← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 71

Sashe 3

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*Janafty*
*24/07/2023*

*KNKB3002*

Kimanin kwanaki takwas kenan da sallamoni daga asibiti bayan na shafe kwana bakwai sati d'aya kenan karkashin kulaawar likitoci.
Na dawo gida da Tud'in mganguna tare da Dokokin likita kan na kiyaye shiga Damuwa da tsananta ma kaina Dogon Tunani,duk jinsu kawai nake yi ana iya raba bawa da Tunani ne..?ballata ni da tunani ya zame min dole ba ma sai na gayyace shi ba.
Tun ina asibiti ina amsa wayoyin yan'uwa masu min sannu sama sama,da kuma muka dawo gida na karajin sauki Tiryan tiryan nake mgana da mutane,sai dai kamar yadda Abba yayi gargad'i ba wanda ya karamin mganar Ishaq dasu Amir duk da suna raina nima nayi kokarin yakice tunanin acikin raina,Kud'in da aka kashe a asibiti na Dawainiyata duk Abba ya dauki nauyin komai da komai bayan na koma gida kuma Goggo ta mike tsaye ta cigaba da kula dani kamar yadda ta saba itama kamar yadda Abba yace bata kara tada wata mganar ba.
Mun yi waya da Anty Fadila ta gaisheni bata min mganar komai ba nima ban mata ba,Haka zalika Badariya ma ta kirani tamin sannu itama a bakinta nake jin jamal sun gama Jarabawa zasu yi graduation dinsu sannan ya taho gida,to shima a daran ranar da ta fadamin haka ya kirani ya gaisheni da farko na zata ba su san ina Karofi ba sai da naji yana tambayata ya su Goggo? sannan nasan sun ji Labari ammh yadda basu nuna min komai ba nima ban nuna musu ba.
Abun mamaki hatta da Mama sai da ta kirani kuma ina da tabbacin shi gogan ya fad'a musu banda Lafiya ta,ni banganeta da farko ba saboda ban da lambarta,sai da tamin bayani sannan na gane bayan mun gaisa tamin sannu,sai naji tana ta kame kamen mgana ammh ta kasa fad:a sai kawai ta bige da fadin"Kiyi hakuri Fa'iza ki yi hakuri don Allah"
Toh kawai nace mata saboda na kashe mganar,Kuma muna mgana da mama yau gobe Ishaq ya dosa kirana a waya na ki dauka Saboda so nake na yanke alaqa da shi a yanzu tukunnah ko zam samu natsuwa inaga shine sai ya kira Abba ya fad'amai ya kirani ya gaisheni ban amsa ba,Damn kuma Abba a rana mukan yi waya sau uku sau hud'u shi da Ammi da sauran yan'uwana Hatta Hajiyar su raliya ta kirani ta gaisheni ita da sauran yayyin su Raliya tace a bakin Raliya taji bani da lafiya,Abba ne ya yi fadan meyasa ban Dauki wayar Ishaq ba..?
Sai na kasa mgana cikin Umarni Abba yace in ya kira na dauka mu gaisa Dalilin da yasa daya sake kira na Dauka muka gaisa kenan bazan taba iyama Abba gardama ba daman ba Halina ba ne.
Mun gaisa kamar bakin juna ya gaisheni na amsa a Tunkushe,kamar bana so,ina jinsa ya dade yana Auna mganganunsa kafin ya fara fadin"Fa"iza kin gani ko.?Dukkanmu bamu da natsuwa yaranmu ma basu da natsuwa basa tare dani suna wajen Fadila,ki dawo Fa'iza mu rumgumi ya'yan mu kamar yadda muka saba"
Ina jinsa yana kuma kai aya na katse kiran ina,jin wani takaici ya kara kumeni.
na kara tabbatarma kaina Ishaq bazai taba sona ba, zai yi kokarin maidani ne Saboda inganta gidansa da wani Muradinsa,Zainab ai mun yi mgana da ita ammh itama ban bata damar min wata mgana ba,Ranar ina tare da baki Yaya Asiya da yan gidan su Ammi Mota guda suka zo dubani sai nace mata ta bari zan kirata nayi baki Daganan kuma na manta ban nemeta ba.
Nana Fatima duk ta waya muke mgana da su ammh ta min alkawarin zata zo har karofi ta Dubani,ina Dakin Goggo bana aikin komai daga ci sai shan mgani sai kwanciya,na rame sosai duk nayi zuru zuru in na kwanta ban da tunanin su Amir ba abunda nake yi ina sharan kwallah Ko Goggo ta ganni ina kuka ci kanki bata cemin Ita da Yaya Mariya ke Dawainiya dani tunda koda yaushe tana gidan,haka ma su Anty Nasara Suma gidan suke yini da matan su Yaya isa wani Lokacin sai in Dare yayi ne,Mallam mijin Goggo ya tarkata kowacce zuwa gidan mijinta,Ni daman ina Daki daidai da Falon Goggo bana lekewa.
Na maida kaina wata Shuru shurun karfi da yaji lura da yanayina yasa suke kyaleni kawai da kuma dokar Abba.
Kabarin komawata Karofi ya shiga kunnen dangi da Dadama,har Hajiyar Dala ita kuma daman iyalan Anty Binta zasu fad'a mata tunda ga ma Halisa a kusa da su,bata zo ba sai dai ta kira Goggo ni ban ma sani ba sai da Yaya mariya ta shigo dubani Goggo na dakin tana bani mgani suke mganar naji ashe bayan ta kira Goggo sun gaisa sai ce mata tayi"Aisha yanzu da girmanki da komai zaki yarda yarinyar nan Fa'iza ta ce zata kashe auranta ta zauna a gidan ki..?
To in ta kashe auran uban wa zai rike mata ya'yan..?ya kamata fa kuyi Tunani shima dan'uwan mahaifiyar nasu naji ance mganar na hannunsa bai ce komai ba. gwara dai ku maida ta bata da inda yafi nan Ishaq ne Rufin asirinta,kuma ya rufa mata tun a baya bama yanzu ba"
Inajin sun manta ina Dakin ne sai da sukaji nace"In har Ishaq ne Rufin asirina, to na yarda na rabu da shi. In yaso sai asirina ya fallasu a duniya gabad'aya"
Na fad'a ina kokarin maida hawayen da suka cikomin ido ko don ganin Aurena da Ishaq alfarma ne ya zama Dole na nuna musu Allah ne kadai ya isa ya yi ma bayinsa alfarma ba Mutum ba,Goggo da yaya mariya suka kalli juna ganin haka ma yasa na tashi na shige Tiolet na rufe na fashe da kuka,Ina jin su Goggo na mgana a Cikin Dakin ban jin dai me suke fadi daga karshe suka fice sai da nayi kuka na ya isheni sannan na wanke fuskata na Fito ina kara ma kaina karfin gwiwa ba kaina Farau mutuwar aure ba, Sannan ba a kaina aka fara zama zawarci ba kuma ba kaina za'a kareta ba,sai dai nayi alkwarin zawarcina ba irin na kowa ba ne.
ban rabu da Ishaq Saboda na koma makaranta domin na samu Ilimin da yake min gori ba a'a na yanke rabuwa da shi ne,saboda baya sona sannan yana zama dani ne Saboda Kalaman Baba da kuma alfarma. tunda ya auri zabinsa sannan ya Jingine aurena da shi addini ya bani Damar iyayena ko shari'a ta shiga ciki ta raba auranmu.
Ranar kamar an yi min fami Yini nayi ina kuka,ni ko sai na nuna ma masu Tunanin Ishaq rufin asiri na ne da cewa ba shi ya Rufamin asiri ba. Allah ne sannan shi ke rufama bayinsa asirin su na Duniya har da na Lahira. naji kwata kwata ko ina da burin komawa Saboda ya'yana na cire wannan Tunanin ina da yakinin tunda ga Zainab ga Anty Fadila yarana baza su yi maraici a Lagos ba.

*****
Chapter 3 · 0% Book details