Sashe 34
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
muryata na da dadi...?muryan da Yaya ishq yace yana jin haushi ina mgana ina rabeta kamar yar koyo. Sai idanuwana suka ciko kwallah kaina na kasa nace"Ni ba ajinka ba ce kafi karfina bani da dukkan abunda mata masu kyau da wayewa suke da shi..ni bazawara ce" "Ya'yan ki kuma hud'u ko..? Yafad'a da sauri bayan katseni cikin mamaki na kallesa shi kuma cikin kwarin gwiwa yace"Nasan ke bazawara ce na kuma san muna da ya'ya yaushe kika shirya kaini na gan su? ko kuma ki bani lambobin su New papa din su zai kira su ya gaishe su" Sai na kasa mgana kiris ya rage in yi kuka kai tsaye yace"Sai kuma me ma kika ce..? Yauwa ke ba ajina ba ce sannan baki da abunda da mata masu kyau da wayewa suke da shi ko..? Yafada cikin sigar tambaya sai na kasa bashi amsa yanayin Fuskarsa sai ta sauya cikin Sautin maza jarumai yace"Kafin na baki amsar ki meyasa kika yi min wannan mganar..? A ransa yana tunanin meyasa suke da wannan tunanin Baban Nana ma ya fad'a masa Ni ko kaina na kasa nace"Saboda mazan wannan mazanin basa auran mace in bata da abubuwan kamar kyau,nasaba,gata,karatun boko wayewa,in kuma suka samu akasin haka sai kuke ganin kamar ba ku auri macen da ta dace da su ba kuma haka naga kuna yi shiyasa" Katsaneni ya yi da fadin"Kika ga suna yi dai Fa'azza..! Ni ba haka nake ba ni Abdulbasit kyan mace bai taba Damuna ba" Wlh tallahi billahil azim in kyau nake nema ba a Nageria zan yi aure ba akwai kasashen larabawa,ina ne bamu shiga ba wasu matane bamu gani ba..? Ammh ba wacce ta kwantamin arai sai ke Faa'iza ina sonki da zuciya d'aya ba domin wani abu naki ba ke din kawai nake so.." Yafad'a yana bina da wani kallo kaina na kasa sai hawaye cikin Tagumi yace"Ya illahi ni Tosin saboda rashin so na har da kuka Faa'izaa..? Sunan da ya fad'a yasa bansan sanda na kwashe da Dariya ba ina Tare bakina kallona yayi yana mirmishi kafin ya cire tagumin yana Fadin"Eh Alowatosin Yoruba name dina ne shine a gida su papa ke kirana Tosin in ba a bangaran aiki ba, achan Benue Da tosin suka sanni ammh yanzu a gabanki Abdulbasit ne" Ina dariya nace"Ko dai Tosin..? Sai kawai ya sake tagumi yana kallon bakina kafin yace"Tosin din FAA'IZAA ammh" Dariya ta shakeni na fara tari da sauri ya mike ya isa frige din Abba ya Daukomin ruwa jiki na rawa ya budemin ya mikamin na karba na sha kadan na mika masa ya karba yana min Sannu sai da yaga tarin ya Tsaya sannan yace"Oh ni Tosin zan ma kaina Tsiya tun kafin na gama na kafa gwamnatina.." Dariya naji ta kara kamani sai da ya sauke ruwan hannunsa sannan ya zauna yana fadin"Ni dai ki bar Dariyan nan ki fara ji da Tosin bawan Allah" Ya fad'a kamar ya yi kuka ni yanayin yadda yake fadin Tosin din ne yasa Naji na kasa daina Dariya ai sai ya Hade rai yana Fadin"Kin san Allah? kika kara shakewa ko ruwa bazan miko miki ba" Sai na natsu ina Sadda kai na kasa mgana sai dai ina ta mirmishi leken Fuskata yake yi yana Fadin"Cute" Nasan ma'anar cute da Sauri nace"Nasan zagina ka yi" Ido ya waro kafin yace"Ni tosin yaushe..? Kai tsaye nace"kace cute ni nasan ba Cute ba ce..Nasan ni mummuna ce sannan ana yawan fad'amin ni mummuna ne" Rai ya hade kafin yace"su waye..? Gaskiya ba gaskiya suke fad'a ba..To ni dai koma menene haka naji kuma nagani" Kai tsaye nace"Baka ce ni. ga shi ban da ilimin boko ban iya turanci ba" Shima kai tsayen yace"Ni bakin ki ya yi min daidai ma,nima baki ga bakin ba ne, mu taru mu ta haihuwan ya'ya dunaye balakai." Hausarsa ta saka dariya ta kamani bai damu ba ya cigaba da fadin"Mganar Turanci kuma ina ruwan Tosin. Ni ai ba da Turanci muke mgana ba sannan ni kaina in fad'a miki gaskiya ba Turancin nakeji ba, duk barazana ce wlh asaran kudin tara Papa ya yi gabadaya kaina nan a Duhu yake" Yafad'a yana Buga kansa Dariyata har tana fitowa cikin dariyan nace"To ya akayi ka samu aiki..? Kai tsaye yana mirmishi yace"To wannan kuma su Papa ne suka shiga suka fita ammh ban chanchanta ba" Fuskarsa fa ba wasa ya cigaba da fadin"kinga kenan dukkan mu bamu iya ba an had'u da an dace kenan" Ina Rufe bakina nace"Kuma ka zama megidan Abba..? Da Sauri yace"ai na fada miki Papa ne ammh ina Tosin ina zaman Ogan Abban ki..? Dariya ya yi shikan shi da mganarsa nasan yana yi ne saboda na amince masa ni ko dan barkwancinsa yasa na saki jikina da shi ban sani ba. Dariya ya rika bani ni ko nama manta inda nake har ina kyakyatawa. Ganin na shashantar da zencen yasa ya marairaice yana Fadin"Har yanzu dai Fa'iza bata ce tana Tosin ba..? Fuskata na rufe kafin nace"Sai na fad'ama Abba" Kai tsaye yace"Da izininsa ma na neni ganinki. Ba ruwan Abba a wannan mganar domin ya fadamin na nemi yarda a wajen ki tunda shari'a ta baki damar zaban miji a karo na biyu. Faa'iza ni ma ba kowa ba ne mahaifina ma'aikacin gwammati ne nima haka muna zaune a garin Abuja tare da mahaifiyata da Sisters d'ina guda Biyu,sai granny kakarmu wacce ta haifi Papa,Shekaru takwas da suka wuce na taba aure sunan matata Tauhidat satin mu hudu da aure wutar gas ya kona ta Allah ya yimata rasuwa ,tun daga Lokacin ban kara mganar aure ba sai yau a kuma kan ki Faa'iza shiyasa na fada miki ni ba yaro ba ne kalleni nan bazawari ne ni ki bani dama bana son na bata Lokaci mu wuce wajen ina sonki nasan Sauran Fahintar junan zamu yi shi idan muka zama mata da miji" Karfin Halinsa ke bani mamaki in yana mganar aure farawa da iyawa alokacin sam na manta da wani Ishaq,sai kawai nace masa zan yi Tunani kara marairaicewa yayi yana Fadin"Tunanin minti daya Faa'iza..? Ina zaro ido nace"Aa nan da wata biyu" Sai kawai ya gyara zama yana Fadin"Abba zai bani Masauki ko..? Nayi dariya kafin nace"Da gaske nake yi" Shima kai tsaye yace"Baki isa ba fa. Sai kuma chan yace Allaha sarki Tosin bawan Allah Fa'iza ki Tausayama Abdulbasit mana kin gani kano zani. ammh saboda ke na fasa sanda kika yi tunanin kika fad'amin Abdulbasit na amince ka zama miji na sai na tafi inda zani" Ganin yadda ya zauna yasa nasan ba wasa a mganarsa da sauri nace"Kayi hakuri ka tafi bazai d'au Lokaci ba. Shuru yayi kafin yace"To kwana daya Faa'izaa." Zan yi mgana ya tareni da kallonsa Dskyar nace"Sati daya dai don Allah" Kamar yana jira yace"Aa kwana Biyu Faa'iza bazan iya jiran Sati ba zaki kashe Tosin da Tunani fa" Kina so in na mutu ki biya Diyya ne..? Da Sauri na girgiza kai sai yayi Mirmishi kafin ya zaro wayarsa a Aljihu yana fadamin"Sakamin lamabarki anan Faa'iza" Yanayin mganarsa yasa ban yi masa musu ba na karba na saka masa ya amsa ya kira da bai ji ringing din ba da Sauri nace"Tana Daki" Sai ya gyada kai kafin yace"Ki rika barinta kusa dake. bana so na kiraki ban ji ki ba" Ina kallomsa kafin nayi mgana yace"Abba ya fad'amin an haifeki da Hearing problem ni kuma nace Daidai kenan daman ai ni kadai ya Dace ki rika jin muryata sosai ko..? Sai ya bani dariya na Lura in muka kai wani Lokaci cikina zai kulle. Wayar mikamin yana cemin na sakamai lambar ya'yan shi. Cikin mamaki nace masa"Basu fa da waya. Yara ne babba ne Amir(Kabir)16yr yana Ss1 sai mai bi masa 14 Anum(Saudatu)tana Jss3 sai Mustapah dake jSs1 Ahmad ne karamin su yana primary 5 ne"cikin gansuwa yace"Masha Allah suna ina yanzu..? Kai tsaye nace"Suna wajen Baban su a lagos" Kai tsaye yace"Ana Daura mana aure zamu karbo su damu zasu zauna in sha Allahu"mamakinsa ya kamani kawai sai nace"In babansu ya baka ba..? Yana kallon cikin idona yace"Zai bani mana nima ai ya'ya na ne" Kamar wacce ta samu abunda ta jima tana nema haka na saki jiki da Engr muna Hira,na manta da kowa da komai sai da Nana khadija ta kawo abun kari naganta da shirin makaranta sannan na Duba agogo tara saura nayi salati ina sallalami shi kuma yana Dariya fadi yake"Kinsan Tosin akawai hira Abdulbasit ma ba baya ba" Ina Dariya na fice ina ji yana kiran sunana naki dawowa dakina na koma na kwanta kan gado ina mirmishi ni kadai kamar wacce tayi gamo ina ji Ammi tana kirana nayi saurin Shigewa Tiolet na tube na fara wanka saboda Kamar zai tafi ne,aka kirani ai ko sai da yabar gidan na fito,nako ga tarin missedcall a wayata har da bakuwar lamba kuma nasan shi ne sai da naga na Zainab kusan guda biyar na Tuna da wayar mu ta dazu sai gabana ya amsa gabadaya jikina ya wani mutu kamar bani da Lakka. Ga Engr ya yi min bake bake a zucci da baki,ko tunasa nayi sai nayi Dariya sai naji mirmishi ya kamani sannan ta wani bangaran ga mganar da na Fad'ama yara na.? Gefen gado na koma na zauna ina jin Hajijiya ni Fa'iza ya zan yi..? Engr ko Ishaq..? Ko da ban ga Abba ba nasan bazai ki ba. sanin Darajan da Engr ke da shi a wajensa, Ammi daman sai tafi kowa murna ammh Ishaq fa..?ba shi kan shi ba, saboda yara na.." Tabbas ina cikin Tsaka mai wuya.