← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 71

Sashe 39

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da Engr ya gama kassara Sauran kuzarinsa kaunar da Engr ke yi ma Fa'iza daga Allah ne, Ubangijine ya hada wannan soyayyar ba ta mutum ba ce. Ya tuna kalamansa dazu da ya kirasa kan bata amsa wayarsa fad'i yake yi"Baban Nana ina son Fa'iza ina jin ta a raina yadda ban taba jin wata y'a mace ba, ka fad'amata tayi hakuri in Laifi nayi mata ta bari in nazo sai ta Hukuntani ammh ta yi ma Girman Allah kada ta hanani jin muryanta" A yanayin yadda yake mganar zaka Fahimcin yanayin da yake ciki sannan zaka san mganar daga karkashin zuciyarsa suke fitowa. Ammi kuwa mgana ma kasawa tayi baki ta bude kafin tace"Bangane ba..? Baban Nana meke faruwa ne..? Ta fada tana kallon Abba na neman karin bayani. Shi ko Abba ni ya ke kallo na wani Lokaci kafin yace"Kin tabbata..? Bana so ki yanke hukunci cikin gaggawa kina da Sauran Lokaci" Kai Tsaye nace"Ban yi gaggawa ba Abba. Na yanke shawaran zan koma gidan Yaya ishaq" Na fada ina kokarin danne yanayina ammh fa hawaye bai bar idanuwana ba. Ammi fadi take yi"Ke baki da Hankali ne..?Engr din fa..? Ina Abba bai bi ta kanta ba zama ya gyara yana fadin"To Alhamdulillah. Allah yasa hakan shine mafi alheri zan yi mgana da Engr zan basa hakuri goben zaki tafi karofin.?. Ina kokarin Dauke hawayena na daga mai kai sai yace"Allah ya kaimu lafiya tashi kije kin ji ko..?Allah na tare da ke Fa'iza" Jikina na rawa na mike na fice ina Kare Fuskata Saboda kukan daya tasomin,haka na koma Daki na kulle kaina ina ta kuka wayata ma kasheta nayi gabadaya.. Sai bayan fitar Fa'iza Abba ya yi ma Ammi bayani ashar ta zuba kafin tace"Wlh wannan mugunta ce ya za'ayi bai yi mgana da Fa'iza ba sai ya kama yad'a mgana haka ake yi baban Nana..?Saboda yasan Fa'iza kan ya'yanta shiyasa yayi mata haka Engr fa ya zaka yi da shi..? Abba ya lumshe ido kafin ya bude yace"Muna namu ne Allah na nashi kuma na Allah shine Daidai. Komawarta gidan Ishaq ba laifi ba ne Aziza,Duk kyan Sabon gini gwara Tsohon yabe" Ammi ta karkace kai kafin tace"Wlh da Tsohon yaben nan na Ishaq gwara Sabon gini irin na Engr ko baka lura itama Fa'izan na son shi ba..?Fin karfi yayi mata kuma kana gani kai bazaka yi mgana ba" Abba ya girgiza kai kafin yace"Ai zabi na bata kuma ta zaba ni bani da wani abu zan yi mata. Ba Hurumina ba ne" Ammi ranta ya baci tace"Sai kayi shuru yarinya ta cutu Baban Nana..? Wannan ba zalunci ba ne" Abba yace"Komama Uban ya'yan nata ne Zalunci..? Ammi ta mike ranta ya gana baci kafin tace"Eh Saboda bai dace da Fa'iza ba" Fuu kamar iska haka ta bar masa Falon kai tsaye shashen Inno ta wuce su Hafsah na wajenta idanuwanta sun rufe ta shiga karanta ma Inno Abunda ke faruwa sai Inno tayi shuru kafin tace"Kin san shi aure rai garesa Azizatu..Gwara da Usman bai saka baki ba,in har Fa'iza ta amince da komawa gidan Uban ya'yanta shikenan Aziza abu ne mai kyau hakan suna da ya'ya a tsakani,sannan ga zumunci kuma ko Allah ma muna masa laifi ya yafe mana ballatana mu d'an adam..?mganar wannan bawan Allah kuma ai ba nisa yayi ba sai Usman ya bashi Hakuri haka Allah ya tsara kuma mu bamu isa muja da hukuncinsa ba" Sai bakin Ammi ya mutu ganin Inno ma bata goyo bayanta ba ammh tasan wannan komen na zalunci ne,Sai ta yi fushi da Abba ta shige dakinta tana kunci tasan da Baffa na da rai shi kadai ne zai gayama Abba yaji,Ga tafiyar Fa'iza ga abunda ya faru ko siyayyan komai ma bata samu yi ma Fa'izan ba. sai da Safe da ta shigo gaisheta ta bata kudin da Abba yace ta bata ita kuma ta hada mata kayan kwaliya da atamfa da less da Hijabai wadanda bata dinka ba. In ta tuna Fa'iza zata rasa mutun kamar Engr sai taji ma Fa'iza takaici har sai da ta mata mgana da cewa"Ke yanzu gidan wanda baisan Darajan ki ba zaki koma Fa'iza..?kada fa ki yi gaggawa kizo ki yi da kin sani" Sai na fashe mata da kuka shiyasa ta kyaleni tare da Nana khadija da Hafsatu zamu tafi zasu weekend achan Abba na gida bai fita da wuri ba Direban sa zai kai mu har karofi. Naje yi ma Inno Sallama ta rika yimin nasihan hakuri da rayuwa Daga karshe tace"Ki yi hakuri ki kuma barma Allah, Zabin nan da kika yi in sha Allahu Hairan ne" Mganganunta suka d'an sanyayamin rai ammh muna mota na makure kaina a gefe ina kuka Hafsah na gaba Nana khadija na baya sai na sanya Nikab ina ta kuka na ba wanda ya sani wayata ko tana kashe ban kunna ba na so ma Enge ya same ni. Nayi niyyar zuwa nayi ma Raliya sallama,ammh bana cikin yanayi mai Dadi shiyasa ma na sha'afa kwana nayi kuka saboda haka da ciwon kai na tashi da shi kuma na isa Karofi. Muna mota amai na dinga yi ni da bana amai a mota ammh Ranar nayi duk na bata jikina,Lagai lagai muka isa gidan Goggo sai ga shi nice kwance da Daddare har da karin ruwa Ulcer ta tashi sai jini da yayi sama Abba nata Fad'an nasan ban ji dadi na shirya Tafiya, ita kuma Ammi ta ce Wlh bana son komawa gidan baban su Amir ne, in aka kyaaleni zan cutar da kaina. Abba kuma yaki biye ma mganarta Domin ya kira Engr tun a daran jiya ya ba shi hakuri tare da yi mishi bayanin Halin da ake ciki ya yi shuru na wani Lokaci kafin yace"Ita Faa'izan ta ce ta zabi komawa gidan Uban ya'yanta..? Abba kunya da nauyi dakyar ya amsa masa sai yayi mirmishi kafin yace"Shikenan hakan nada kyau. Allah yasa hakan shine mafi alheri na so ni na sameta domin na cike mata wani gurbin da ta rasa, ammh ko a yanzu bazan cire rai ba sannan bazan mata bakinciki ba,ina yi mata fatan alheri Allah ya sa tayi farinciki fiye da in ni ta aura." Sai Abba yaji ya kara jin girma da wani Darajan Engr ya karu acikin Idanuwansa,abun mamaki kuma sai suka cigaba da mganar aikin su ko alama bai nuna masa wani Damuwa ba duk da yasan tabbas akwai damuwan. Shi kan shi abun ya kamasa ammh kuma Fa'iza yake so ta yi ma kanta da Rayuwarta zabi shiyasa bai shiga mganar ba kuma a ranar da Fa'iza ta koma karofi ya kira Ishaq yace sati mai zuwa za'a maida auran sa da Fa'iza ranar asabar kenan in an yi walima jumma'a asabar daurin aure. Ishaq farinciki kamar an yi masa Bushara da gidan aljannah,Haka ya Dawo gida yana fad'ama Mama ta washe baki tana fadin"Masha Allah. Allah ya sa albarka" Zainab ma tun tana wajen aiki ya kirata ya fad'amata itama tana ta Murna yaran na Gidan Anty Fadila yaje ya Daukosu a daran Sukaje shan I.cream da kayan kwalama saboda Murnan dawowar Fa'iza hatta Amir ranar an ga walwalansa ya shige cikin kannensa yana ta wasa da su. Akwai wani Farinciki da annushuwa a fuskokin yaran. Ishaq har kati na waya ya saka an buga masa gayya yake so ya yi sosai,ita kanta Zainab tace zasu yi walima in Fa'iza ta iso Lagos. Abba shi da kanshi ya kira Mallam mijin goggo ya fad'amasa ranar maida auran, shi kuma ya fad'ama Goggo ina kwance tunda na dawo ina fama da kaina da zuciyata wayata ko ban kunnata ba har a lokacin tana kashe ne ga,shi tunda aka san na dawo ana ta kawo ayyuka ai bani ma da wani guzari su jummala ke yi kunin aya da zobo daman Goggo ke yi yanzu. A bakin Yaya Mariya nake jin ranar asabar za'a maida aurena da Ishaq ranar sai a asibiti na kwana,Haki na farayi sama sama numfashi na sama sai kuka,kuma na kasa fitowa nayi mgana Abba kuma yayi bakam domin shima ya yi katin daurin aure, ya gayyaci abokan aikinsa. Labari ya kai ma Ishaq bani da lafiya shima Yaya isa ya fad'amai kwana na Biyu a asibiti aka sallamoni da gargadin na rika cin abinci sannan na daina yawan Tunani to ai tunani a wajena ya zama Dole. Sai dai sun ta kirana wayata a kashe shi da Zainab,Badariya ma tana son mgana dani ammh na Toshe duk wata hanya,sun yi sun yi su ji Tsarina na Biki naki mgana sai shirin walimarmu kawai nake yi dubu ashirin ashirin muka bada sai Hijaban da muka dinka iri Daya. sai ni a gida zamu yi abincin Sadaka,Sai kuma na baki Tunda Abba da Ammi da Inno suna tafe ga su Hafsah suna nan basu koma ba. Nana Fatima ma mun yi mgana ta wayar Goggo tace ranar jumma'a zata zo da safe tun da walimar sai la'asar ne, bana yarda ayi min mganan Daurin aure yanzu sai na saka kuka duk wannan Dauriyar da nake yi Engr na makale a raina bai fita ba kowani Bugawar Numfashina tare da shi acikinta ammh Farincikina ya'yana ne ya yi min katanga da shi har Abada. Tun ranar alhamis Abba da Ammi da Inno sai Raliya da walid suka Dira a Korafi daman na fad'ama Hajiya zencen walimar ammh ban gayamata na Daurin auren ba sai Raliya ne ta gayamata sannan na kira sa'adatu da Habiba na gayamusu sun kuma min alkwarin suma zasu zo min in sha Allahu. Su Ammi a gidan da Abba ya gina suka sauka,tunda Daman Baba Ati na cikin gida ita da ya'yan makota ta kama ta rike,ranar jumm'a da Safe sai ga Badariya abun bai wani bani mamaki ba nasan abunda ya kawota ko murnan ganinta ban yi ba, itama ta ga hakan don da tace min tayi ta kiran wayata a kashe yake kawai nayi mata sai kuma ta kalleni tana fadin"Amaryan tamu ba kunshi ba gyaran kai ba na jiki..?me kike nufi..? Ko amsa ta ma ban yi ba a raina sai da na Zageta in da ace yau Engr zan aura da sai nayi masa abun yafi haka ma sanin shi zai aureni ne ba
Chapter 39 · 0% Book details