Sashe 38
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko gani bana yi haka na fad'a kan gado yaraf kamar kayan wanki. tunanina ba shi a tare dani ya tafi wani waje mai nisa na tunanin yadda zan iya kara zaman aure da Ishaq..?tuna Engr kawai in nayi sai naji gabana ya amsa kaina da zuciyata suna amsa kuwwar Rugugi a lokaci daya. Tsakani ga Allah ina son Engr a lokacin da ban sani ba,na fara son shi batare da na sani ba,Sai dai na amince da kyawawan hallayarsa da barkwancinsa da kuma yadda yake sona batare da shi ya yi tunanin alfarma ya yi min ba,shiyasa na ba shi amanar duka rayuwata gabadaya. Saboda Tsabar Rudanin da na shiga har bansan ana ta kiran wayata ba sai da Hafsatu ta shigo ta kawo min nata wayar tana fadin"Yaya Asiya ce tace tana ta kiran wayarki baki dauka ba" Idanuwana har sun yi ciki ciki Tsabar Tashin Hankali na mike a kasalance zaune kan gado ko Hijabin jikina ban nemi cirewa ba, na karbi wayar ina gani tana kallo na kasa kasa nazarina take yi ganin yanayina,ammh bata ce komai ba ta juya ta fice ta bar min Daki. A amsa kuwwa na saka wayar kamar yadda na saba,Sallama nayi Yaya Asiya ta amsa muka gaisa kamar yadda muka saba jin muryata a chunkushe yasa tace"Ya na ji muryan ki ta yi ciki ne ko Mura kike yi..? Na rasa amsar da zan bata sai nace"Uhm' Sai ta min fatan samun sauki kafin ta zarce da fadin"Ashe kuma zaki koma gidan mijin ki Fa'iza naji dad'i wlh. Gwara ki koma ko Saboda yaranki" Wani irin Dum!naji a tsakar kaina nama kasa mgana saboda bakina ya yi nauyi sosai kamar ma miyau ya kasa tsirgamin saboda yadda naji harshe na ya nad'e waje daya. Ina jinta tacigaba da fad'in"Gwara da kika yi wannan tunanin Fa'i komai lalacewar Ishaq dan'uwanki ne kuma akwai zuru'a a tsakanin ku,tunda kuma yayi nadama kema ai kin kwatarma kanki yanci na tabbata kika koma kina da Darajan ki" Ni da yake ma ko Goggo bata fadamin ba Gidan Halisa naje jiya kinsan ta kara samun bari Anty Binta ta kirani tace naje na dubata, ita ke min zencen daga gani suma sun ji dadin komawar da zaki yi,Da farko mamaki nayi tunda ban san mganar ba sai da na Kira Mariya tace itama haka taji baku yi mgana a waya ba dai gaskiya" "Uhm" kawai na samu kaina da Fadi Saboda yadda harshe na ya Nad'e waje daya,mgana ta cigaba yi tana tunamin manufa da alherin komawa gidan Ishaq jin yanayina yasa bata neme ni da wata mgana ba. muka yi sallama na rude zufa kawai nake yi kenan mgana ma ta shiga bakin yan'uwa ban sani ba..? Zufa ya jikamin jiki tunda ga Hijabi na har jikina, Tsabar shiga wani yanayi,kenan har su Goggo suma sun ji labari ni ina nan bansani ba..? Dole na zare Hijabin jikina ina Fifita da shi zufa har kasan wuyana,sai lokacin na tashi na Dauko wayata kira ne ba adadi kuma nasan duk na Engr ne domin tun safe da shi nake fara mgana. Wayar na hannuna ina Tunanin kiransa ammh kuma kamar an hanani saboda ina ganin ban kyauta ba in na cigaba da yaudaransa,kila ni tawa kaddaran kenan yin aure har Abada batare da naji dadin auran ba. Zama nayi na tasa wayar a gabana ina gani Engr na kira ammh na kasa Dauka Idanuwana suka cika da kwallah Hirarmu na dawomin a cikin kaina bansan Lokacin da naji hawaye sun cikamin ido ba a fili na Furta"Allah Sarki Tosin" Kiransa na katsewa sai ga kiran Badariya sai da gabana ya fadi daman mun kwana Biyu bamu yi mgana ba. kamar bazan dauka ba saboda nima bana cikin yanayi mai Dad'i sai dai na Daga kiran Tuna fa Badariya ce. Ina Dauka sai jin guda nayi a cikin kunnuwana sai da na matsar da wayar Cikin Ihun murna tace"Lalle Anty Fa'iza irin wannan kome na ban mamaki ba Labari.? Wayata ta lalace tun last week Mama ta fad'amin da muka yi waya sai yanzu nan Yusuf ya kawo min sabuwa ina saka layi ke na fara kira. Ina murna Anty Fa'iza yayan dai nawa In sha Allahu" Salati na saki a raina kafin naji na tsinke da al'amarin itama kenan taji Labari,ni dai bayan Badariya na amsa wayoyin mutane da dama ciki har da Anty Fadila a bakinta nake jin har kayan dakina da ita akaje aka siyo an gama shiri dawowata kawai ake jira naji ina kuka ne batare da nasan hawaye na fitomin ba Anty Fadila na fad'amin irin murnan da su Anum suke yi zan dawo har a makaranta sun gayama yan ajinsu, suma Umman su zata dawo hatta da Zainab da Mama suna farinciki da dawowata,har muka gama waya hawaye nake ina sharewa a matsayina na uwa ban isa na Karya ma ya'yana zuciya ba. Zan koma ma Yaya Ishaq ba domin ina son shi ba sai domin Ya'yana da Farincikin su,bazan iya karya musu zuciya a karo na biyu ba,barin ma da Na kira jamal saboda shima naga kiransa shima zencen yake yi min,jikina bai kara saki ba sai da yace a wayar wani dan ajin su Amir shi Amir din ya ara ya kirasa ya fad'amai haka na zauna na hada kai da gwiwa ina ta kuka kamar raina zai fita,kukan rasa wani abu da nake so kuma ya yi min nisa. Kamar kuma yan gidan sun sani ba wanda ya nemeni da Hafsatu tazo karban wayata baya na juya bata ma ga Halin da nake ciki ba,bakin kowa sai dai yace na koma ma Ishaq Saboda yarana ba wanda ke tunanin shin in na koma zan samu Farinciki ko bazan samu ba..?meyasa mata da dama ake kokarin Danne musu hakki Saboda yara da an yi mgana sai ace ki koma Saboda yaran ki babu wanda ke tunanin ya mace zata yi in ta koma..?Shin zata yi farinciki..?ko zata Dauwama cikin kunci Allah Sarki Uwa uwa itace wacce zata Sadaukar da Duka Farincikinta Saboda Farincikin ya'yanta. in dai ko hakane naji zan Sadaukar da farincikina saboda Farincikin ya'yana na. Na Tsaida mgana zan koma gidan Yaya Ishaq saboda yarana Engr kuma bansan ya zan yi da shi ba,Sai dai ko sunan shi na tuna sai naji kuka yazo min na san yana sona ya zai yi in nace na fasa auran sa..?wlh da nasan hakane da tun farko ban basa Dama ba da tun farko ban karya masa zuciya ba. Ammi bata a gida diyar kawarta ta haihu sun je barka,shiyasa na yini a Daki ina kuka Engr ya kira har ya gaji yayi sakonnin ammh saboda na riga na yanke hukunci yasa ban bude Sakon ba,Ina son na bama kaina karfun gwiwa abincin ranar bai shiga Cikina ba sai ruwan Tea sai yammah Nana Khadija ta lekoni tace Inno na Cigiyata,sai nace tace mata bana jin Dadi ne zan shigo da Daddare. Bayan sallar mangriba Abba ya Dawo gidan tare da Ammi kila sun biya ne sun D'auketa,ina daki Hafsatu tazo ta kirani In ji Abba sai da gabana ya fadi amnh sai ban razana ba na riga na yi zabi kuma bazan sauya ra'ayi na ba. Cike da kwarin gwiwa na tafi falon Abba ammh duk wanda ya ganni yasan bana cikin natsuwata. Suna tare da Ammi Lokaci duka na duka na gaishesu. Ammi ta kalleni idanuwana sun kumbura tace"lafiya naga idon ki sun tasa..? Cikin Dishewar muryata da yanayina nace"Lafiya kalau Ammi inaga ciwo suke" Sai ta faramin fad'an meyasa ban yi mgana ba da sai aje asibiti Abba na gefe yana jin mu bai ce komai ba. Ni nace ma Ammi idon fa ba sosai ba ne duk Abba na jin mu bai yi mgana ba sai da aka kira wayarsa bai Dauka ba Ammi ta kallesa tana fadin"Ba kiran ka ake yi ba Baban Naana..? Kai tsaye ni ya kallah kafin yace"Engr ne yau ban san adadin sau nawa ya kirani akan Fa'iza ba" Ammi sai ta zaro ido kafin tace"Topha lafiya ba su yi waya da Fa'in ba ne..? Abba yace"Gata nan kiran da nayi mata kenan ya kirani a rude baki ji sa ba, yace tun safe bata daukan wayansa kuma ya tura mata sakonni bata bude ko Daya ba,yanzu ma kiran da kika ga ya yi min nace mai ne ina Office ya bari na koma gida" Ammi mamaki ya kamata ni ko sai sharan kwallah Abba ta kallah kafin tace"To me ya faru.? Ke Fa'i meyasa baki daukan wayansa kada fa ki rikita bawan Allah kinga yana son ki" Sai kawai na Fashe da kuka Abba Da Ammi suka tasani suna kallona cikin mamaki yi nake yi harda shessheka daganan Ammi tasan akwai matsala. Cikin Sausauta Murya tace"Fa'iza bar kukan nan fadamin meke faruwa..? Ko kun samu Sabani ne..? Abba na gefe yaki cewa komai ammh Tabbas ya fahimci wani abu. Fa'iza na son Engr ammh Ishaq ya sakata cikin Tsaka mai wuya. Wayar Abba aka sake kira sai ya Turo wayar gabana yana fadin"Ina jin nauyin Engr Fa'iza ki dauka ku yi mgana kada yaga kamar ina masa yawo da Hankali ne" Kaina na kara shigarwa cikin Hijabi ina kuka Abba bai nuna ya damu da kukana ba,ya cigaba da fad'in"Dauki mana Fa'iza" Sai na dago kaina cikin kuka nace"Abba bazan iya ba. Bazan iya mgana da shi ba" Na fada ina rufe bakina saboda ji nayi zuciyata na wani harbawa saboda yanayin da nake ciki. Ammi ta kalleni a tsorace kafin tace"Wai ban gane ba..? Mgana da Engr ne bazaki iya ba ko mene..? Abba kuma shuru yayi bai yi mgana ba ammh kukan fa'iza ya gama tadamai Hankali Cikin kukan na cigaba da fadin"Abba ka bama Engr Hakuri.." Gabadaya da shi da Ammi suka kafeni da ido shi yana min kallon Tausayi ita kuma Ammi na Rudani da mamaki. Kafin tayi mgana Abba ya rigata da fadin"Hakurin me..? Kai tsaye ina kokuwa da Numfashina nace"Na zabi Ishaq. Zan koma gidansa Saboda ya'yana Abba ka tayani ba ma Engr hakuri wlh ba da son raina ba ne Bansan haka zai faru ba Wlh bansani ba" Na karishe fad'a cikin gunjin kuka Abba yaji jikinsa ya yi sanyi Tausayin Fa'iza