Sati Daya ya yi min ya koma,yaso ma mu koma tare zuwan Hajiya Kudirat Abuja yasa ya barni. bamu tafi tare ba yace sai in dan ya dawo. Shiyasa gudun zaman shuru na kan je gidan su Papa na yini watarana har kwana ma ina yi Hajiya Kudirat ne ta tsawatarmin akan na rika zama agidan mijina yau da gobe sai naga na Saba,jin haka yasa sai Papa yace su Kafayatu su bini in Oluwatosin ya dawo sai su dawo gida hakan sai ya ragemin zaman kadaici tunda muna tare da su basa dai yini a gida ne suna makaranta sai weekend wani Lokacin ma Ranar Lahadi ne kadai suke gida. ammh tunda muna kwana tare a kallah dai nasan akwai mutane a kusa dani,kuma a baya nasan na yi zaman kadaici ammh lokacin akwai yara suna Debemin kewa yanzu ko bayan kewar mijina har da ta yara ina yi kuma ko da yaushe cikin Tambayar Zainab nake yi yaushe zasu samu hutu Saboda ina so suzo su yi min Hutun su awajena. A na cikin haka sai ga wayar Badariya daman na jima bana samunta a waya tun sanda muka dawo in na kirata wayarta a kashe nayi ta Damuwa har sai da na fad'ama Engr sai yace mu mata mun cika raggon azanci meyasan bantaba karban lambar mijinta ba..?Da sai na kirasa naji ko lafiya sai da ya fad'a naga gaskiyansa kuma ban taba wannan tunanin ba shiyasa akace mu mata karkatattu ne duk ta inda aka gyaro mu sai mun sake karkacewa. Lokacin da naga kiranta da Zumudi'na na amsa kiran sai dai yanayin da na jita ya fad'armin da gaba cikin damuwa bata budemin komai ba kawai tambayata tayi ina ina..?Nace mata ina Abuja sai ta nemi da in turo mata address din ta manta Dakyar ta iya kawo kanta. Ban rike anguwan da kwatancen ba Sharifatu na bama ta rubuta mata duk sai jikina ya yi sanyi da na kara tambayan ta meke faruwa muryanta a matukar Shake tace min"Zamu yi mgana Anty Fa'iza in da na zo" Sai na kyaleta har tazo din,har ga Allah na zata ba ta saka ranar Tafiyar ba,ban dauka da wuri haka ba sai dai a daran da misalin Tara na Dare sai ga Badariya cikin wani yanayi mara Dadin ji da gani tazo a galabaice saboda Tafiyar mota tana ta faman amai ga jikinta da zazzabi. Na rude sosai da ganin yanayinta Fadi nake yi"Badariya lafiya..? Ko wani abu ne ya samu Yusuf din..? Duk bata bani amsa ba tana cikin wani yanayi,tsabar na rude ma na rasa taimakon da zan bata sai su kafaya ne sukace bari su kira Family Doctor din su yazo ya dubata jin haka yasa na samu Tunanin kaita Dakina na taimaka mata tayi wanka,sai rawan Sanyi take yi hakoranta na Haduwa waje daya ga shi ta rame ammh naga ta kara fari kumatunta sun cika sosai. Suna ko kiransa ba jimawa sai ga shi yazo ya dubata sai ya Dibi jininta yace da safe zai kawo Result bai bata mgani ba allura kadai ya yi mata Sai Drip da ya saka mata ta samu barci,haka na ta sata ina kallonta Lokaci daya na zabga tagumi. Engr ranar yasan ba na cikin sukuni Tunda ka'idan kafin na kwanta nakan kirasa,mu yi bamkwana yaga ban kirasa ba kuma ya kirani ban dauka ba Allah nagani ban ma ji kiran ba wayar na inda na idar da sallar Isha'i. Sai ya kira Sharifa itace ta fad'amai nayi bakuwa tazo ba lafiya. Sai yace ta kawomin wayar ta wayarta ne muka yi mgana na fadamasa Badariya ce ga kuma Halin da tazomin cikin damuwa. Sai ya shiga lallashina da irin tausasan kalamansa. Hankalina tashe nace"Abunda ke damuna ina mijinta yake da ya barta ta yi doguwar tafiya ita Kad'ai? Engr yace"Allah masani kuma ga shi ba lambar shi mijin ballatana akira aji ko lafiya" Kai tsaye nace"Sai dai in wayarta.Gata nan a hannuna" Engr ya yi shuru kafin yace"ko kuma ki bari ta farka sai ki fara jin ta bakinta kada mu yi gaggawa" Da haka ya samu ya lallasheni da zamu yi sallama yace"Kada ki damu zata farka cikin lafiya. In kika saka damuwa ina kike so ni kuma na saka kaina Babyna..? Sai ya bani dariya daman Burinsa kenan yaga Dariyata,Kuma daman yasan in yace Bby sai nayi dariya don in yace min haka sai nace"Wata Bby da ya'ya zarata har hudu..? Bby kamar wata Anum.? Shiyasa in ya tashi zolayansa haka yake kirana tun ina jin wani iri har nazo na saba. Shawaransa na bi ban kira kowa ba,To in ma zan kira bani da zabi Tunda wayar tana cikin Password ne Dole sai in ta farka tukunnah. Ba ta kuma tashi ba sai da asuba,Cikin ikon Allah ta tashi da kwarin jiki Daki daya muka kwana na bar mata Kan gado ni na kwana saman Cafet. Ba tare da taimakona ba tayi wanka ta Dauro alwala ta fara rama salolinta ni kuma na fita zuwa kitchen tunda na saba bana barcin Safe,Wani lokacin tare da su kafaya muke abun kari wani Lokacin sai dai su fito su ga nayi musu komai. Yau ma hakan ce ta kasance,Indomie na Dafa sai na dafa musu kwai ni kuma daman na fi son sayayye sai na soya na Dafa Ruwan tea mai kayan kamshi,Na kuma soya Buredi,ina da Sauran Soyayyan Nama sai nayi musu pepe. Ko kafin takwas na safe na gama komai na goge kitchen din daman na fi yin abincin rana da yawa tunda ina aika ma su Maa da shi su yi ta saka albarka shi kan shi Engr bai sani ba sai dai in su Maa din suka fad'amasa domin ya yi min mgana ba Dawaniya ba ce..? Nace masa ba Dawainiya bace,daga karshe sai yace Allah ya ba da Lada. Koda na koma Daki Badariya na kwance ammh ba barci take yi ba,gaisawa muka yi na tambayeta jiki cikin sakewar murya tace min taji sauki.. Gefen gadon na zauna ina fadin"Kin kira yusuf kin fadamai halin da kike ciki..?wai ma tsaya da sanin sa kika yo wannan Doguwar tafiyar..?kuma baki fad'amin jiya zaki kamo hanya ba" Shuru tayi kafin ta yamutsa fuska tace"Bai sani ba" Kai tsaye na kalleta da tambayan"Bai sani ba..? Bangane ba..? Sai ta koma ta lumshe ido kafin tace"Miye baki gane ba..? Nace miki bai san na taho ba,bama shi ba ba wanda ya sani" Ban yi mamaki ba ganin yanayin yadda ta zo sai na muskuta kafin nace"To sai ki kira yanzu ki fad'a masa" Kai tsaye tace"A"a.." Mamaki ya isheni na mike ina fadin"To ni bani lambarsa na kirasa na fad'amasa kina wajena kada hankalinsa ya tashi in yaji bakya gida" Da sauri tace"Bazan baki ba Anty Fa'iza" Ina kallonta nace"Saboda menene..? Sai ta muskuta ta mike ta gyara zama kafin tace"Saboda bana so yasan inda nake. Na gaji Anty Fa'iza Ina so na rabu da auran Yusuf ko na huta da wannan bala'in da nike ciki" Ta karishe fada cikin gunjin kuka sai naji Tausayinta ya fad'amin. Na karisa gareta na zauna gefenta na rumgumota jikina ina Lallashinta Fadi take yi"Nagaji nagaji. Bala'in yau daban na gobe Dabam,ga na Matarsa ga na mahaifiyarsa ta tsaneni bata son ganina bata barina nayi girki ta karbe makullin Store sai taga dama zan ci abinci,matarsa kuma har gidan take zuwa tamin Tijara,ban ce komai ba shi ma kamar ta shanyesa baya iya Daukan mataki in nayi mgana sai yace nayi hakuri yana raga mata ne Saboda Hajiyar su, Wlh nagaji ne Anty Fa'iza gwara ya sakeni na koma gida yafiye min zaman auransa na rashin kwanciyar Hankali" Tana gama fad'amin haka ta fashe da kuka ma ban tausayi ga wanda ya Saurara ni kaina ta rauna na min zuciya ina tuna a baya nima fa na Fuskanci iri wannan rayuwar da Badariya take fuskata. Cikin Bubbuga bayanta nace"Subhanallah har yanzu matsalolin nan basu gyaru ba..? Shi Yusuf din bai dauki wani mataki ba..? Sannan yanzu me ya faru kika taho.? Badariya na gunjin kuka tace"Yaushe zai iya daukan wani mataki yana taorin matarsa yana tsoron uwarsa,Kwanaki fa har yaji nayi na tafi lagos na kafe bazan koma ba sai ya sauyamin gida da Hajiyarsa saboda bala'in ya yi yawa da yunwa nake kwana da nayi mgana sai tace Danta ya gaji da ci da juya nazo ba na Haihuwa sai ci nayi kashi abinci fa sai dai na siya,shi bazai iya mgana ba sai dai ya bani kudi a hannuna na rika cin abinci gajiya nayi sai nayi tafiyata Tunda bata amince