Sashe 43
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
u Faa'iza ni masoyin ki ne masoyi na Hakika" Sai a lokacin yaji muryata cikin sanyi ina Fadin"Duk da haka nagode Abba ya fadamin abun alheri Allah ya biya da Aljannah" Kai tsaye ya amsa da Ameen Ameem. Duk kokarinsa na kada ya kalleni ya kasaa sai da ya kuramin ido yana daga zaune kan kujera ni kuma ina zaune a kasa ne sa da shi, daman sanda na shigo anan na samesa. Sanye da Farar shadda har da babban Riga sai kwarjinsa ya karu a cikin Idanuwana mirmishin nan nasa bai bace ba. Cikin kauda shurun yace"1pm ne Daurin auran ko..? Kaina na kasa saboda kallon Engr Daidai yake da Ruguza duk wani kwarin gwiwata. Ban ba shi amsa ba sai ya yi mirmishi kafin yace"Abuja zan wuce ana gama Daurin aure nan, sanadin ki yasa cikin wattanin nan ina ta tafiyan Mota Faa'iza" Muryata a shake nace"Allah ya kiyaye hanya' Ya amsa da Ameen kafin yace"Tafiya ta a America ranar Tuesday ne fa,sai nayi wajen 1month achan kafin na dawo tunda aikin daga nan Ma'aikatarmu ta Edo ne suka turani" Ni dai ina jin bayaninsa na ko kasa motsi kamar yadda Shima Ishaq ya kasa motsi Amir kuma tunani yake Umma zata auri Daada na biyu ammh me take yi da wannan mutumin kuma ..? Gani nayi na kusa rasa jarumta ta ga Khadija taki dawowa yasa na mike ina fadin"Zan tafi" Shima sai ya mike yana fadin"Tun yanzu Faa'izaa..? Yadda yaja sunan Faa'izan ne ya karyamin Lago na sai da na Dago ina kallonsa sai ya wani sakarmin mirmishinsa mai kassarani lokaci daya yana Lumshe idanuwansa.. Ji nayi kamar zan fadi ammh bai lura da haka ba kai tsaye yace"Kin yi kyau Faa'izaa.." Yau dai kad'ai Ki bari Tosin ya yaba faa'izarsa" Yanayin mganarsa yasa na kwashi Saurin zan fice Tsautsayi yasa na ci tuntube da Cafet din dake Tsakar Falon sai nayi gaba zan fad'i da azama da wani karfin gwiwa ya rikoni sai gani na Dawo baya Dumu Dumu a acikin kirjin Engr. Sai na ganni yar karama dani a saman hammatansa tsabar yadda bani da Tsawo da girma Cikin Sanyin muryansa yace"Subhanallah sannu baki dai ji ciwo ba ko..? Kamshin Turaransa ne ya cikamin Hanci yasa na kasa mgana ina shirin kwace jikina daga rikon da yayi min, kamar daga sama mukaji an bankad'o labulen Falon an shigo. Gabadayan mu a tare muka juya sai idon mu ana Ishaq. Gabana ya yi kwance kwance yace Ras! Ban ga Amir tare da shi ba ashe shi kuma sai yaki shigowa. ya tsaya daga bakin kofa bai so ya shigo yaga wani abu da zai saka yaga bakin Umma. Engr bai damu ba sai ma sakina da yayi bayan ya tabbatar da na Tsaya Daidai har yana fadin"kin tabbata kina Lafiya..? Kai na d'agamai jikina na rawa ganin irin wulalakantattacen kallo da Ishaq ke bin mu da shi kamar wand'anda ya kama suna wani abun assha. Engr ko Ishaq ya kallah yana Fadin"ko ka biyota ne kaji ta shuru..? Sallama ma muke yi zata tafi" Cikin kallon reni ya ke kallonsa duk da ya gani bai damu ba, ni ko jikina na rawa na kama Hanya zan fice sum sum sai ji nayi Ishaq yaja hijabi na ya Dawo dani ta baya kee da karfi ya yi jifa dani har na kusa fad'i wannan karon ma Engr ne ya rikeni yana Fadin"Sannu" Lokaci daya yana kallon Ishaq kafin yace"Ka yi mata a hankali mana..? Ai cikin tsawa da Fusata yace"Kace nayi mata a hankali mana tunda abokiyar shashancin ka ne.." Dagani haar Engr a rude muka kallesa baki bude shiko kishi da rashin sanin Daraja yasa idanuwansa ya Rufe gani yake yi raina masa wayau nayi ina tare da wani zan kuma koma gidansa. Cikin Dariyan renin wayau yace"Ku ke kallona kamar baku gane manufa ta ba ko..?karya nayi ba shashancin kuke yi ba..?Abun naku ma bai isa ba har sai a ranar da za'a Daura mana aure shine kika lallabo kikazo a yi abunda aka saba, achan kaduna duk watsewar da kuka yi bai isheku ba ya sake biyo ki nan. Anan din ma a filin Allah na kamaku rike da juna saboda Lalacewa Fa'iza me kike nema.? Me kika rasa..? Oh na gane kudi ko..?yana sakar miki kudi ke da iyayen shi shiyasa kike sakar masa jikin ki Tir dake Fa'izaa. wlh kin yi asara idan har kin san kin Fara watsewar ki a waje tun wuri ki yi min bayani domin duk yadda nake so ki koma gidana bazan kwashi datti na kai gidana ba,ki gurbatamin Tarbiyan yarana ba Faa'iza ba zai yuyu ba,Ki Fad'amin gaskiya nawa yake Biyan ki kina bashi jiki..." Mganarsa tasa bata gama Fita ba na Sauke masa tagwayen maruka har guda Biyu dama da Hauni. kafin na Fashe da wani irin kuka wanda daga ji shi kasan na tsatsananin bakinciki ne da bacin rai. Cikin kuka na nunasa da hannuna cikin ihu da Tsawa nace"Kul..Karka kuskura ka kara dangantani da barna ko datti Ishaq kada ka kuskura" Na fad'a ina zubar kwallah shi ko duk da Mamakin marinsa da nayi haka ya watsake idanuwansa sun rufe Engr ko Daskarewa ya yi a Tsaye yana kokuwa da bacin ransa. Dariyan wulakanci ya saka yana nunani sama da kasa daga karfi yace"Don na fad'i gaskiya shine kika mareni..? Karya nayi nace karya nayi..? Ba rike da juna na same ku ba..? In ba iskanci ba ina ruwansa da cewa kin yi kyau kuma meyasa kuka kebe a gida daga ke sai shi nace Muharraman juna kuke..? Ya karishe fad'a yana min ihu kawai sai na kasa tsaida hawayena cikin dauriya da wani Turiri dake taso min daga kasan raina nace"Gaskiya ka fad'a. Tabbas ka fadi gaskiya bai kamata a yi maka rufa rufa a kai maka Datti agidan ka ba,ballatana ta gurbata maka tarbiyan da ka kwashe shekaru kana yi ma ya'yan ka.". In sha Allahu baza'a kai maka Datti gidan ka ba". Na karishe fad'a cikin kuka hawaye wani na korar wani na kama Hanya zan fice Engr ya yi saurin kiran sunana"Faa'izaa.." Ban juyo ba sai da na tsaya cikin kukan dake tasomin ina Dannewa nace"Kayi min alfarman bazaka je ko'ina ba sai an gama Daurin auran nan..? Ina jin muryansa cikin jarumta yace"In sha Allahu" Ban tsaya ba na fice da Sauri ina jinsa ko kunya wai yana kiran sunana ashe da na koma ma auran Ishaq haka zan cigaba da Fuskantar wulakanci..? Ashe a shekarun da na kwashe tare da shi bazai iya shaida ta ba? Ina fita naci karo da Amir na tsaya ina kallonsa sai raunina ya karu na fashe da kuka da Sauri ya kariso zai rikeni na kauce na fita da gudu shima sai ya Biyo ni yana Kiran" Umma Umma" Ina tafiya ina kuka kamar mahaukaciya ban je gidan Goggo ba. sai na wuce gidan su Yaya isa Dakin matar Yaya salisu ke bude ciki na shiga ina ta rafzan kuka sai ga Amir ya biyo bayana. ba kowa a falon sai wayar yaya Salisun kila yana ciki ne,ita na Rarumi na shige uwar Dakin matarsa da ita na rufe kofa. Ina ji Amir na kiran sunana Daga baya har da muryan Yaya Salisu suna kiran sunana cikin kuka da Ihu nace"Ku tafi kyaleni. lafiyata kalau bana son ganin kowa.." Sun jini shiyasa Yaya Salisu yaja Amir suka fita daga gidan nan. Ni kuma nan na sulale ina kuka kamar karamar yarinya.