← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 71

Sashe 52

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai naji Tausayinsa kad'an ya kamani yaga Takardan nayi ban ce komai ba Anum tace"Umma ya ki ka ga yaga..? Sai na kalleta kafin nace"Bata da amfani Anum. na yafe ma Daadan ku ko Saboda ku! Allah ya yafe mana Gabadaya" Sai ta rumgumeni tana fadin"Yauwa Umma daman ai Allah na son mai yafiya ko..? Sai na daga mata kai ranar dai uwa da y'a tare suka kwana har abinci tare mukaci bini bini tace Umma kaza tana kuma nane dani ranar ma ko waya bamu yi sosai da Engr ba jin Anum tazo kai tsaye yace"Ah'a muna da babban bakuwa to bari Baba ya daga ma yarsa kafa. na ara miki kanki ki kularmin da Diyata Sosai" Bai kuma hakura ba sai da na bashi Anum suka gaisa cikin sakewarsa kamar yadda ya Saba Radam ya rike sunayen su Amir yana ta tambayanta su Daya bayan Daya sannan ya tambayeta karatu tana bashi amsa daga karshe yace sai sun hadu a Benue. Bayan sun yi sallama ta bani wayar nima bamu jima ba muka yi sallamar ina sauke wayar Anum tace"Umma Sabon Baban mu yana da kirki" Kai na daga mata ban yi mgana ba,Sai da Safe ne Anty Fadila ta kawo min Sakon Zainab a wani kwali ne ashe Sleeping dress ne kala uku masu kyau da Tsada sexy na rike baki ina mamaki da na kirata in yi mata godiya sai tace"A sa ayi ma Yallabai kwalliya da shi. Don Allah white din nan ranar First nigt zaki saka shi" Kunya ma ta bani ina yar Dariya nace"First Night sai kace wasu yara" Shewa ta saki kafin tacr"ke kika san wannan, namiji baya tsufa ko shekara Dari yayi zai yi shagalinsa ni dai don Allah ki saka maman Amir ni fa a yar'uwa na Daukeki kin sani" Sanin Halin nacinta yasa nace mata zan saka mun jima muna taba hira kafin tayi mana fatan isa Abuja Lafiya sannan muka yi sallama. Duka shiri ake ta yi,su Ya Mariya da Anty Nasara sun fi kowa zumud'i tun asuba suka shirya karyawa ma sama sama suka yi nima nayi wanka cikin kayan lefena na saka Abaya doguwar Riga sukayi suka yi na yana mayafinsa naki na zuba Hijabina fari har kasa,sannan na fesa turare duk inda na Gifta ina tashin kamshi. Anum ma da Falaq sun yi wanka sun saka kaya iri d'aya na wani leshi sun saka mayafai sun kyau kamar yan Biyu. Mota bata zo ba sai karfe sha daya na Safe tun safe da muka yi waya da Engr ban sake jinsa ba. nima da zamu tashi na kirasa bata shiga sai nayi Tunanin network ne. Motar nan gabadaya ta Daukemu mu da kayan mu har da rara ma su Hafsatu kamar zasu yi kuka suna Dagamana Hannu Hajiyar su Raliya tace sai gobe zata taho Abujan tana taro yau Abba har da shi a masu rakiya ya yi min kuma dukkan nasihan da Uba zai yi ma yarsa. Shi da su Baba Ati da Inno tunda tun Daurin auren suke min har kuma da zamu tafi sai ga shi ina sharan kwallah Rayuwa kenan kana naka Allah na nashi kuma na shi Tsarin shine daidai. Da yake motar Sabuwa ne ga Lafiya karfe biyu muna garin Abuja,Direban baisan wajen ba,na kuma ta kara kiran Engr lambarsa bata shiga muna cikin Tararradi ne sai Kafaya ta kirani ita ta agaza tayi ma Direba kwatancen gidan su na gwarimpa tunda daman nan zamu fara sauka kafin Su rakamu gidansa na Abuja mu kwana kafin gobe mu wuce Benue din. Gidan su Engr wani katon gida ne Aljannar Duniya har ta Hajiyar Dala mai takama da suna da shi sai ta ce"Kai kun ga gida kamar a turai" Komai ba hayaniya cikin aji da kudi,Gida ne mai girma daga su sai ma'aikata acikin wannan wargajejen gidan Hajiya Shukra da kannenta mata su suka tarbemu tare da su kafayatu,munga karamci irin karamcin da bamu taba zaton suma sun iya ba,ko don ita Hajiya Shukran Bahaushiya ce..? Wani shashe mai falo biyu suka saukemu ashe shashen Engr ne Sharifatu ke fad'a,babu abunda babu a shashen na kayan more rayuwa,abinci ko kala kala da ababen sha ga su nan nama ko harda na Dawisu sai wanda kake jin ci. Sallah muka farayi kafin zaman cin abinci ni dai na kasa ci saboda rashin jin Engr,nasan kuma nasan shima bai Sameni ba ne shiyasa ban jisa ba. Direban da ya kawomu shima an sauke shi a daki na musamman an bashi abinci da abun sha ya huta zuwa Gobe tunda Har Benue da shi zamu je. Dakyar na iya tsakuran abinci shima sai da Ammi ta matsamin sai bayan mun gama cin abincin sannan Hajiya Shukra ta shigo sanye cikin wata shadda Doguwar riga taji aiki,ta ci Daurinta daga ganinta kinga bahaushiya mai ilimi da wayewa da sanin ya kamata ga ta da fara'a,haka hakoranta duk a waje ita da Sister dinta suna mana maraba da zuwa da tambayan Hanya. Su kafayatu ma basa kama da Engr sai dai kama ta jini ammh yanayin Fatan su iri daya ne,tsawon kuma ma Hajiya Shukra suka Dauko dukkansu zabga zabga ne masha Allah. Tana ganin su Anum ta kirasu tana tambayan su sunayen su dayake sun san juna da Ammi suna ta Hira tace"Wannan jikata ce ko..? Tafad'a tana kallona ni daman Tunda ta shigo kaina ma kasa tun kafin ma Anmi tayi mgana Hajiyar Dala tayi karaf tace"Eh ita ce ma ta biyu. ai akwai ma yayanta da kannensu biyu,Kunsan ai auran zumunci ne da shi tsohon mijin nata" Ammi sai hararanta take yi fadi ba'a tambayeta ba sai Hajiya Shukra ta bata mamaki da cewa"Ai Babatunde ya fad'amin Allah Sarki ya sunanki..? Ta tambayi Anun ni kuma ina jin tace Babatunde nasan Engr take nufi tunda shi ya fad'amin sunan datake kiransa. Anum da Falaq suka fada mata sunanyensu cikin Mirmishin ta tace zasu zo mata hutu sai suka juya suna kallon mu tayi dariya kafin tace"Suna tambayan ku ne ku ce eh" Gababaya sai akayi dariya,ni kuma har inda nake ta kariso ta dagoni ta Rumgumeni kafin ta dago kaina Tana Fadin"'Sannu da zuwa Faa'iza.." Allah ya sanya alheri ya baku zaman lafiya" Gabadaya aka amsa da Ameen cikin yanayin fara'arta tace"Papa din su na hanya. bari ya kariso ku gaisa sai muje chan gidan ko..? Kaina na kasa na kasa mgana sai ta Dafa kaina tana fadin"ki saki jikin ki kin ji ko..?nan din ma duk gidan ki ne kina jina ko.? Sai na daga mata kai sakin Hannuna tayi kafin tace"Baku yi mgana Da Babatunde ba ko..? Meeting garesu nima tun safe da mukayi mgana ban kara jinsa ba" Sai naji Hankalina ya kwanta jin yana Lafiya sauran yan'uwanta ma suna ta saka albarka kamar zasu lasheni. Bayan fitan su su Kafaya suka shigo dukkansu kaya iri da'ya suka saka Atamfa riga da sikat har da Murjanin su,Rumgumeni suma suka yi suna murnan ganina Yan biyu ne masu kama daya baka iya bambamce su. Harda Mirmishin su iri daya ne. Suna kallo na suna min mirmishi sai na Tsargu naga kamar sun ganni ba yadda suka yi Tsammani ba ammh basu nuna ba. Kafaya tafi yawan mgana ita tace min"Anty Fa'iza u are welcome..'" Ita kuma Sharifa ce min tayi"Bro Tosin na son ki sosai ya bamu Amanarki yace mu kula dake sosai kiji abinci kada ki zauna da yunwa" Dariya kawai nayi nasan zai aika su Ammi na gefen mu suna ta kallon mu gwanin ban sha'awa zama suka yi dani suna min hiran Engr ina dariya ashe har a gida haka yake na Dauka yana rage wasu abubuwan ashe ma ni banga komai ba. Sai da akayi la'sar suka fita suka barmu muma muka yi sallah Ammi da su Anty Nasara sai fad'i suke nayi dacen suruka da dangin miji Hajiyar Dala dai ba baki sai dai nazarin abubuwa da take gani,sai bayan mun yi sallah ne aka aiko cewa mu shirya zamu tafi chan gidan daman bamu fito da kayan mu ba,sai muka natsa sannan Maa tazo ta tafi dani wajen Paapa dake falonsa. Dattijon ne mai kamala,yana zaune yana karatun Jarida da siririn gilashinsa mai karamai karfin gani,har kusa da kafafunsa Maa ta kaini ta zaunar tana fad'amai ga ni nan ya sakamin albarka. Ba ruwan shi kaina ya dafa yana ta sakamin albarka daga karshe yace"Allah ya sa ku zauna lafiya ki yi hakuri kin ji ko..?Oluwatosin God Boy ne ammh in bai yi miki daidai ba. juzt call me nima papa din ki ne kin ji ko? Sai na gyada mai kai ina Godiya ya bani kyautar kudi cheque Maa ta amsamin,nayi masa sallama muka fice bayan yace bazai samu zuwa Beneu ba. saboda aiki sai dai akwai brothers dinsa da Danginsa yasan i will Enjoy it. Bayan ni ma har su Ammi sun je sun gaisa sannan muka tafi gidan Engr Dake Apo,a motar Papa direba ya tukamu ni da Maa da Ammi sauran kuma suka Biyomu daga baya,su da yake basu da wani al'adu kamar namu na Hausawa Nakiya kawai da alkaki Ammi tayi musu aka raba biyu aka bamasu Maa sauran kuma Ammi tace sun munje Benue tunda iya abunda muke da shi zamu yi. Gidan Engr dake Apo Abuja karamin gidane ammh ya hadu falo biyu Bedroom hudu sai compaund akwai kitchen da bayika sai ta chan baya akwai tsakar gida da Famfo. Ammh gidan ya had'u yaji kayan alatun rayuwa har da wajen shakawatawa da wajen lilo,Akwai megadin dake tsaren gidan,Kowa sai santin gidan yake masha Allah. Hajiyar Dala fad'i take yi"Allah mai kyauta da kari yanzu Fa'iza ne a wannan gidsn..? Tana tunanin ko yayanta da suka auri masu da shi ba wacce ta samu gida kamar nawa,daganan ta sare tasan na riga na sha kwana daman ai abunda ya baka dariya watarana shi zai baka Tsoro. A babban bedroom din gidan Maa ta saukeni tana min addu'a su kafaya ne suka rika zagayawa da mutane suna ganin gidan da suka dawo suka baje suna labarin gidan Yaya Mariya tace"Faa'iza mutumin nan kudi garesa kenan" Ashe bamu ga kudi ba sai da Maa ta saka aka bude dayan bedroom d'in shake da akwatina bakwai babu abunda babu
Chapter 52 · 0% Book details