← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 71

Sashe 40

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

domin ya yi min alfarma ba sai domin yana sona. Baki duk sun hallara har da Yaya Asiya su Anty Binta dai ance suna katsina wai Mama sun zo ita da Ishaq da Yaran nima a bakin Yaya Asiya nake ji tunda tace tare suke da Halisa ta sauka katsina Hajiyar Dala ko cewa tayi nasan zan koma uban meyasa na matsa sai da aka kashe auran..? Bata zo ba kuma wani nata bai zo ba ,ni dai gidan su Yaya isa na koma da shirin walimata na tsani naji ana ambaton sunana da na Ishaq,sai dai na ji sanyi da akace da yaran yazo garin ko banza zan ga ya'yana naji dadi. Ko kafin karfe hudu an gama komai na walimar ni a gida ma na barsu mun isa makarantan tun biyu na rana,an shirya taro tunda dukkanmu iyayanmu zasu zo,su zasu shaida karban Shahadar. Sai bayan la'asar aka fara a babban masallacin makarantar za'ayi abun,dukkanmu mun sanya Hijabai Sea greeen har kasa da Safa da bakaken likabai ni kadai ce bazawara mai ya'yan sauran matan duk yan mata ne sai maza uku. Ahalina kaf sun zo,abun mamaki har da Anty Binta, Mama,Anty mahma,Halisa,Da Ishaq,sai Amir da nagani banga Sauran ba tunda mu muna chan gaba ne,Nima din waige nake yi,Nana Fatima tazo duka ita da ya'yanta sai Sa'adatu da Habiba Allah sarki tare da su Anty Nasara suka iso masallacin,Hajiyar Raliya ma tazo ita da yayar Raliya Salima,Yaya mariya da ya'yanta su Hafsah har da su jummala laure da makotan Goggo. Naji dadi matuka har sai da nayi hawaye Amir ina cikin nikab ammh sai da ya gane ni yazo wajena na Rumgumesa ina tambayansa sauran yan'uwansa yace"Suna gida Umma Tare da Anty" Cikin mamaki nace"Katsina suka zo" Kai tsaye yace"Lagos dai ai Daada yace tare zamu koma dake ko Umma..? Sai na kasa mgana illah kai da na Dagamai,an fara gabatar da walimar jawaban manyan baki da kuma mai makaranta sai na malamai sai kuma jawaban iyayen yara har Mallam mijin Goggi yayi jawabi Abba ya yi amatsayin Babban bako. Sannan Ya muhallin d'in mu an basa dama yayi jawabi na samu lambar yabo na Hazikar mace ta farko da shekaruna na Hankali na Haddace Qur'ani ya yi kira da sauran mata su koyi dani kada su duba shekaru su tashi su nemi ilimi,Sannan ya yi mganar Lalurata ammh yace hakan nan na Dage har na riga masu lafiyan Haddace Qur'ani,mu sani Allah baya maka hallita batare da yana da manufar hakan ba ina kallon su Abba suna ta mirmishi Allah Sarki tamadina da Baba nayi musu addu'an Aljannah da na tuna da su. An fara kiranmu d'aya bayan Daya Domin karban rantsuwa naga Fitan Abba ina ta Allah Allah ya Dawo kafin a kirani sai dai addu'ata bata amsu ba nice ta Biyu,tunda in zaka karbi shahadar sai da Hannayen iyayenka da yan'uwanka gabadaya. Sanda sunana ya karade lasifikan hankalina na baya ina leken Abba domin bazan amsa ba sai hannunsa na kan Hannuna. Kira sunana ake yi"Fa'iza Sidi karofi" Ammh ban ta shi ba sai da Yaya Mariya da su Nana Fatima suka zo suka tadani ina kamkame da Hannun Amir,Sai waige nake yi Yaya mariya tace"Wai wa kike nema ne..? Kai tsaye nace"Ina Abba..? Sai alokacin suma suka san baya masallaci Nana Fatima ta matsa gefe tace bari ta kirasa kuma ta kira bai Dauka ba ganin ana ta kirana yasa na tafi,ina zuwa akace ina Dangin Fa'iza Gabadaya sai su Goggo suka taso abun mamaki har da Ishaq su mama daman tare da su Goggo suka taso zuwa inda nake tsaye. Ni dai hankalina na wajen kofar shigowa,ina jin ana jawabai wlh ban Fahimci komai ba, gabana ke fad'uwa fat Fat! Mallam ya juya bai ga Abba ba cikin wani yanayi yace"Ina Alhaji ko fitan sa din nan bai dawo ba..? Ina shirin nayi mgana sai ga Abba ya shigo masallacin ina ganinsa sai naji sanyi araina ban tsaya ma kallon bayansa ba na juya ina kallon Ishaq dake ta bayana,taka hijabi na yake kamar zan fad'i sai na juyo sai ya kauda kai yana Dariya yayi fari ammh bai yi kiba ba,sai kasumba daya tara kamar wani kumurci. Ni ko harara na ballamai ta cikin nikab dina na sauya waje zuwa kusa da Goggo Amir kuma ya Biyo ni. Sai ji nayi Yaya Mariya na fadin"Abba ashe bako ya yi" Dago kaina kenan naji Nana Fatima na fadin"Ammi kamar Engr..? Dum! Gabana ya amsa ina Dago kaina sai a na Engr yana sanye da Fararen kaya shadda ce tana maiko da yarari,Daga sama har kasa shigansa ta manyan mutane fuskarsa ma'abociyar Haiba da mirmishi tana nan har alokacin Abba na gaba yana bayansa da Takunsa na Cikakkun maza yan kwalisa. Ni dai naji Abba na gabatar da shi abun mamaki Ishaq har yana bashi Hannu harda rankwafan girmamawa Abba dai bai ce komai ba kansa ya kulle shi kuma Ishaq yasan sunan Engr a bakin Abba ammh bai taba ganinsa ba. yana jin Abba yace ga Megidansa Engr dole yakai gaisuwa tunda da taimakon Engr Aka wankesa daga Zargi. Abba kuwa mamakin Engr ne ya kamasa duk da yasan Halin nagartansa bai taba fad'amasa yasan Fa'iza zatayi walima ba,sai kiransa kawai suna masallacin nan yace gashi sun shigo Karofi ya bashi address din wajen walimar. Sai da ya fita suka had'u ya gasgasta wannan kauna da Engr ke yi ma Fa'iza,kai tsaye ma yace masa"Nan da kwana hudu tafiyata America ban manta gobe ne Daurin Fa'iza ba. sannan na rike date din walimar su ina daga cikin masoyan Fa'iza dole zan bar duk abunda ke gabana Saboda nazo na tayata murna" Daganan yasan Fa'iza ta rasa masoyi,masoyin kwarai da nagarta irin Engr Abdulbasit. Ni ko jikina sai naji ya saki ammh kuma Farinciki ya lullubeni ina kallonsa yana wurga idon nema na,karaf ko ya ganni ta idona inaga ya gane sai naga ya yi min wani kayattacen mirmishin da ya shiga har cikin tsokar jikina sai na kara Damke hannun Amir ina makyarkyata. Kafin a ba ni Shahadar sai da nayi karatu cikin suratul Yusuf farko da Tsakiya da karshe aka yi min kabbara,sannan akace yan'uwana su matso su tayani karban shahadan. Duka muka had'a hannayen mu,Engr na gefe bai saka hannunsa ba sai da Abba yaja hannunsa ya hada da nashi suka mika a tare nima na rike na Amir na mika nawa sauran ma suka miko nasu hannayen muka karba Tare sai kabbara ni ko sai ruwan hawaye. Ya muhallin d'in mu ya karbi abun mgana yace"yau na karbi shahadan haddan Qur'ani mai girma gobe kuma a wannan masallaci zan karbi nauyin igiya uku na aure, yana tayani murna Allah ya sanya alheri" Sai aka kara Daukan kabbara,Mallam ya bada sanarwan Ammi jikinta duk yayi sanyi ganin Engr,Mallam shi ya nuna Ishaq yana fadin"Ga mijin nata nan ga kuma d'an su" Yafada yana riko Ishaq kusa dani da Amir sai masallaci ya Dau kabbara sai fatan alheri ke tashi ni ko kaina na kasa ina jin nauyin idanuwan Engr a kaina Ina ko dago kaina muka hada ido sai naga ya sakarmin mirmishi ammh wannan mirmishin ba so acikinsa sai zallar kewa da tunanin ka rasa wani abu mai daraja,mirmishin nasa babu karsashi a cikinsa sai karfin hali kawai. Ido na suka kawo kwallah bansan lokaci da suka fara shatata ba har suna jika nikad di'na. Ga dai ishaq ga kuma Amir a gefena ammh,Engr dake nesa da ni shi zuciyata ke bugawa da amsa kuwwa a kansa anya ni Fa'iza zan iya kuwa..? Maida aurena da Ishaq kamar na koma gidan jiya ne." Amince ma Engr kuma bawa raina da zuciyata abunda suke so da muradi ne..! Farincikina ko farinciki ya'ya na..? Wanne ne kan gaba..? Wanne zan zaba..?
Chapter 40 · 0% Book details